Sashe 46
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
mgana ba sai ya cigaba da fad'in "Ki ce wani abu mana karo na farko da aurane na akan ki Faa'iza" Dakyar na iya fadin"Ina mana Fatan alheri" Ina jin Sautin mirmishinsa kafin yace"Kin gama mgana gabadaya..? To Ameen ykk..?kin ci abinci kuwa..?kin daina kuka..? Ina dariya nace"Duk ni kadai wanne zan fara amsa maka..? Kai tsaye yace"Duka nake bukata" Cikin karya murya da bansan na iya ba nace"ina lafiya kamar yadda kake. abinci kuma ban ci ba kila sai an jima kuka kuma na daina tun daga Lokacin da naji Labarin na zama matarka" Ni kaina in ina tare da Engr bana sanin ma ina sakin baki ina mgana. Sai da naji yace"Da gaske Faa'iza..? Ni kaina bansan adadin Halin da na shiga ba nayi ma Allah godiya Sosai har Umra zamu Faa'iza domin mu kara godema Allah" Jin nayi shuru yasa ya cigaba da fadin"Papa da sweetheart sun ce na gaishe ki sosai tare da Sister dina. Suna ta min magiyan gobe na taho dake Abuja" Da sauri nace"Ni kuma..? Sai ya marairaice kafin yace"Eh suna so su ganki ne. Ni dayake ma kinga jibi zan yi tafiyata bama ganina zaki rika yi ba" Dariya ya bani kafin nace"Ai sai jibi ne Tafiyar goben bazan ganka ba ne..? Sai ya yi saurin fadin"Nufina daga goben nake so nace" Yafad'a yana sosa keya kamar ina ganinsa yana jina ina yar Dariya wani irin farinciki ya mamayesa kafin yace"Wlh da na son da auran nan Visa zan yi miki kafata kafarki zuwa America Faa'izaa" Ina mirmishi nace"Ayya sai kuma ga shi kafarka kafarka zaka tafi" Kai ya kada kafin yace"Kin ci ba shi. Zakuma ki sha wahala wajen biya' Ni dai dariya nayi masa hira ya dinga min yana bani labarin granny din su ta kirashi tana fadan meyasa aure cikin gaggawa haka? bai fad'ama kowa ba yana cemin"Kinsan me na gayamata..? Sai na girgiza kai cikin Danne Dariyansa yace"Ce mata nayi gaggawan na rabo ne,gwara ayi ayi auran kada na haifa mata yaran da take son gani a titi" Sai na rufe baki ina salati shi kuma yana Dariya kafin yace"To karya nayi..?haka tsohon mijin ki yace nawa na biyaki kika bani jikin ki..? Ni wlh ban ji haushinsa ba ga shi Sanadin mganarsa ya sa jikin ya zama nawa har Abada, in a baya ina biya ne yanzu a kyauta ma za'a bani sai ma ina yanga" Kasa mgana nayi ina toshe bakina kada nayi dariya shi ko ajikinsa cikin Kada harshe yace"Wayyo na tausaya masa sosai" Kai kawai na girgiza kafin nace"Ba kai kayi masa kwacen mata ba" Da sauri yace"A'a daman ai Faa'iza ta Abdulbasit ne shi kadai ban cika neman abu na rasa ba Faa'iza,ni da kika ganni nan ina da sa'a duk abunda na nema ban Samu ba to ki tabbatar da ba Alherina ba ne" Cigaba ya yi da bani labarin sa kad'an da wasu abubuwa na shi,ya yi mganar yana dawowa zan tare na zabi in da nake so na zauna kaduna ko Abuja,ko Edo Saboda na Zolayesa nace"Lagos nake so"Da sauri yace"Ban da nan. Ni bana zuwa Lagos" Yafada har da hade rai sai na kyakyalce da dariya shima tayani yayi kafin yace"In domin yaran mu ne kada ki damu tare zamu rika zuwa ganin su bazan lamunta da barin ki ke kad'ai ba. gwara ki zabi kusa dani wlh kika zabi nesa korata za'ayi a aiki Tunda wajen ki zan tare kinsan makale mata manne mata'? Ina Dariya nace"Eh.." Shi kuma sai yace"To ai irina kenan so gwara ki neman mana masalaha" Hiran ce tayi dadi cikin wasa da Dariya da barkwanci har bansan Dare ya yi ba,sai da wayata ta dauke,ashe ba Chaji na fito naga duhu ya yi sosai har mallan ya dawo dukkanmu bamu yi sallar isha'i da wuri ba. Koda na koma Daki ina Sadda kai Badariya batayi barci ba Nana Fatima kuma na wanka Raliya na Dayan dakin Goggo. Kallona tayi kafin tace"Uhm za'a kwashi kallon kauna agidan ki Anty Fa'iza.." Kai na Sadda kasa sai naji ina jin kunyarta dariyanta naji tana Fadin"ni ce fa. Badariya ce Anty Fa'iza. Wlh ina miki murna na jima ina addu'aan Allah ya baki miji mai sonki wanda zai kasheki da Soyayya kuma Daga gani Allah ya baki" Sai na kwashe da Dariya a raina ina Tuna Engr duk da ba'a son maci Tuwo ba sai miya ta kare,ammh alaman karfi yana ga mai kiba Engr karshe ne a sanin kan mace to ya shiga ko'ina meye bai gani ba..? Nasan ba domin wayar ta mutu ba bazai kyaleni ba chaji na sakata da Nana Fatima ta fito nashiga nima nayi wanka na Dauro alwala nazo nayi sallah ranar raba Dare muka yi muna Hira suna ta bani sharwari Badariya tace"Yaushe ne tarewar.? Ina kauda Fuskata nace"Wai fa yace da ya dawo" Nafada kamar zan yi kuka suka kwashe da Dariya har da tafawa. Nan fa suka fara min mganar gyara nace bazan yi ba Nana Fatima tace"Zaku gamu da Ammi" Ina jin haka na zaro ido nasan Halin Ammi mutumcina zata ci. Sai wajen uku na Dare suka kwanta ni dai sai da nayi raka'a biyu nayi ma Allah Godiya sannan na kwanta,shiyasa muka makara sallar asuba sai da aka rika bugamana kofa da karfi. Da safe ma daganan akayi abun karyawa aka kaima su Abba,kuma sai da Safen na kunna Wayata da Sakon Engr na fara cin karo.