Sashe 58
Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yake su ba su cikamai mgana da Hausa ko Turanci ba, sai ya nemi izinina kan zasu yi mgana da yaren su da nace meyasa yake neman izinina sai yace"Kada ya shigga hakkina naji kamar suna yi da ni" Daga ranar na kara ganin kimarsa da Darajansa sannan ya samu babban matsayi a rayuwata. Iyayensa kuwa tsakanina da su sai Godiya bayan kwana biyu sai sun kirani suna tambayata lafiya ta Papa da Maaa kamar diyar su suka Daukemi. haka suma su kayafatu nima kuma na saki jiki da su kamar yan'uwa na,nima ina kiran su tunda kudi yake sakamin kamar bai san zafin su ba. koda yaushe nima cikin waya nake yi da yan'uwana. Su Anum kuma bai wuce a sati mu yi mgana sai biyu ta wayar zainab ba. Engr har mgana yayi zai siya musu waya nace Babansu bazai bari ba Daganan bai kara mgana ba illah cewa da yayi wannan tunani ne shima mai kyau. Sannan bai taba Tursasani akan na sauya ra'ayi kan karatun Boko ba. sai ma supporting dina da yake kan ra'ayi na ba ruwansa yace ni ya ke so kuma Dole ne ya girmama Ra'ayi na. karatu nace ba na so. wlh bazai taba min Dole ba ranar da nake da sha'awa ko na furta masa ko wata makaranta ne zai kai ni nayi karatu har sai nagaji. Watan mu biyu da zuwa Edo Engr yace na shirya zamu je Lagos na zata zan rakasa wani aiki ne,ashe Hutu zamu tafi tafiya ce mai mikakkiya. Tafiyar mota muka yi kuma bai sa na Dauki kaya masu yawa ba a hotel muka kwana ranar sai da safen yake fad'amin London zamu je ya dauki Hutunsa na karshen shekara zamu sha Honeymoon yadda zai ji dadin yin kara'in sa sosai. Da nace ban fad:a kowa ba sai yace shi ya sanar da Abba baki na bude kafin nace"Kace mai me..? Kai tsaye yace"Nace masa zamu je Honneymoon mana sannan na fad'amasa kila ma sai kin samo ma su Amir kani ko kanwa zamu dawo" Nasan fa zai fad'a hakan din yasa kunya kamar Abba na gabana da yasa ma na kasa kiran shi wlh. Zuwana Lagos sai ya tasomin da kwad'ayin ganin ya'yana da na yi ma Engr mgana sai yace min na bari in muka dawo ta nan zamu sauka zamu je mu gansu. sai na bar mganan Saboda zama da shi na Fahimci yadda yake Daraja kowata mgana ko shawara da ta fito daga bakina, na kuma san tunda yace to haka din zai kasance. Kwanan mu biyu a lagos kafin jirgin mu ya tashi zuwa London Ranar an ga rawan banjo da rawan jiki a gurina haka na rike Engr da jirgi zai karta tashinsa sai da jikina ya juya,kamar zan yi fitsari karshenta dai har da zawo sai da Engr ya rakani Tiolet din Jirgin nayi,Allah yasa ma muna Vip ne,Kunya duk ta kamani sai daga baya bayan na dawo hayyacina na kalli Engr ina fadin"Kayi hakuri ban taba hawa jirgi ba ne" Sai hawaye sharr sai ya kamani ya Rungumeni yana fadin"To meye aciki..? Ai jirgi yanzu kika fara hawa Hajiya ta" Ai ko dai domin kwana goma muka yi a london mun yawata sannan ta bakin Engr ya gwangwanji amarcinsa nima ai na yi amarcin nayi kiba nayi Fari kamar bani ba na samu hutu,Hutun da ban taba Tunanin zan samu ba. Daga London Dubai muka je muka yi sati Biyu shima mun yawata naga manyan Dogayen gine gine sai da na zama yar kauye daman chan yar kauyen ce munje mun yi siyayya katin bankin Engr na Hannuna yace na daukan ma ya'yansa tsaraba tunda zamu sauka a wajen su kafin mu koma Edo. Daga Dubai sai Mumbai India shi kam garin ya yi min dadi mune har Cinema kallo, tsukewa cikin Riga da wando yanzu tuni na kware akai,sai dai bana yadda na bayyana jikina Tunda nasan Halin mijina. Duk inda muke muna tare da juna hannayena na makale cikin nasa Hotuna ko ban san adadin da muka Dauka ba da ni da shi,ina kallo kaina ina kara tuna ni ce dai Fa'izan nan da bani da komai ban mallaki komai ba. nice yau ke zagaye kasashen ketare a haka a yadda nake din nan, Allah shi bakayi masa Dubara sannan ka sani abunda ka raina watarana shi zai tsole maka ido. Duka yawon mu da muka gama a Saudiya muka yada zango Lokacin an fara Umra sai muka yi ta Ibada a Masallaci muke yini sai dare muke haduwa mu tafi masauki. Wata daya muka kwashe a Saudiya kafin mu fara shirin tafiya Lokacin da naganni gani ga ka'aba sai kuka nayi ma yan'uwa na Addu'a tare da yara na da Mijina,sannan na rikor ma kasata zaman lafiya tare da Allah ya bama iyayena aljannah,tare da sauran musulmai gabadaya. Ta Lagos din muka sake sauka kamar yadda yace,kuma tare da kayan mu muka taho Tunda Engr ya saki kudi ni kaina Sauran kayan nawa duk achan ya siya mana wasu na sawan,ba wanda ban yi ma Tsaraba ba Paapa maa,su kafayatu har da Hajiya Kudurat sai su Amir da Abba da sauran yan'uwana Tunda in ban Siya ba Engr zai ce kin ko yi ma wance Tsaraba..?in nace A'a sai yace to nayi ma kowa da kowa shi ya bani Dama. Sai da muka Huta na kwana Hud'u sannan Engr yace na kira Anty Fadila Tunda gidanta zamu fara zuwa kamar yadda na bukata Daman wayata kasheta nayi,lokacin da taji ina Lagos zamu zo ni da Injiniya ta saka ihun murna tana jin dadi. Tace tana asibiti ne ammh zata dawo sai ta turomi lambar babansu Falaq Engr ya kirasa shi ya bashi address din,Tashar Taxi muka yi tunda Direba da mota chan Edo muka barsa. ya ma ce Kano zamu je daga Lagos mu gaida Hajiya Tafeesu tana ta korafin bai kai mata ni ta ganni ba.