Sashe 11
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ne ya fara bude taron da addu'a sannan ya gyara zama ya yi gyaran murya kafin ya fara da fad'in"Alhamdulillah dukkanmu nan mun san abunda ya taramu Magana ce akan ya'yan mu Fa'iza da Ishaq," Ya na gama fad'in haka sai ya karkato ya kalleni kaina na kasa ya kira sunana na amsa bakina na rawa na Dago ina kallonsa,Sai ya karkata kansa zuwa ga Uban gayyar shima ya kira sunansa abun mamaki da kwarin gwiwa ya amsa har yana wani gyara zama. Abba ya sauke numfashi yana Fadin"Zaman nan naku ne. Tun tuni ya kamata mu yi sa sai bamu yi ba. Saboda Rashin Lafiyan Fa'iza da wasu uzurirrikan da suka sha kan mu, ammh yanzu Alhandulillah ga shi lokaci ya bamu dama mun zauna ke Fa'iza dake zan fara mganata" Ina jin haka naji na fara rasa karfin gwiwana bai damu ba ya kalleni ya kara kiran sunana Idanuwana cike da kwallah na Dago ina fadin"Na'am Abba" Cikin kaushinsa yace"Mijin ki ya rasa aikinsa a baya kin zauna da shi acikin Halin babu kuma da bakinsa ya fad'a min kin Tallafa masa da sana'o'in ki,bamu taba jin kan ku ba,Sannan Daga Baya Allah ya wankesa aka dawo masa da aikinsa da karin girma. kowa yasan Dake aka yi shirin komawa Lagos sai kuma Daga baya zence ya sha bambam,ina so ki bud'e baki ki Fad'amana me ya faru kika bin mijin ki Sabon Muhallinsa? sannan meyasa kike neman Saki a wajensa..? Yana Dire mganarsa nima na Dire kukana saboda yana mgana zuciyata na bud'ewa da wani kunci sai na kasa mgana gabad'aya suka zubamin ido suna kallona. Ammi dake gefe ta kalleni ta kalli Ishaq taga sai kifta ido yake yi alamun rashin gaskiya karaf ta taso tazo gabana ta rike min hannu tana Fadin"Yanzu ba Lokacin kuka ba ne Fa'iza. bude baki ki fad'i Abunda ke faruwa dukkan mu nan mun zauna me domin yi ma kowanni bangare adalci" Wani irin kallo Abba ya watsa mata da ban taba ganin yayi mata irin shi ba. Da Sauri ta sakeni tun kafin yayi mgana ta koma wajen zamanta tana Fadin"Kayi hakuri Baban Nana" Kai ya jinjina cikin bacin rai yace"Baki da Hurumi a kan wannan mganar ki yi shuru da bakin ki" Jin haka yasa ta hade rai ta kama bakinta,Abba ya dawo da kalllonsa kaina yana Fadin"Umh muna jin ki Fa'iza ki juya ki ga wad'anda ke zaune gabadaya iyayen ki ne da kakaninki, zaki iya fad'amana duk abunda ke Faruwa Domin neman masalaha" Hannayena na saka na kare bakina ina kuka,kamar a wani Lokacin kalamansa suke min duka acikin raina Dakyar na iya bude Idanuwana cike Taf da hawaye na sauke kan na Ishaq na wani Lokaci ina kallonsa ina kallo ya sunkuyar da kai yana zufa ni kuma kai tsaye cikin muryata da kuka Ya taimaka wajen Dasashe su nace"Ku tambayesa shi ke da duka amshoshin tambayoyin ku Abba. Ammh ni bazan iya cewa komai ba matukar bai yi mgana ba" Na fad'a ina kuka na da Sauri ya Dago yana kallona gabansa na fad'i bai Dauka zan iya Dawo da wannan mganar ba Tunda nace na yafe masa cikin rawan baki yace"Haba Fa'iza na dauka mun gama da wannan mganar Tunda na roke ki gafara,kuma kika yafemin" Ina Sharan hawayena da bayan Hannuna nace"Da gaske nake yi na Yafe maka yaya ishaq duniya da Lahira,sai dai ka sani ba hurumina ba ne Tun a wata Hudun Farko addini ya bani Damar haka. Mganar nan kuma Wlh kamar yadda nayi alkwarin baza'a ji ta daga bakina ba. Ka sahale min auran ka,kamar yadda na Bukata sai mganar nan ta mutu har Gaban Abada ba wanda zai jita" Sai ya Rude kamar zai ta shi Daga inda yake Abba da suka zama yan kallo yace ya koma ya zauna ammh ya kasa zama Daidai Cikin sigar Lallashi yace"Bazan iya ba. ai na fada miki bazan iya sakin ki ba Fa'iza Baba yana kabarinsa wlh zai yi fushi dani Sannan me zan fad'ama su Anum da suke jiran na dawo musu da Umman su..?Sannan Zainab na fad'amin bazata zauna ba indai bakya gidan don Allah ki yi Hakuri Fa'iza ki janye wannan mganar ki had'a kayanki mu tafi" Yadda yake mgana zaki san bai da gaskiya duk ya rasa natsuwa sai kowa ya koma yana kallonsa ni kuma Sai naji duk wani Fargaba na fita daga rainaa. Naga kamar yama raina min wayau yana so na koma saboda ya'yansa da Muradin matarsa ba domin muradin kansa ba. sai na samu kaina da yin Wata karamar Dariyar da babu Nishad'i ko kadan acikinta sai zallar bakinciki sannan nace"In dai Saboda kalaman Baba ne kada ka damu Bazai kamaka da Laifi ba ko da yana raye domin ba'a so dole, sannan ba'a aure Dole. Maganar yara kuma Kai ne Uban su kuma Dolen su. ni kuma nan ne ya Dace dani kayi hakuri ka rike su domin bazan bika ba,mganar matarka kuma ta zauna mana ai daman bani na aurota ba, kai ne mijinta kuma kana Tare da ita daman kuma bamu taba zama waje d'aya da ita ba. ballatana Domin bani ya zama abun damuwa,masu kular muku da yara kuma akwai ma'aikata a gari in kuka nema zaku samu in sha Allahu" Na fad'a ina kokarin maida kwallan dake neman ziraromin,kowa sai mamaki ya cikasu na mganganun mu daga wannan ya kalleni sai wannan ya kalleshi Inno ta gyara zama ganin Abba ya kasa mgana cikin muryan data kwana Biyu tace"Kai mu duk bamu gane kan mganganin ku ba .Ku Bude baki kuyi mana mgana yadda zamu gano bakin zaren kai Usman ka yi musu mgana mana" Abba ya sauke Numfashi kafin ya kalleni yana bude baki yace"Fa'iza..". Ban bari ya cigaba da mgana ba ina kallon Ishaq nace"Abba shi zaka tambaya in dai bai yi mgana ba nima bazan yi ba. Saboda ina so na cigaba da yimasa adalci da ya rokeni nayi masa Tun a baya" Ina mgana ina kuka muryata na Sauyawa sai Abba ya maida kallon kansa sai zufa yake yi duk da Fanka sama data kasa dake aiki a Falon da ka gansa kasan ba gaskiya, bai taba zaton zan iya dawo da wannan mganar ba na Shammacesa. Abba ya kira sunansa ya amsa yana Rawan baki Abba mamaki ya kamasa sai dai bai nuna ba cikin Sanyi yace"Kaji abunda Fa'iza tace..?shin zaka iya yi mana bayani ne yadda zamu gane? Ko kuwa zaku cigaba da wasa da Hankalin mu ne..? Sai Ishaq ya fara share zufa da Farin Hanky din dake hannunsa ya Juya yana zare ido suka Had'a ido da Mama wacce ta kauda kai da Sauri ta kasa kallonsa ya dawo da kallonsa kaina ya kasa zama kansa na kan kafafunsa Cikin rawan murya yace"Plz Fa'iza ki bar wannan mganar mana" Nima kai tsaye nace"Zan bar ta kad'ai ne in ka sahalemin auran ka Ishaq" Marairewa ya kara yi kafin ya kalli Abba yana Fadin"Abba ka bani minti goma kacal mu yi mgana ni da Fa'iza" Har zai yi mgana Goggo tace"A baya da baku fallasa mana abunda ke Faruwa ba,ba wanda yaso yaji ammh yanzu tunda kuka fallasa a gaban kowa da kowa zaku yi mganar daga yau koma menene muna so mu ji kuma mu sani" Tafad'a tana kallona ina Kuka haka kurum taji duk abunda yasa Fa'iza mgana abu ne mai taurin da jinsa sai ya Girgiza zukata,kuma ta fi kowa sanin zaman hakurin da Fa'iza tayi a gidan Ishaq mganar ta yasa Inno da Baba Ati suka ce ya yi mganar nan kowa yaji ai Sulhu ake nema Abba ya kalli Ishaq ganin yadda yake rawan jiki yasa ya Dafa kafad'ansa yana Fadin"Kada ka damu ni ba Uba kad'ai nake ga Fa'iza ba. Har da kai,in ita ke da Laifi wlh da kaina zan tasata sai Dakinta bazata kara kwana a garin nan ba" Jin kalaman Abba yasa sai ya fara samun natsuwa yana Hango adalci a mganar Abba Cikin ajiyar rai ya koma ya zauna yana Fadin"Abba ku yafemin kuskure ne na aikata cikin Rashin Sani ammh wlh nayi nadama Tuni kuma naba Fa'iza Hakuri tace ta yafemin ban san me yasa ta kuma Dawo da mganar data wuce ba" Da sauri nace"Saboda itace mafarin duka al'amura. mganar yafiya kuma na Jima da fad'amaka na yafe maka Duniya da Lahira" Abba sai ya koma ya kalleni ya kallesa kansa ya Daure,da yasa ya kasa mgana Shuru falon ya Dauka Kafin Inno tace"Muna jin ka Isiyaku" Ya dago yana kallon Inno ga Tsoro ga Takaicin sunan da ta kirasa da shi ya Tabbata in bai yi mgana ba,ba mafita ammh kuma yana ji ajikinsa Abba zai Fahimcesa Mama ko Jikinta nata rawa,kunya duk ya kamata bata Fatan Fa'iza ta fad'i musgunawanta gareta duk da taga irin kallon da Goggo ke jifanta da shi ji take kamar ta tashi ta Fita sai dai ba Dama. Kamar Daga sama taji Ishaq na Fadin"Wato Abba..Lokacin da zan kara aure ne..Sai sai na ce ma Fa'iza..Mu mu.." Ya kasa karisawa Saboda kunya da nauyin mganar Abba ya kuramai ido yana Fadin"Uhm ina jin ka" Ishaq ya Runtse ido kafin yayi gundinbalan fad'in"Nace ma Fa'iza zamu jingine auran mu ni da ita" Gabad'aya sai Falon ya Dau shuru kamar Mutuwa ta gifta ni ko kamar a Lokacin yake min mgana Hawaye wasu na korar wani a saman Fuskata. Goggo cikin mamaki tace"Wani irin jingina kuma..? Inno ta karb'e da Fadin"Ni kaina na kasa ganewa fa" Mallam mijin goggo da sai a lokacin yayi mgana cikin kallon Ishaq yace"jinginar aure kala kala ne Ishaq, kayi mana bayanin wata irin jingina ce ka nemi ku yi ma auran ku kai da Fa'iza? Ishaq kansa na kasa ya Dago yana kallon Mama itama shi take kallo Cikin mamakin kalamansa kafin ya Sadda kansa domin ya kasa kallon Abba cikin rawam murya yace"na nemi alfarman Fa'iza kan mu jingine auran mu, ba mu'amalan miji da mata a tsakanin mu ,ba wani hulda ta ma'aurata Tsakanina da ita,sai dai kawai ta zauna ta cigaba da kularmin da ya'yana" Yana Dire mganarsa sai gabad'aya su Inno suka Dauki Salati suka Dire Baba Ati tace"Lalle lamarin Babba ne" Ni ko hawaye kawai na bari suna zobomin da