← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 71

Sashe 47

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Fatan kin tashi lafiya Amaryan Abdulbasit?
"I love u"

Na lura baya son yana yi min Turanci Saboda kada na rika jin kamar zai kureni Allah Sarki Engr sai ya koma Daidai dani mun taba mganar karatu da shi nace masa bana ra'ayi kai Tsaye yace"Bokon banza Bokon wofi kin burgeni wlh meye a bokon ban da wahala.?ke ce mai ilimin duk duniya Tunda kinsan Qur',ani da Hadisai ni kaina kamar na kwashe bokon kaina na Kona haka nake ji"
Alokacin bansan Dariyan da nayi ba,Shi komai nawa ya gama yi masa ba shi da wata matsala.
Tun Safe nayi wanka na cakare da Wani materil Doguwar riga ya kuma yi min cif mayafi dai suka yi sukayi na saka nace Hijabina zan saka.
Yace min daman kafin ya tafi zamu yi mgana,bamu yi waya da Safe ba na dai yi kokari na tura masa amsar da cewa"Lau na tashi Ya Tosin din Faa'iza shima ya tashi.?
Sai bai bani amsa ba kuma bai kirani ba nafi Tunanin ko yana waya ko kuma wanu uzuri ya rikesa.
Wayar tana hannuna ina jiran kiransa sai naji kira na dauka jikina na rawa na zata shine sai naga bashi ba ne Zainab.
Sai da jikina ya yi sanyi ina Dauka ko sallamata bata amsa ba tace"Shikenan sai ki yi mana haka Maman Amir..?
Ta fada a sanyaye cikin wani yanayi nace"Ba haka ba ne Zainab shi bai fad'amiki yace baya son Datti a gidansa ba..?kinga kuwa tunda ni Datti ce ya kamani da kwarto bai kamata kuma na koma masa ba"
Cikin damuwa tace"Duk ya fad'amin komai wlh yace kishin ki ne ya rufaimai ido ammh ba har zuciyarsa ba haka ba ne,ga shi nan da zazzabi ya Dawo sai rawan sanyi yake yi yana kuka yana Kiran sunan ki"
Sai naji dadi ko banza shima zai ji abunda naji acikin raina.
Cikin Mirmishi nace"Allah ya ba shi lafiya bani da abunda zan yi masa bakin Alkalami ya riga da ya Bushe zainab.."
Cikiin wani irin sanyu tace"Yanzu shikenan Maman Amir..?
Sai naji nima Tausayin ta ya kamani Cikin karfin hali nace"Shikenan ba shikenan ba. akwai amanar ya'yana a wajen ki zainab ki kularmun da su ki yi kuma Hakuri da su ki yi musu Gyara a inda suka yi kuskure, Allah me ya had'amu ba Ishaq ba saboda haka bai isa ya rabamu ba zamu cigaba da waya da zumuncin mu in sha Allah"
Cikin Tausaawa tace"Hakane ina yi miki Fatan Alheri Allah ya bada zaman Lafiya"
Na amsa mata da Ameen ina so na tambayeta yaran sai kuma na kasa haka muka rabu zukata ba Dadi.
Ita kanta Zainab tasan Alhakina ke Bibiyan Ishaq,daman tun kafin dawowarsa Daddy ya kirata ya fad'amata ga yadda abun ya kaya ta sani har ga Allah bata bakinciki da Dawowar Fa'iza ammh tayi farinciki da ya rasa ta, ko domin haka ya zame masa izina gobe ko kashi ya aura sai ya san yadda zai iya Daraja shi.
Ni ko muna gama waya na bama Nana Fatima Labari daman tana Dakin cikin Tausayawa tace"Allah sarki. Sai ta bani Tausayi,ai yaran suna gidan Anty Fadila tace jiya tana gidan Baban zainab din ya kira yake fadin abunda ke Faruwa, sai ta tafi da su kada su ji labari su fara kuka tunda suna ta Murnan Umman zata dawo"
A raina nace"Ai ko Umma bazata Dawo ba har Abada"
Naji ma damu ammh jin suna tare da Anty Fadila sai naji na samu natsuwa.
Sai wajen sha Daya su Abba suka shigo muna daki Badariya tazo tana Fadin ga su Abba chan har da Engr sun zo gai da su Inno da su Goggo.
Ni dai leke nayi ta yi ta Labule har da Dr.Lawal mahaifin Zainab ko kunya.
Ni dai gwanina na rika d'age ina son gani a chan na hangosa kasa gaban su Inno kansa duke ya sanya Shadda mai ruwan kasa hular kansa na hango duk da yana Duke ne ammh duk yafi su Abba tsawo shiyasa na hangosa.
Sun jima ana ta dai yan nasihu kafin Naji ana cigiyata kamar an jefoni haka na fito daman na saka Hijabina har kasa,nasan idanuwansa na kaina shiyasa ban yarda na Dago mun hada ido ba. har kasa na duka na gaida su Abba.
Inno ce ta kalli Engr tana fadin"To kai Ango an ce kuma zaka yi tafiya kasashen Turawa wa zaka bar ma amanar amaryan taka..?
Tafada cikin zolaya kai tsaye yace"Nan zan bar muku ita Hajiya har sai na dawo sai ayi shirin tarewar nata in sha Allahu"
Sai inno tace"Au to na zata ai wayau zakayi mana ka dauketa kai kaita cikin yan'uwan ku yarbawa"
Gabadaya aka saka dariya tunda cikin Sigar wasa tayi mganar shi ko sai so yake mu hada ido naki yarda ina zan yarda ya bani kunya gaban su Abba.
Sallama ya yi musu bayan ya sauke ma su Inno kudi suna ta saka albarka Abba ya gabatar da Dr.lawal sai kika ji Allah Sarki na tashi.
Da suka fice kasa fita nayi ina kunyar Abba sai da Ammi tace naje mu yi sallama da mijina,ko alokacin kasa bin shi nayi sai da ya kirani a waya yana Fadin"Kuna shikenan zan tafi ban yi sallama da iyalina ba Faa'iza.?
Dole na fita yana zaure su Abba kuma na waje jikina ke kyarma na zata zai rikeni ammh wlh ko Tafin hannuna bai Taba ba,sallama kawai mukayi ana ta kiransa a waya yace zamu tattauna in ya samu natsuwa haka ya tafi yana Dagamin hannu ina Dagamai kamar kada ya tafi.
Koda na dawo cikin gida sai naji kewa sai dai fa har suka isa Abuja muna waya kamar ta bakinsa manne mata makale mata kenan..

  Washegari Litini su Abba suka koma Kaduna Yaya Asiya ma ta koma kano,Badariya ma Direba yazo ya Dauketa ta Dau Hanya Gida ya rage dagani sai Nana Fatima sai baba Ati,Inno an tafi da ita Saboda zuwa asibiti.
Nana Fatima sai talata ta tafi Ammi taso na bisu nace mata zan taho Daga baya tace gyara zatamin na sosai,Nima ina son na gyara din Domin Farincikin Engr shi kadai nake so tunda nima yake sakani Farinciki shima ina son saka shi,100k ya turomin yace kada na kara tambayan Abba komi shi zai yi min yanzu sannan bai ce nacigaba da wannan sana'ar na wahala ba, sai mun tare sannan zamu zauna  mu zamanantar da al'amarin yadda bazan rika wahala ba., Yana chan fa bai barni ba daya samu Sarari sai ya taboni,sai dai ko in aiki ya yi masa yawa na rasa wani irin so Engr ke yi min haka Mamansa da Yan'uwansa ya basu lambata haka zasu kirani suna gaisheni Mamanshi kuwa ba dai kirki ba in ta kirani haka zata rika ce min"Ba dai matsalan komai ko..?
In nace mata babu sai tace Allah ya yi muku albarka dukkan ku Allah ya baku zaman lafiya"
In na fad'amai sai yace"Sweetheart haka take bata da  damuwa Faa'izaa"
Yana chan mun yi mganar Lefe sau daya yace dai sai ya Dawo mganar in da zan zauna ma yace ya fasa bani Zabi yaga in ya Biyemin zan cuceshi ne.
Saboda zan zabi nesa da shi, shikuma wlh kara'in Holewa zai yi ba ruwansa.
Engr. Uhmm sai da na had'u da shi na farajin ashe nima macece kamar sauran mata..?
Shi d'in ya wuce namiji,gwarzo ne ta kowani Fanni.

*Janafty*

*KNKB3016*

*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

*ENGINEAR ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLUWATOSIN*
Chapter 47 · 0% Book details