← Book details Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 71

Sashe 27

Kana Naka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bana gida ma Lokacin ina gidan Raliya ni da su Hafsah Ammi tamin waya,daga gidan Raliya Ashiru Direba  ya wuce damu kasuwa nayo cefane,a hanya ma muna ta waya da su Anum sun samu wayar Mama,Amir ne kadai bamu yi mgana ba shi bai cika karamniya ba. sai mu yi waya da sauran yaran sau nawa shi bamu yi ba ko yana daki ko yana karatu baya son damuwa sai dai mun yi waya da shi ta wayar Jamal in yana gari zai saki jiki mu sha Hira da shi na lura Shirgin yaran ne baya son shiga gudun reni.
Tare da su Hafsah muka yi aikin Tuwon Shinkafa mukayi da miyar Allayahu wacce taji kashin Rago da manshanu sai Ferfesun kayan ciki da priderice,sai Fruit salat sai nayi musu kunin Aya ga zobo,sai lemun kankana,sai yammah muka gama muna gamawa ana kiran sallar mangariba Ammi bata da ko yar aiki komai ita ke yi da kanta,su hafsah na bar ma gyaran kitchen din ni kuma na tafi yin wanka nayi sallah ba Karya nagaji sosai shiyasa ina fitowa daga wanka nayi sallah na kishigida ina azkar barci barawo nata son sace ni karar wayata yasa na zabura Jummala ce ta kirani kan mganar gidan Alhaji Bukar na cikin gari sun turo da kaji talatin za'ayi musu Dambun kaji na girgiza kai ina fadin"Kai aikin ya yi yawa jummala..?zaku iya kuwa..?
Jummala tace"Zamu iya maman Amir ga Zainabu ta dawo ma, sai nayi ma su laure mgana su Auwalu sai su tayamu Matsewa"
Kai na jinjina kafin nace"Sun hado da kayan yi ne..?
Kai tsaye tace"Ban duba ba tukunna"
Ban damu ba nace"Duba bari na kira Goggo mu yi mgana"
Goggo na kira bayan mun gaisa na fadamata yadda muka yi da jummala Goggo tace"Sai su yi ga su Auwalu ba komai zasu iya, da  kina nan ai kun sha yin masu yawan su"
Jin haka yasa sai nace to shikenan bayam gama wayarmu da Goggo ashe ma matan gidan Alhaji Bukar ta kirani sai na kirata daga baya mukayi mgana tace an ce bana nan,ammh sun kai ma Jummala nace ta fadamin kada su damu za'ayi ammh sai nan da kwana Biyar zasu samu tace bakomai sun san ka'ida na ko wacce kaza daya Dari takwas ce nake yi tace zasu hada su Turomin kudin aikina ta banki da haka muka rabu cikin Karrama juna.
Sai daga baya na kira jummala na fad'amata yadda zasu yi tunda tace sun kawo komai da komai harda kayan kamshi,wayar ne ta Daukemin Hankali har akayi isha'i na tashi nayi salla barci ne malale a idona shiyasa na koma na kwanta saman gado sama sama naji mganar su Hafsah kamar wacce ta sha wani abu na kasa tashi,sai asuba shima sai da Ammi ta shigo ta tasheni na tashi ina jin kaina yamin nauyi.
Ban ko san yadda bakin Abba suka kare ba sai da safe na shiga gaishesa ya Turomin tulin kudi gabana na kallesa da mamaki ina fadin"Kudin miye wannan Abba..?
Kai Tsaye Ammi dake kusa tace"Kudin ki ne jiya bakin Abban ku suka ce a baki Tukwici da godiya"
Ido na kwalalo,cikin mamaki kafin na samu bakin mgana Abba ya yi dariya yace"To rufe bakin mana Fa'i"
Ganin yadda na bude baki cike da mamaki,da sauri na rufe bakin ina fadin"Abba naga kudin ne da yawa..?ni fa yarsu ce Abba don ma nayi ma abokan aikin ka girki bai kamata su biyani ba wannan kudin ai kamar biyana suka yi"
Abba yace"Wlh haka na fad'a musu suki jin mganata sun so ma kizo ku gaisa akaje kin riga kin yi barci. nace a kyaleki sunce kema yarsu ce ba Kyauta ba ne Tukwaici ne"
Sai naji na kasa mgana Ammi tace"Dubu Dari ce cif Fa'iza sai a kara jarin Turaruka.."
Ina mirmishi nace"Allah ya biya su da aljannah kamin godiya sosai Abba"
Abba yace'In sha Allahu"
Ammi na daukan bandir daya na kudin take fadin"Kowanne goma ya bata kenan..?
Abba yace"Ban sani ba fa. ni naga dai suna tarawa waje d'aya"
Ammi tace"Tab..don ma ba babban Gwaska kenan Engr da kila sai a takarda check"
Abba na Dariya yace"Maman Nana ke dai kina kaunar Engr din nan"
Ammi tace"To dole na kaunaci Engr da zuru'arsa mana Baban Nana suna da kirki da Dattako ga harkan girma. karon farko fa kyautar dubu Dari ya yi min Baban Nana ina zan manta da wannan kyautar,nayi takaicin rashin zuwansa jiyan nan wlh"
Abba ya girgiza kai yana kallo na kafin yace"Fa'i kina jin maman ku ko..?
Ni ma mirmishin nayi ban ce komai ba Ammi tace"Wlh da yazo da Fa'i taga kyautar girma"
Abba yace"Kila yana da abu mai muhimmanci ne shiyasa. ni dai yace  min ayi mai afuwa ammh na bisa bashi zai zo har gida ya gaida Maman nana da Diyarta da gajiya"
Ammi tace"Allah yasa dai yazo rabonsa da gidan nan tun murnan auran Nana fatima da ya zo maka Bayan ya dawo kasar na Abdul'ahad a waya kuka yi abun ku bai zo ba"
Abba yace"Yana da ayyuka da yawa ne kinsan Babban mutum irin haka Allah yasa kada tafiya kuma ta kamasa zuwa wani wajen"
Ammi ta amsa da Ameen suna ta Tattaunawar su ni dai sallama nayi musu Abba yasa na kwashi kudina zuwa shashen Inno nan nake zuwa mu sha hirarmu in su Hafsah sun shiga makaranta.
Na nuna mata kudin ta yi ta saka albarka da na matsa ta Dauka sai ta kalleni tana Fadin"Shikenan komai sai kin bani Fa'iza..?
Ban ce komai ba ta saka Hannu ta dauki Dubu biyu tana fadin"Na dauka Allah yasa albarka ni da ba abunda na rasa baban ku da mamanku tun kafin nace ina bukatar abu suke min. kuma ga ku kuna iya bakin kokarin ku Allah yadda kuka ji kanmu Allah yasa kuma naku ya'yan su ji kan ku'
Na amsa mata da Ameen Ameen muka ci gaba da Hira,ina jin dadin zaman kaduna alherin da na samu na kudi ban san iyaka ba sana'a nada dadi da amfami mu tashi mu nemi sana'a sannan mu kuma gayama Allah
Cikin Hirar ne take tambaya na ya wajen yarana nace duk suna Lafiya cikin mganar su na manya tace"Fa'iza kina ganin bazaki ba ma baban yaran nan wata dama ba..?ya yi nadama zuwan sa gidan nan ba adadi yana zuwa gaishemu kuma cikin neman ki koma ne Fa'iza"
Ina jin nauyin Inno sai na kasa mata musu,Ishaq ya riga ya samu kan Abba da Inno harda anty Fadila ko da yaushe muka yi waya sai ta fara korafin na dawo gidan mijina na zauna da ya'yana Abba dai bai taba min mgana ba sai dai a yanayinsa na Fahimta,ga Inno ma tagaji ta furta kaina na kasa na kasa mgana sai ta jinjina kai kafin tace"Ki yi Tunani ko Saboda yaran nan Fa"iza. ko wani aure da na shi kalubalen yanzu bama shi ba ko Ahalinsa bamai kara takaki kina da komai da bazai saka namiji ya rainaki ba. ga yaranki sun kawo girma ki yi tunani a matsayinki na uwa ko Saboda ya'yan ki"
Tafada cikin wani yanayi na lallashi,kafin ta gama mganarta hawaye sun kawo ido na,Inno ta Cigaba da fadin"kuma in ki duba kina da kuruciyarki bai kamata ki kare rayuwarki ba aure ba, ko ki yi Tunanin koma ma uban ya'yanki ko kuma ki fitar da wani mijin ki aura ammh a shawarata da hangenmu na manya gwara ka koma inda ka saba ka kuma sani da ka koma inda baka sani ba Fa'iza, sannan ko bakomai akwai zumumci tsakaninku ko ba'a duba komai ba a duba zumumcin Tunda Allah ne ya Umarcemu da mu yi zumunci kuma mu rike zumunci wlh wutar Allah zataji wanda bai rike zumunci bai kuma taimaki zumunci ba"
Ni dai na baro shashen Inno ina Hawaye yinin ranar a kwance na yi sa ya tadomin wani tsohon ciwo ne daga abunda ya shafi rayuwata ina neman in binne mganar Ishaq,ammh sainaga kamar yanzu ne ma suke neman tadomin da ita Tsausayi yake bama kowa yanzu har Yaya Mariya da a baya take adawa da shi yanzu ta dawo itama tana min mgana komawa gidansa,Harta ko Da goggo itama abunda take fadamin kenan,su Anty Binta da su badariya sun gaji da rokona na koma har sun gaji Zainab ma har gobe bata Hakura ba ni Uban gayyar bana jinsa sai dai gabada'ya ya Nannade dangina da Nadamarsa da kirkinsa,A satin kaf naji kaduna ta fita raina saboda matsawar Inno kan mganar  Ishaq,Sai na dai zuwa na zauna a shashenta ita kuma in dai naje sai ta Tsaidani da nasiha da tunasarwanta.
Chapter 27 · 0% Book details