← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 128

Sashe 99

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dudda batasan ko'ina ba dan ita bata taba zuwa kaduna da wayonta ba, sanan tsawon zamanta a gidan Baffa saida zasu kasuwa dawurin kapinta ne ta taba fitowa daga anguwan nan, but ganin yanda yake zabga gudu yasa gabanta yafara faduwa sosai ahankali tace "har yanzu bamu kaiba?" cikin muryan matan yace "yanzun nan zamukai, munkusa" sunyi tafiyan kaman na minti goma sha biyar saida yabari suka fita daga kawo sukadau hanyar zaria sanan ahankali ya gangara gefen titi yay parking tareda kashe motar, da sauri Aneesa datai wani irin danji tayi duk hankalinta yatashi ta kalli hanya ganin inda suke bakin dajinema kan hanya babu mutane ko daya awurin sai motoci dake gittawa daidai yasa da sauri tajuyo ta kallai gabanta nafaduwa sosai tace "anan ne Ammi na take?" ahankali Aliyu ya ciro fararen hannayenshi daga hijabin yakai hannun yazare glasses din kan idanunshi ya ijiye, wani irin bin hannunshi da kallo Aneesah take ga hannu wan farare tass kaman na ta mace kaman na namiji, ahankali yakai hannunshi bayan nikabin ya warware kullin tareda jan nikabin awanin irin hankali harya zareshi daga kan fuskarshi, wani irin mummunan faduwa da gaban Aneesah yayi saida tazabura tadafe kirjinta, dago jajayen idanunshi yayi yadaura akanta yana mata wani irin kallon So, shauki, kewa, kauna da bege dakuma fushi kafin ahankali yasa hannu yazare hijabin daga jikinshi gabaki daya ya yaye ya dunkule ya jefa a kujeran baya yajuyo ya kalleta yana gyara zaman riganshi, wani irin zabura Aneesah tayi kafin arude tasa hannunta ta shiga kokarin bude kofan motan danta fita daga motar, ahankali cikin sassanyar muryan shi yana kallon yanda take kicinyar bude motar yace "kozaki kwana kina kokarin bude kofar motar nan bazai taba abuduwan mikiba Fateema!" juyowa Aneesah tayi da sauri ta kallai hawaye yasoma taruwa a idanunta, gabanta nawani irin faduwa, bakinta narawa sosai tace "y.....y....ya akayi kasan inda nake?" kallonta yayi ido cikin ido wani irin azaban sonta na dakan zuciyan shi yace "inba dai aturbaya zaki boyeba ko ina abinda nakeso yaboye aduniyan nan zan iya nemoshi Fateemah!" yanda yake mata magana asanyaye kaman mara lafiya yasa taji jikinta yadau rawa, da sauri bakinta narawa har lokacin tace "k.....abude mini kofa nakoma gida yaune bikina kabude min kofa kafin afara nemana, kabude min nakoma gida" murya chan kasa yace "keda gida har abada Aneesah" wani irin kallonshi tayi hawayen daya taru a idanunta suka zubo sharrr, da sauri ta share hawayen tai dan murmushi tace "you are joking right? Please I take this as a joke, kindly take me back home Aliyu, kar kasa afara nemana agida, yanzun nan za'a dauramin aure" wani irin dukan gaban motan Aliyu yayi cikin fushi yay ihu dasaida ya firgitata yace "stop telling me yanzunan za'a dauramiki aure, bakida wani miji sama dani aduniyan nan cus I Love you, I love you Fateema, I love you" har zuciyanta taji kalaman I love you daya fadi mata, lumshe ido tayi da sauri tana hana kanta kukan dayake shirin zuwan mata tace "banason ka ni Aliyu, babu abinda zanyi dakai, babu abinda zanyi da wanda aka min shirin kisa akanshi, babu abinda zanyi da yaron da mahaifinshi yaturani gidan yari akai, Aliyu yanzu bada bane I don't want anything dat has to do with your family, so am telling you one last time bana sonka, bana bukatar ka arayuwata, kabudemin kofa nafita nakoma gida" wani irin girgiza mata kai Aliyu yayi yana dafe kirjinshi dakemai zafi kaman an yaba dalma akai yace "Anebaby! Society da invaders, my parents or yours, family issues ko abu makamancin haka are too small to break the bond of our love, Aneesah am sorry for abinda mahaifina yamiki, My Dad wronged you and I am sorry, I never wish for any of that to happen, kin manta soyayyar mu Aneesah? Have you forgotten the type of love we shared? Kin manta da salon soyayyar mu, kin manta da soyayyan mu Aneesah, are you willing to give it up? Are you willing ki saki soyayyan mu tabi iska sabida wasu? What about me love? Wat about my precious heart that knows no one banda ke? What about my soul, my body that yarns you only? Aneesah soyayyar mu, our love" shiru Aneesah tayi kuka kecin ta amma ina bazata yishiba, wani irin murmushi ciwo tayi tace "Aliyu kenan, mahaifinka yariga yaraba soyayyar nan dakasani, banda hakama ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu wata kyakyawar tsaftatatcciyar soyayya ta shigo, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu akwai wata soyayya, IN BETWEEN OUR LOVE lies another love which I cherish, I have my man now da zuciyata ta aminta dashi, wanda mahaifiyata ta aminta dashi, yan uwana suka aminta dashi sanan suka soshi, mutumin daya rufamin asiri yasoni despite my flaws, he helped me rebuild my self and gain my confidence back Dr Hafiz Zaid, My husband to be wanda nake bala'in s........." "shut up!" Aliyu yamata wani irin mahaukacin ihu yana buga jikin motarshi kaman zai fasa da kafa, yasake ihu kaman wani zakin daji yace "shut up, stop telling me kinason another Man, Fateema u are my wife, u are mine, only mine, and am gonna show u that today, bakida wani miji inhar am alive a duniyan nan sama dani, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu babu wata soyayya, babu wata soyayyar data isa ta shigo TSAKANKANIN SOYAYYAN mu, IN BETWEEN OUR LOVE lies no any love, you are mine Mrs Aliyu Hydar Gadanga, you belong to me, and inhar abu nawane baya taba zama nakowa, zuciyar ki na tareda sona we love each other, family issues ko anything is too small to break d bond of our love, we are connected, gap din da iyayenmu sukai creating ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu zamu ciketa, me and you are inseparable, and I love you very much" yana gama maganan yawani irin kunna motar kaman mahaukaci yajata, arude Aneesah ta kallai saikuma tasaki kuka tamugun tsorata da yanda taganshi yanajan motan ko idanunshi ma baya budewa da kyau tsabagen fushi da masifan zuciya, ganin sun cigaba da tafiya ne baimada niyyan komawa baya yasa tafashe da kuka tace "na shiga uku, ina zaka kaini Ya Aliyu, ka maidani gida, Ammi na zata nemeni, ka maidani gida" ko kallonta baiyiba sai gudun daya cigaba dayi, bakaramin bakanta mata rai abin yayiba, cikin fushi tanuna shi da yatsa hawaye nabin idanunta sosai tace "zakaja namaka illa wlh, Aliyu take me back home nagaya maka, wlh zanji maka ciwo" batare daya kalleta ba yace "do me a favour and kill me, ki aikani lahira shi yafimin da in bude idona naga kina auren wani wlh I will never allow that to happen saidai in bana numfashi" cikeda fada tai ihu tace "to me ruwanka dani haaa? I don't love you bana sonkai nace, dole ne, where are you taking me to, karabu dani, kaga Aliyu ka komar dani gida kona jimaka ciwo wlh" murya chan kasa yana numfashi ahankali ahankali kaman mai shirin suma yace "ki kasheni kinji Barkono" duk zuciyanta kasamai komi tayi dan gani tayima baida lafiya karfin hali kawai yake yana mata bala'in nan kaman ma baya gani da kyau sabida yanda yake kyapkyapta ido yana tuki da masifan gudu, fashewa dawani irin kuka tayi ta kife kanta akan cinyarta hankalinta ya matukar tashi tace "Aliyu me haka, me amfanin satoni dakayi? Baka da lafiya, ina zaka kaini eh? U are risking our lives, Aliyu dan Allah ka komar dani gida kar hankalin Ammi yatashi" dudda yanajin kukanta har zuciyan shi amma ko kala baice mataba harsukakai garin zaria yadauki hanyar gidan sarkin zazzau.
Chapter 99 · 0% Book details