← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 71

Sashe 7

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Mallam mijin Goggo ya kirasa yana shashen Inno ya shiga gaishe su da kwana ita da Baba Ati,shiyasa yana gama wayar Inno ta jefamai tambayar me ya faru..?ba shi da mafita illah na gyara zama ya fayyacemusu abunda ke faruwa. Inno ta rike baki kafin tace"Ikon Allah. Shi aure fa daman rai garesa Usman duk yadda ka so ka san al'amarin sai kaga daga baya komai ya Sauya, ya kamata a zauna da ita da shi din domin yi musu sulhu, ba saboda komai ba sai domin yaranta" Abba yace"Daman akwai niyyar haka Inno. rashin Lafiyar da tayi ne yasa na Dakatar da komai sannan ga Dokokin Likita a kanta" Inno ta jinjina kai tana fadin"Allah Sarki wlh duk cikin ya'yan Hafsah tafi bani Tausayi sai ka ganta shuru shuru bata da Hayaniya Allah kad'ai yasan bakin cikin data Had'iya, sai dai bazamu yanke ma barayin mu Hukunci ba har sai shima yazo an zauna da shi, an ji Daga ina aka Haihu a Ragaya" Baba Ati na gefe tayi karaf tace"Fad'i ki kara Inno yarinyar nan Fa'iza ta Had'iye Bakincikin wannan mijin nata da danginsa" Daga Inno har Abba Hankalinsu suka maida kan Baba Ati na neman karin bayani sai ko ta gyara zama ta cigaba da Fadin"Mganar gaskiya sauran yan'uwanta sun fita sa'ar gidajen mazaje,Nasan wasu abubuwan tun Tamadina nada rai sannan ita Hajiyar Fatiman Goggo nasu na fad'amin wasu abubuwan" Da Sauri Abba yace"Don Allah Baba ki fadamin abunda kika sani kan auran Fa'iza da Ishaq" Ya fad'a Lokaci daya yana jin ransa na kuna,Baba Ati tayi shuru taki mgana Inno ta kalleta Lokaci daya tana Fadin"Atine ki fadamasa komai Uba yake gareta kuma domin a samu gyara in zai gyarun kenan fa" Baba Ati tace"Da dai ban so nayi mgana ba. ammh Tunda takai suka Kure Hakurin yarinyar nan nasan komai ya zo karshe. Duk cikin ya'yan Tamadina ita ta Dauko hakurinta da Zurfin cikinta Wlh ni nasan ko yan'uwanta ba kasafai take zuwa Inda suke ba,mijin ya hana sannan Karofin ma sai ta shekara bata zo ba sai wani babban sha'ani,ance Mahaifiyarsa da yan'uwansa basa Son Fa'izar ne ta sha wahalan su,Uwa uba kuma yazo yayi aure,Goggon su ke fad'amin sai yafi wata uku a chan inda yake aiki wajen Amarya bai waiwayi Fa'iza ba. sai itace ke mata sako akai akai Saboda yaranan,kuma nima na gani Rasuwar ta madina wlh sau d'aya Surukarta tazo ranar uku daganan bata dawo ba. mijin nata kuma ni dai har muka watse wlh bai zo ba,kuma har Ciwo Fa'izar tayi Goggon su ta wuce da ita gidanta ta yi jiyya har ta warke ta koma bai zo ba, ammh mazajen su Asiya sun zo wlh da su aka Sallaci tamadina sannan da su aka zauna akayi karban zaman gaisuwa,wannan mijin na Fa'iza yanzu ne ya yi sanyi daga shi har uwarsa da Rayuwa ta koya musu Hankali Saboda d'an rashin da Shi Yaron yayi Fama da shi" Baba Ati ta karishe fad'a tana gyada kai Inno ta kalli Abba shima ya kalleta Cikin takaici da wani bacin rai,Inno na son mgana sai ya rigata da Fadin"Tabbas biri ya yi kama da Mutum.." Sai yama kasa mgana Saboda bacin rai,Inno ta jinjina kai Lokaci da'ya tana Fadin"Gaskiya Yarinyar akwai zurfin ciki ga sanyin Hali" Baba Ati tace"Irin uwarta ce. Har tamadina ta bar duniya bata da abokin Fad'a haka Mijinta da abokan zamanta suke fadin Tarin alheranta Ita kan ta Dace wlh ta samu shedar Duniya Saura ta Lahira" Inno tace"Allah ya jikanta ta. Lahirar ma muna mata Fatan Dacewa in sha Allahu" Kamar Daga sama sukaji Abba na fadin"Shi Ishaq din baya son Fa'izan ne..? Baba Ati tace"To ni kam ban sani ba ammh ai auran zumunci ne. mahaifinsa Alhaji Kabiru mutum mai son zumumci shi ya had'a auran,zai iya yuyuwa Saboda kaga ita Fa'izar na da Lalura,ammh dai kam ta yi zaman Hakuri da shi da kuma iyayensa" Cikin kaushin Muryan Abba yace"Shi ne an san wannan ba'a raba auran ba.?ta yaya za'a bar yarinya tana kunsan bakin ciki haka..?oh na gane Hawan jinin da ta samu ma Dalilin sa ne da Danginsa kenan..? Baba Ati tace"To wa suke da shi da zai tsaya musu?Goggon su ce kad'ai da ya'yanta,kuma kasan sha'anin aure yadda yake, sannan zurfin cikin yarinyar ba'a jin kamai a bakinta sai dai in an Fahimta fa,To ta ina zasu fara sai mutum ya shiga mganar kuma ita tazo taki mgana shiyasa aka saka mata ido ake binta da addu'a. baga shi yanzu da tagaji don kanta ta nema ma kanta Mafita ba Usmanu..? Abba sai sakin Huci yake yi yana auna wasu abubuwa kowa zai bude baki sai yace Fa'iza sai a Hankali Ashe sa'ar Gidan miji ne batayi ba. Ya na ji su Inno na mgana baya Sauraransu sai ma mikewa da yayi yana Fadin"Cikin Satin nan za'ayi ta kare In sha Allahu" Inno tace"Gwara hakan dai gaskiya. Nima ina son zuwa na Dubata in zaka tafi sai na bika muje tare" Da Sauri Baba Ati tace"Ni kuma sai ki bar ni ni kadai..?ai kafata kafarki" Abba duk da bacin ran da yake ciki sai da ya Dara kafin yace"Shikenan duk sai muje Direba ya tukamu. Gidan nan daman an gama komai Funitures,kadai suka rage ban samu zama ba ne,ammh zamu yi mgana da Maman Nana,saboda mu samu wajen sauka in munje garin" Inno da Baba Ati suka hada baki wajen Fadin Allah ya taimaka ganin yadda Abba ke yi ne yasa Inno ta kira sunansa ya amsa sai ta kallesa tana Fadin"Kada ka yanke hukunci cikin Fushi Usman, mu bi komai a sannu kaji ko" Kai Tsaye yace"In sha Allahu Inno" Daga shashem Inno Dakinsa ya wuce yana neman Fadila a waya bayan ya sameta ta Dauka sun gaisa cikin Dakushewar murya yace"Fadila ki kira mijin Fa'iza ki tambayesa asibitin da suke kije ki Dubamin Ahmad dan wajen Fa'iza. in da yuyuwa ki saka ayi masa Transfer zuwa in da kike aiki " Cikin Ladabi tace"To shikenan Abba" Daganan ya katse wayar saboda Haushin Ishaq din yasa bai kirasa ba,ransa kawai yaji yana Tafasa a Fili ya furta"in dai ko hakane Zan tabbatar masa da Fa'iza na da Gata" Ko Ammi da taga yanayinsa ta tambayesa,sai yace mata bakomai gajiyan aiki ne kawai shi kadai ya zauna yana auna wasu abubuwa sai yaji ya zaku a zauna ma domin yaji inda bakin zaren ya fara Ya kira wayar Fa'iza bata Dauka ba,sai ya kyaleta Tunda Sun sake mgana da su Goggo sun tabbatar masa sun hanata tafiya ta shige Daki tana ta kuka,sai ya bari sai zuwa anjuma zai sake kira ya lallasheta. Har ma ya fita yana Office Nana Fadila ta kirasa ta fadamai jikin Ahmad da Sauki,zazzabi ne ya rikita jikin yaron,sannan kuma ta maida shi asibitin da take aiki Abba yaji Dadin jin haka cikin Murna yace"Dakyau Allah ya yi miki albarka Nana Fadila" Ta amsa da Ameen Abba kafin tacigaba da fadin"Ammh Abba Laluran Ahmad har da rashin Uwa a kusa. Sai kuka yake yana kiran sunan Umma sai da muka saka alluran barci cikin Drip dinsa sannan muka samu ya kwanta yana barci" Shuru Abba ya yi kafin yace"Bakomai Fadila ina shi Ishaaq din..? Fadila tace"Yatafi wajen aiki sai dai Mahaifiyarsa na nan,tare da amaryansa suka tafi inaga ita gida ta koma tazo da wasu kayan" Abba ya jinjina kai yana fadin"Bari zan kiraki ina office ne" Daga haka suka yi sallama Ranar gabadaya ransa a bace ya yini a office duk wanda ya gansa sai yace yau waya bata ma Eng,rai an riga an san shi Mutum ne,mai barkwanci da Wasa da Dariya shi ko Bacin ransa irin Labarin da ya samu ne Ishaq ya basa,kunya sosai shiyasa yaga kiransa yaki Dauka sai dare da ya koma gida yayi wanka ya na Hutawa ya kira Fa'iza domin yaga kiranta Daga baya. Sanda wayar Abba ta shigomin na Idar da Sallar isha'i kenan,ina ta kuka tun Safe da Mallam ya hanani Tafiya nake kuka sannan ban ko kara lekawa ko Falo ba, da Farko Kin amincewa nayi da Goggo taso tsaidani sai da Mallam ya fito da kansa ya rika lallashina sannan na Hakura bayan yace Abba yace kada na tafi na Dakata,Tunanina Ya'yana sai a lokacin na Fahimci nayi Wauta,kada na zo na rasa ya'yana Saboda su na zauna shekaru ina kunsan bakinciki yanzu in na rasasu wake da asara? kamar an rufe zuciyata na daina Hango duk abunda ya Shude a baya ya'yana kawai nake tunawa da kuma Halin da Ahmad yake ciki nayi ta kiran Ishaq naji ya jikin nasa Ammh bai Dauki wayata ba, sai na sakama raina na rasa Ahmad shikenan ya rasu Goggo kuma banza dani tayi bata kara kulani ba Har Yaya Mariya tazo tayi ta aikin Lallashina ban saurareta ba. Sanda naga kiran Abba kukana sai yaci karfina a raina nace rasuwar ya kirani ya fad'amin Shiyasa sai da ta kusa katsewa Sannan na Daga ina kuka nace"Ahmad ya rasu ko Abba..? Cikin Muryan Lallashi yace"In ji wa..?Ahmad na nan da ransa kuma jikinsa da Sauki, yana asibitin da Fadila ke aiki Ita ke kula da shi" Fadin haka yasa ajiyar rai ya kwacemin har sai da Abba yaji cikin Dariya da kuka nace"Da gaske Abba..?Da gaske Ahmad yaji sauki"? Kamar yana ganina ya gyad'a min kai kafin yace"In sha Allahu ki kirata kiji yanayin jikin nasa. in baki yarda dani ba" Da Sauri nace"Na yarda Abba wlh na yarda" Sai yace"To ki daina kuka mana Fa'i Share hawayen ki kin ji ko..?Ahmad ya samu sauki sosai har yana mganarsa ma" Kamar yana ganina na ko share Hawayena Hankalina ya kwanta Cikin Sanyin murya nace"Na share Abba. Na bar kukan wlh" Abba ya gyara zama yana fadin"Dazu ni nace Goggon ku su tsaidake saboda barinki ki tafi Lagos ke kadai Fa'i hatsari ne ga shi baki da ishashen Lafiya,kuma baki san waje ba wahala zaki sha ki bari in kina son zuwa zan zo sai mu tafi ta jirgi yadda bazaki wahala ba" Da Sauri nace"Na hakura Abba daman da naji jikin Ahmad din ne ammh tunda ga Anty Fadila ga su Zainab basai naje ba" Abba yayi mirmishin su na manya kafin yace"Shikenan to ki
Chapter 7 · 0% Book details