Sashe 29
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wanda yasan Abba yasan waye Engr duk da ban san ko cikakken sunansa ba nadai san yana da babban matsayi a wajen Abba,da Ahalinsa gabadaya. Ban san komai a kansa ba,illah sanin shine sanadin Samun aikin Abba. kuma megida yake garesa, yana gabansa da babban matsayi a wajen aikin su. Sannan sun zauna makota ka da kakaninsa na bangaran uwa da su Ammi,tunda Ammi daman diyar yayan Inno ne Baffa yake ga Abba Allah ya yi mai rasuwa tun Abdul'ahad na karami. kafin a haifi su Nana Fadila bayan wannan bazan iya Dora komai a kan sunan da naji yau kadai an kira yasakani fad'uwar gaba ba. Daman kuma bana cikin yanayi mai Dadi sai kuma abun ya sake rikicewa har wani sanyi sanyi naji yana shiga kashina sai na kara lafewa saman kujeran in ba ka duba dakyau ba bazaka ma lura dani ba. Ina jin mganganun su Hafsah na kasa tashi ballatana nayi mgana Daga baya sai naji kamar suna hawa min kai ma hirar tasu na yanke shawaran tashi na shiga ciki ne,sai ga Ammi ta shigo Falon Cikin mayafinta daga gani Daga Falon Abba take cikin fara'arta data karu na lokacin tace"Kuzo falon Abban ku ku gaida Engr. Ina Fa'i..?ko ta kwanta ne..? Ina jin ta ambaci sunana sai na yi kamar ina barci haka kurum naji ko tashi ma bana son yi Nana khadija ne ta Dago tana kallona ganin idanuwana a rufe yasa tace"Ina ga tayi barci Ammi" Sai ta juya tana fadin"ok ku kyaleta tunda tayi barci daman tun dazu naga kamar bata jin dadi" Hafsatu tace"Ammi bari mu karisa assigment din mu" Ammi ta wuce tana fadin"Ku bari ku gama shima yana cin abinci ne" Da toh suka amsa mata ta fice ta bar Falon,ina jin fitar ta su kuma suka cigaba da hirarsu kan abunda ya shafi karatunsu kara lafewa nayi zuciyata na tsalle waje daya kamar zata faso kirjina ta fito na kasa gane meke damuna,ammh ina ji ajikina wani abu zai faru dani ko mai kyau ko mara kyau,tun ina karyan barci har ban san Lokacin da na gasken ya yi awon gaba dani ba. Sai farkawa nayi na ganni ni kad'ai a falo ba su hafsatu sai tarin littafansu dakyar kasala ta sakeni na mike ina Dafa kaina nayi Daki ina sauke Tawagayen ajiyar zuciya ina jin Hiran Abba a falonsa kenan har zuwa Lokacin bakon na Abba bai tafi ba. Achan Falon Abba kuwa su Nana khadija da Hafsatu na zuwa gaishe da Engr yana zaune a saman kujera bayan ya gama cin abinci Abba na gefensa suna hira suka shigo suka Durkusa cikin Ladabi suka gaishe shi ya amsa cikin Fara'a yana tambayan su sunayensu suka fad'amai sai ya tambayesu matakin karatu shima suka fadamai sai ya jinjina kansa Lokaci daya yana fadin"That very good. Allah ya bada sa'a a maida Hankali da karatu ban da wasa kun ji ko..?suka amsa mai da toh duk a Lokaci daya har sun yi musu sallama sun tashi zasu tafi Engr ya kalli Abba yana fadin"Baka nuna min wacce ta rika dawainiya damu ba Karaye,ina so nayi mata godiya" Abba na mirmishi yace"FA'IZAA.." Bata cikin su wadanan ai kannenta ne " Sunan kawai da Abba ya ambata sai da yaji gabansa ya fadi a saman labbansa ya maimaita sunan da "FAA'IZAA.." shi kadai kawai ya murmusa kafin yace"Nice name.." Kafin ma hankalinsa ya dawo su Nana khadija sun fice ba Dabi'arsa ba ne yawan tambaya ammh sai ya samu kansa da kallon Abba yana fadin"To ita ta na ina..? Abba yace"Bansani ba kila ko ta kwanta ne,kuma ita ma tayi maka kayan bude baki da yake itama ma'abociya azumin litini da Alhamis ne. in naga tana azumi kai kawai kake fadomin a rai Engr'" Kansa na kasa yana Duba wani sako da aka turomai bai dago ba. ammh sai ya samu kansa da son ganin Fa'izar nan da Baban Nana ke yawan mgana a kanta. yasan yar baiwa ce ta karshe ta hada komai a rayuwarta. Shuru kuma ya biyo bayan mganar Abba shi Engr na duba wayarsa shi kuma Abba ya Dauko tasa ya lalubo Ammi sai gatama ta shigo da Fara'arta sai ya sauke wayar yana Fadin"Ke nake kokarin kira" Kai tsaye tace"Gani nan na shigo kuna Bukatar wani abu ne..? Abba yace"A'a Engr ke tambayan Diyarki wai yana son yi mata godiyan Dawainiya" Ammi na Dariya tace"Haba dai bakomai wani kuma Dawainiya an zama Daya ranka ya Dade" Tafada tana kallon Engr wanda ke karkad'a kafarsa Daya dake kan Daya bawai girman kai ko reni ba,ya riga ya saba in dai ya zauna sai ya Dora kafa d'aya kan dayan nan ya karkad'a. Da mirmishi a saman fuskarsa ya dago yana kallon Ammi kafin yace"Duk da haka Maman Nana a kiramin ita na gode mata." Sai Ammi ta juya tana fadin"Bari to na dubata na gani" Tafada Lokaci daya tana ficewa falon ta,ta koma sai su hafsatu da ta tambayeni sukace kila na shiga ciki nan dai suka barni sai ta shiga Dakina ta iske har nayi barci kuma har ga Allah nayi barci domin ina shiga kaya kawai na sauya na kwanta. Tana ganin nayi barci sai ta koma Falon Abba tana fadin"Engr ta yi barci Fa'izan" Kai tsaye yace"Is ok..ma gaisa wani Lokacin" Har Ammi zata fita ta barsu su yi hira tunda daman sun gaisa da ya shigo sai ya yi gyaran murya ta juyo cikin yanayin mganarsa yace"Ammh yaran ku ba duka sun yi aure ba..?in ban manta ba,Baban Nana ka fad'amin Autan ka kadai ta rage ko..? Abba na mirmishi yace"Yes mun taba mganar dakai" Ya fad'a yana kallon Ammi itama Mirmishi tayi kafin tace"Oh Na gane. yan mata biyu da suka zo suka gaisheka Doguwar ciki ita ce Hafsatu diyar kanwar Baban Nana ce mai rasuwa, d'ayar kuma Nana khadija itace Auta mu" Kai ya jinjina kafin yace"Good. Allah ya raya su" Suka amsa mai da Ameen Ammi ce ta fara tambayan sa ya gida ya su Hajiya yace duk suna lafiya. Ammi tace"Ya jikin kakan naka ta warware ko..? Kafada ya zakuda kafin yace"She is fine now, tana Benue granny ai akwai rigima taki zaman Abuja" Ammi na yar dariya tace"Nagani fa haka tsofaffin suke Allah dai ya kara tsawon rai" Ya amsa da Ameen Hajiya Tafeesu ta tambayeshi yace sai jibi kila zai sauka ta kano kafin ya wuce Abuja ya Dubata ta,sun yi hira da Ammi kan itama Rigiman Hajiya Tafeesu na Tsufa,Abba na taya su da dariya tun da zuwan nasa ma na rigiman nata ne na sai an kawo mata D'anta Bukar. kuma fa ya rasu ammh duk sanda abunta ya tashi sai tayi sati tana kuka tana kiran sunansa. Ya jima a gidan sai wajen goma ya tafi bayan ya shiga ya gaida Inno dubu ashirin ya zube mata tace ya Dawo ya Dauka yana duke gabanta yace"Haba Hajiya in Baban Nana ya yi miki alheri kina cewa ya dawo ya Dauka..? Sai bakin Inno ya mutu ta bisa da saka albarka Ammi ma kudi ya zube mata ita da yara Sai dai bai ce ga na Fa'iza ba aran Ammi nata tunanin ko ya manta sanin Halinsa mai Hannun Alheri. Abba har bakin bakar motarsa ya rakasa inda Direbansa ke jiransa wannan karon tafiyar mota ya yi Daga Abuja yake shiyasa wani aikin gaggawa ne ya dawo da shi ,sun yi sallama ya wuce Abba ya Dawo cikin gida Ammi ta taresa da fadin"Baban Nana nace Engr ya manta da Fa'iza ne..? Naga bai bar mata nata Sakon ba.." Abba sai ya kalli Ammi kafin yace"Sakon me..? Sai da ya fad'a ya gane manufarta kai ya girgiza kafin yace"Allah ya shirya ki Maman nana,abun bin bashi ne" Dariya tayi batace komai ba. Bansan duk wainar da suka toya ba sai da Safe Ammi ke fad:amin Engr yaso ya ganni yamin godiya na yi barci da wuri cikin mganata nace"Wlh Ammi kaina ne jiya ya yi ta ciwo shiyasa na kwanta da wuri" Ammi tace"Ayya sannu.in bai yi sauki ba sai muje asibiti" Da haka muka rufe hiran bayan Ammi ta bani labarin kudin da Engr ya bata na tayata godiya,Ammi macece dake son kayi mata kyauta komai kankantarta tana jin dadin haka Nana Fatima ta fadamin sannan nima zama na da ita yasa na Fahimci wasu hallayan nata. Panadol na sha sai ciwon kan ya fad'a ranar na yini ina harkokina har kasuwa naje siyo kamshin Turare saboda zan hada ma wata kawar Ammi,tare da na Nana Fatima tace min nata ya kare zan hada mata,za'a saka a mota a kai mata,da na dawo sai na hada Humra na itacen kuma na bari sai zuwa da Safe zan gama hadasa. Maganriba ma Dakin Inno na yi shi su Hafsatu daga makaranta suna gidan Raliya,sun je ganin Walid,na idar da salla kenan bayan na gama azkar na Dauki wayata ina Dubawa,Sai ga kiran Abba mamaki ya kamani sai kuma nayi tunanin kila bai samu wayar Ammi ba ne sai na daga kiran bayan mun gaisa Abba yace"Ya ciwon kan..?ya fada kuwa.? Kai tsaye nace"Eh Abba na warware yau har kasuwa na shiga" Dagachan bangaran yace"Masha Allah Allah ya kara sauki..Daman Engr ne ya kirani ya roki alfarman Dinner sai gobe zai wuce kano, na kira maman taku ban sameta ba shiyasa na kiraki" Da sauri nace"bari na tashi Abba daman Doya da miya muka yi da rana,kuma ta kare bari sai a dora da shi" Abba yace"Shikenan Allah ya yi miki albarka after isha'i yace zai shigo" Da haka muka rabu da Abba,na mike da sauri ina fadama Inno sai tace nayi hanzari,sai da na Shiga Bedroom din Ammi na fadamata washe baki tayi tana Fadin"To maza hanzarta" Kitchen na fad'a kamar na sani daman da rana nayi nikan Ayan zan yi kunin aya sai nayi amfani da shi yanzu,Na fara tunanin abunda zan dafa masa,kawai sai nace bari nayi Cousscouss da Souces din kwai,da yaji albasa,Ban yi fruit salat ba,sai da na yayyaka lemu da abarba da apple sai kankana,Nama kuma daman muna da Soyayyen Nama sai nayi dubara na yi masa pepe yaji kayan kamshi Gabadaya nayi na gidan. Inno Daman bata cika cin wannan cimar ba kunu na Dama mata