← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 11 min read

****

Abba tun goma ya baro warri ta jirgi ya sauka a kano Direban gidan su Ammi yazo ya Daukesa bai zarto da shi ko'ina ba sai karofi ba kuma wai don ya gama abunda ya kaisa ba ne matsalan data kunno kai ne yasa ya yanke komai ya taho.
Yau da safe Ishaq ya kirasa bayan sun gaisa yadda yaji muryansa yasan shima a rikice yake tun kafin ya yi mai mganar Fa'iza ya tsinke da Fadin"Abba Fa'iza zata barni. Ta ki yarda ta biyoni Lagos Abba. Kayi ma girman Allah kada ka bari Fa'iza ta bar gidana"
Daga jin yadda yake mgana ba cikin natsuwa ba ne Abba nata ya saurareshi yayi mgana ya kasa sai ma ya cigaba da fad'in"Abba jiya har mun shirya Fa'iza tace bazata bimu ba.Yara suna ta kuka Abba,Na kasa lallashin su,Mama da su Anty Binta ma sun kasa lallashinsu Abba wlh tallahi ba domin ajiyan sun kirani suna Bukatar ganina affice karfe bakwai na Safen yau bacda karofi zamu bi Fa'iza Abba,bazan iya tafiya Lagos batare da Fa'iza ba,Abba su Amir sun ki yarda su kwana wajena sai Anty Fadila ne ta koma da su gidanta suka kwana har kuma da Safen nan mun yi mgana tace Amir da Anum sun bar kuka ammh Ahmad kwana yayi yana kuka yana kiran sunan Umma. Abba ya Fa'iza take so nayi..?zata kasheni ni ne kwana na bai kare ba.? ka ganni nan ina Office ne ammh wlh Abba bani da Natsuwa kamar zararre nake ji na,ni dai ka taimakamin in na gama abunda nake yi zan sake biyo jirgi Abba ni dai Fa'iza tayi hakuri ta janye kudurinta"
A yadda yake mgana ba tsayawa yasa Tausayinsa ya kama Abba shi kanshi yayi mamakin abunda akace daga bangaran Fa'iza yarinyar da yake mata so na Dabam duk cikin su Mariya,tana da sanyin Hali ga Hankali da natsuwa sai dai shi sha'anin aure baka katsalandan in ka shiga ka zakewa sai kaji kunya in sulhu ne to zai nemi a zauna a samu Fahimtar juna ko don zuru'ar dake tsakani.
Dakyar ya Lallashi Ishaq da cewa ga shi yana Hanyar Karofin,kuma ya hanasa tahowa, da alkwarin da kansa zai kawo masa Fa'iza har Lagos da haka suka yi sallama yana cigaba da masa a magiya shuru yayi ya na tunanin a mganganunsa kamar shi ne bai da gaakiya domin yana ta nanata a bama Fa'iza Hakuri ta duba ya'yansu kada tace zata barshi.
Sannan kuma yana auna mganganun Ammi a jiya da Daddare da suka yi mgana shi dai bai kirasu ya fad'a musu komai ba,sai dai yana tunanin a wajen su Nana Fadila taji abunda ke faruwa,shi yace kada ta sanar da su Inno tukunah yaje ya gani ko zai iya Daidaita lamarin Kalaman Ammi alokacin sun saka ya fara nazari.
Ce mai tayi"Baban Nanah tsakani ga Allah kada ku zake kan sai Fa'iza ta koma Allah kad'ai yasan bakincikin da yarinyar ta Hadiya.
Nifa tun ganina na farko da ita na Fahimci tana da Damuwa,kuma duk sauran sun fita kama mai kyau da sakin jiki cikin mutane Nana Fatima ta fadamin tana da abokiyar zama tana chan Abujan"
Abba ya fadamata diyar abokin karatunsa ne Dr.Lawal bako abokiyar zaman Ita Fa'izan.
Ammi ta cigaba da fadin"Ku saurareta ta fad'a muku dalilinta kuyi ma kowani bangare adalci kada kuce zaku Tursasata"
Shi dai bai yi wani mgana ba,saboda bai je ya gani ba ammh mganganun Ishaq yasa ya fara auna maganganun Ammi sannan yana jin Tausayin yaran shima ai sun yi mgana da Fadilan shi ya ce ta dauke yaran zuwa gidanta har komai ya Daidaita. har ya isa Karofi yana fatan komai ya Daidaita
Sai dai me? koda yaje su Goggo na Cikin Tashin hankalin tun jiya ban bude kofa ba sannan ana ta Bugamin naki Budewa suna Tunanin ba Lafiya.
Cikin Tashin Hankali Abba yace"Tun jiyan data shiga bata fito ba..?
Goggo na sharan kwallah tace"Tun jiyan nan Alhaji. Ni na fara jin tsoron ko lafiya yanzu da ka ganmu Tsaye mariya nace ta kiramin Isa ya kira mai balle kofa yazo balle kofar nan muga Halin da take ciki,daman tun jiya da tazo take ta faman koke koke"
Abba ya fito da waya yana fadin"Bazai yu yu  mai rai acikin Daki tun jiya ba'asan halin da ta ke ciki ba, akwai ciwo akwai yunwa dole a san yadda za'ayi a balle kofar nan bari na Kira Isan da kaina"
Ya daga waya yana kokarin daidaita yanayinsa,Yaya mariya da Hafsah sun yi tsuru tsuru Yaya Asiya sai kiran mariya take yi domin tunda suka fada mata itama Hankalinta ke matukar tashe.
Abba ya samu Yaya isa ya fad'amai Halin da ake ciki yace ga shi nan zuwa da mai balle kofar suna zaune Jugum Jugum sai ga su sun shigo.
Hankalin tashe gabada'ya a kabi bayansu mai balle kofa na aikinsa su Abba na tsaye cikin Zullumi.
Kofar tayi gaddama Saboda Sakata na sakata ta ciki Sai da aka warwareta sannan akayi iya budeta,chan bakin gado suka ganni ina Numfashi sama sama daga kirjina baya sauka a cikina iyakarsa nan yana sama da kasa Goggo da su Yaya Mariya suka yi kaina suna kiran sunana ina ko jin su bana yi lokacin ina kokuwa da numfashina ne ga jikina ya Dauki zafi kamar wuta.
Goggo ta tattaba jikina tana Fadin"Jikinta zafi."
Abba a rud'e yana daga kofaar Dakin yace"Muje asibiti..Isa daukota muje Asibiti"
Yana fada yayi waje a binsa Yaya isa ya Fada dakin cak ya Daukeni su Goggo suka biyo bayansa har waje suna fitowa sai ga su Anty Nasara Goggo ba takalmi ba Hijabi sai da Yaya mariya ta bata na jikinta tare da ita da Yaya Isa sai Abba suka Daukeni zuwa asibiti a halin Rayuwa da mutuwa.
Wani asibitin kudi dake cikin garin Dutsenmah suka kaini nan da nan suka karbeni suka shigar dani Likitoci suka Rufo kaina Saboda Numfashina Dake neman kwacewa sai da suka sakamin Oxygen,sannan suka min allurai da Drip,numfashina ya fara Daidaita Likitan dake on Duty haka ya rika yin fad'a yana fadin ina da Hawan jini meyasa ake tadamin Hankali..?ga jinina nan ya haye sama ina neman mutuwa Abba ya shaki mamaki yana kallon Goggo Lokaci daya yana Fadin"Fa'izar ke da hawan jini..?
Goggo ta dagamai kai tana fadin"Tana da shi shekarun wajen hudu muma bamu sani ba,domin bata gayama kowa ba ta mgangun da aka bata a asibiti yara suka gani suka gane"
Mamaki ya kara kama Abba duk da Hawan jini ya zama ruwan Dare a wannan rayuwar,ammh Fa'iza tayi kankanta a shekarunta ko shi da ya Haura Hamsin wlh ba shi da wannan mugun ciwon.
Gefe ya koma kawai yana kara nazarin wasu abubuwan,sai dai yayi mgana da likitan yace a kula dani komai zai iya kashewa saboda na samu lafiya,suna asibitin nan har Yammah sai sallah ke fitar da su Abba ko ruwa bai isa sha ba sai dai yana amsa wayoyin dake shigomai ciki har da na Ishaq Abba na Daukan wayansa yace"Kayi hakuri Ishaq mu bi komai a sannu. Yanzu haka nazo na iske Fa'iza ba yadda take gata ma a asibiti likitoci na kokarin ceto numfashinta"
Shima cikin karaya yace"Wlh nima Abba in naje asibiti na kwanta nima zasu kwantar dani. Nima bani da lafiya bani kuma da natsuwa"
Abba ya rintse ido kafin ya bude cikin Dattakonsa yace"To kai ma ka natsu kasan satin ka na farko kenan da Fara aiki plz ka tsaya kayi abunda ya kamata. Fa'iza na bukatar addu'anka, in ta ji sauki sai a zauna ayi sulhu a Fahimci juna insha Allahu komai zai Daidaita"
Da haka jikinsa yayi sanyi yana fadin"Allah ya bata lafiya Abba meke damunta..?
Kai Tsaye Abba yace"Hawan jininta ne Likita sukace ya tashi,Damuwa ne yasa jinin ya Daga sama sosai sannan ga maleria"
Cikin mamaki Ishaq yace"Hawan jini Abba?Fa'iza ke da Hawan jini?
Cikin mamaki Abba yace"Eh baka sani ba?Goggon su tace an yi shekaru fa"
Sai ya kasa mgana kunya ya kamasa,To yaushe ya san Laluran Fa'iza ballatana yasan Halin data ke ciki Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un bazai raba dayan biyu ba,Dalilinsa Fa'iza ta kamu da wannan cutar nauyi da yadda ya fara fallasa kansa yasa bai kara ce ma Abba komai ba suka yi sallama Ya bar Abba da kara auna Tambayarsa kan mizani girgiza kai yayi a fili ya furta"Allah yasa ba abunda nake zargi ba ne. Domin in zargina ya tabbata bazan ragama kowa a kan wanda ya nemi kashemin y'a ba"
Abba ya fada yana kokarin daidaita kansa shi mutum ne mai zafi baya son ka wulakantasa ko kaci zarafinsa alhalin shi bai ci naka zarafin ba,Sannan ya'yansa ba abun wulakantarwa ba ne,shiyasa yake tsaya musu tsayin daka ga duk wanda ya nemi tozartasu ta kowacce siga.
Sai Dare na Farfado kuma Alhamdulillah na farfado cikin Hankalina sai dai tun da naga Abba sai kuka,alluran barci akayi min na koma barci kamar mattaciya sannan har da rashin samun hutu da bana yi sukace. shiyasa sukace zasu rikeni na Tsawon kwanaki anan.
Sai da su Anty Nasara da su Yaya Mariya sukazo Yaya isa ya tafi da Abba gida yaje ya huta yaci abinci,Goggo kuma bata koma gida ba su Hafsatu suka zo mata da abubuwan da zata bukata,nan ta kwana tare dani kafin kuma wayewar gari ciwo na ya shiga kunne kowa ana ta kiran wayata bata hannuna tana wajen Yaya mariya,da Safe na tashi Lafiya sai dai idanuwana sun yi luhu luhu sai ciwon kai da bai sakeni ba,ammh bana ma kowa mgana in an gaisheni sai na amsa dakai.
Zuwan Abba ya rikitani yana cemin"Fa'i ya jikin naki.?
Sai kawai na Fashe mai da kuka sai ya zauna gefen gadon yana Lallashina fadi yake yi"Kinga bar wannan kukan kin ji ko..?ba mai kara takura miki Fa'iza har sai kin samu lafiya"
Jin haka yasa na tsaigaita da kukana Daman Fargabata kada Abba ya ce na koma ma Ishaq abu na farko da zai Umarceni naji na kasa cika umarninsa ammh jin haka yasa sai naji nauyin kirjina ya kwanta,Kaina kawai na Dafe nayi kasa da kaina ina ji Abba nata waya ciki har da Nana Fadila na kasa kunnena sai naji ana mganar su Amir da sauri na Dago ina kallon Abba tun kafin in yi mgana yace"In ta kara jin sauki zuwa yammah sai a had'ata da yaran su ji muryanta ko zasu samu natsuwa"
Sai  na kurama Abba ido har ya gama wayar ya kariso gareni yana kallon yadda na rame da bai taba Lura ba sai yau cikin son kwantar min da Hankali yace"Kada ki damu su Amir na wajen Nana Fadila tace suna ta kiran sunanki ne, sai nace ta bari in kin kara jin sauki zaki yi mgana da su ko..?
Kai tsaye na girgizama Abba kai karo na farko da nayi mgana nace"Ku kyalesu Abba. gwara su saba da rashina"
Na karishe fada muryata a shake,Gabadaya sai suka bi ni da kallo ganin haka yasa na koma na kwanta na kauda kai ina tsiyayan Hawaye ni kadai nasan yadda nake azbatuwa da rashin su Amir ammh bani da mafita kila tamu kaddaran kenan dagani har su.
Wasa wasa sai da na Shafe kwana Biyar kwance a gadon asibiti,ranar da na kwana Biyu Ammi ta zo Dubani ita Nana khadija da Yaya Abdul'Ahad da Raliya,aranar kuma Abba ya koma tare da su da Hafsah da zata fara karatunta a Kasu Kaduna State University,Abba ya tafi da Dokar kada wanda ya karamin wata mgana a kyaleni sai nasamu lafiya tunda likita yace jinina ya yi sama a guji tadomin da abunda zai rika tadamin Hankali. da wannan Abba yace a rabu dani mganar Ishaq ko ta yarana kada a sake Daukomin ita,a kyaleni sanda na samu Cikakkiyar Lafiya sai a zauna a samu mafita shi kuma Ishaq din Abba ya masa mgana da kakkausan murya akan kada ya baro aikinsa ya taho in yana so ya shiga mganar in kuma baya so shikenan ya taho Dole ya Hakura ya zauna su Anty Binta kwana Hudu sukayi suka biyo mota ita da Anty Hure,suka bar Mama agida ita kad'ai tunda yaran sunki zama kamar ma basu san su ba har Shi kanshi Baban ya kasa Lallashin su,Anty Binta ita kanta tasan rabuwar Fa'iza da Ishaq wani abu ne wanda kowa ba zai so faruwansa ba,Da ka gansa kasan yana cikin damuwa duk ya fita Hayyacinsa,Abinci siya yake yi Mama bazata iya wani girki ba. Anty Binta a ranta ta saka cewa in suka koma zata je ta samu Fa'iza ta mata mgana ta roketa ko zata koma ko saboda yaran dake tsakanin su.
Zainab kuma daman tace sai ta gama shirinta,Ishaq din tun a washegarin tahowarsu Lagos ya fada mata Halin da ake ciki itama hankalinta ya tashi tace zata kirani to kuma tun ranar take kirana bana Dauka bata san ina Gadon asibiti ba,sai daga baya Yaya Mariya ta Dauka ta fadamata ga Halin da nake ciki, sai jikinta ya karayin sanyi itama ta kuduri niyar cewa kafin ta wuce Lagos zata zo ta sameni mu yi mgana domin har ga Allah kamar yadda na bata gummuwa a auranta da Honey itama bazata zo aurammu ya samu matsala ba.
Tunda ya fad'amata cikin damuwa cewa Saki nake nema batayi mamaki ba,tunda ai zuwanta tasan wasu abubuwan dake faruwa tsakani ga Allah abunda Honey da su Mama suka aikata,ma Maman Amir bai kyautu ba.
Chapter 2 · 0% Book details