← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 128

Sashe 30

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Dady yace "nose bleed kuma Aliyu, mekuma yakawo maka nose bleed ana zaune lpy?" yay maganan yana kai hannu zai taba hancin Aliyun da tip din yay jajir, da sauri Aliyu yarike hannun yana kawad da fuskan shi dan baiso ataba dan zafi zaiji yace "nikarka tabamin hanci am fine, ba zafi yakemin ba kuma tuntuni ya tsaya, are you just coming back now Dad? ina kaje kadade haka?" goran ruwan da Dady yagani kan table dinshi mara sanyi ya dauka tareda budewa zai sha yace "bamu gama meeting din dawuri bane, and on my way coming back kuma something happen saida na taimaka ma wata mata da yarta batada lpy na kaisu asibiti gwanin ban tausayi wlh" dan lumshe ido Aliyu yayi tareda shigewa cikin kujera more yace "am sleepy Dad" hanunshi Dady yaja yace "tobaza kaje ka kwanta ba afalo zaka kwana? Ehen Gadanga na that reminds me of something, taso kaji wata magana, tashi, tashi kaji" yadaga Aliyun da sauri yana dan murmushi, turo baki Aliyu yayi kaman zaiyi kuka yatashi zaune yakallai yace "uhmm tell me" matsowa kusa dashi Dady yayi sosai yadaura hanunshi akafada yace "daman kagane wanan aminin nan nawa Alhaji Hassan?" dan yatsine fuska Aliyu yayi yace "what about him?" murmushi Dady yayi yana kara matsowa kusada shi yace "to agidanshi mukaje meeting dazu dana fita, yarshi ce tazo tai serving dinmu, na yaba da hankalinta da natsuwan ta, kasan tareda sukayi school da kanwar ka Hajara a Dubai, sa'an Hajara ce, she's just 24 Zainab, na yaba da natsuwan ta, tama cemin gobe zatazo wajen Hajara, inaso idan tazo kusasanta ka aureta Gadanga, so karkaje ko ina inaso ku sasanta ka aureta batada matsala very quite and obedient girl, kaga yanda kakeda shegen zuciyan nan you need yar yarinya maijin magana, mara hayaniya dazata bika sau da kafa, is just the best choice Son namaka trust you Dad" dariyan iskanci Aliyu ya shiga yi irin na sangartattun yaran nan, Dady yabude baki yana kallonshi instead of yamaji haushi saima washe baki yayi arayuwan shi yanaso yaga Aliyun shi na dariya, yanaso yaganshi he's free and very happy, da kyar Aliyu ya tsayar da dariyan yace "are you for real Dad, like are you serious about this eh Babana?" da sauri Dady daya tsaya yana kallonshi kaman wani TV yana murmushi yace "yes now Boy, am serious, nafada maka she will make a best wife" dan tabe baki Aliyu yayi yadauki wayarshi yana kallo kafin ya dago kai ya kalli Dady yace "please, please Dad kaga am begging you don't start with this neman min mata stuff, am I a kid daza ka wani nemomin mata, ni nama isa aure ne?" baki Dady yarike yana kallonshi yanda yakemai maganan yana turo baki sounding serious saikuma yay murmushi yana girgiza kai yace "kace kaikama isa aure ne, sanan kace are you a kid, wat does your statement and your question makes you now?" dan murmushin rashin gaskiya Aliyu yayi baice komiba ya dauke kai hakan yasa Dady yadanyi dariya yace "stop taking the advantage of the love I have for you Aliyu, kasan dai burin kowani uba ne yaga danshi yay aure ko, I want to see my grand kids Aliyu, banso namutu banga y'ay'anka ba Aliyu" da sauri Aliyu ya kallai jin kalman mutuwan daya fito daga bakinshi dan ko kadan baiso yaji Dady ya ambaci kalman mutuwa, gyadamai kai Dady yayi ganin tarkon daya dana mai yakamashi dan finally yasami full attention nashi, hakan yasa yasake kwantar da murya yace "yes Gadanga, banso namutu banga jikokina ba, kasan shekara na nawa yanzu aduniya? Talatin da takwas ga ishirin da tara ka lissafa, inada shekaru talatin da takwas aduniya mamanka ta haifamin kai kaga yanzu shekaruna sittin da bakwai, rayuwa taja Aliyu, Aliyu tai nisa kullum kara kusantowa da kabari mukeyi, nasan bazan taba kara shekaru dari akan wanan shekarun nawa ba, idan ma nakara to komi mini za'a dingayi" dan shiru yayi yana kallon yanda maganganun shi sukasa Aliyu yay sanyi sosai, dan fuzar da iska Dady yayi yace "is alright, naji nakuma yarda bazan nemama mata ba, konima nafison kazabo mata kafadamin choice dinka, na tattaro abokanai na da yan uwa muje munema maka ita but promise me zaka fito da mata nan da one month, you are 29, a graduate, har masters kanada shi, your company na running perfectly fine wat else kake jira? Promise me zaka fito da mata kwanan nan Son" dan lumshe ido yayi yana ganin fuskar Aneesa namai murmushi kafin ahankali yabude idon ya kalli Dady, hannun Dady yakama yarike ahankali yace "I promise Dad, and karka karamin maganan mutuwa, nothing will happen to you, jikoki harsaika gaji, duk wacce zan aura triplets triplets zata dinga haifowa and every year so get ready jekokin ka will break all your bones and fibers" dariya sosai Dady yayi yace "haka nake so ai, abun nema kenan hausawa sukace wai matar direba ta haifi mota kaga ai tuki har nijar" yasake fashewa da dariya kafin yay shiru ya shafa gashin kan Aliyun yace "nagode Aliyu na, yarona maijin maganan babanshi, Allah yamaka albarka kaji" murmushi yayi yace "Ameen Dad" hanunshi da har yanzu bedawo normal ba Dady ya karba yana kallo yace "tell me the truth what happen to you dazu Aliyu, eh what happen to you? Why were you so angry dazu?"
Dan shiru yayi yana tunanin abinda yafaru dazu da sauri ya kawad da tunanin daga ranshi danji yake kaman zai sume, ahankali yace "never mind Dad, I don't wanna talk about it" dan murmushi Dady yayi ganin baiso yafada mai, amma dai yaso yaji meya sameshi yace "Alright bari naje na watsa ruwa na kwanta, kaima saida safe, jeka kwanta dan ka iya zuwa masallaci da asuba" tashi yayi yana kallon Dady saida yafita sanan yawuce bedroom dinshi singlet din jikinshi tacire dudda dazu yay wanka jiyayi yanaso yasake yi kuma koyaji dadin jikinshi, bathroom yabude ya shiga yakai almost 20min a bayin sanan yafito ya shirya tsaf cikin wani milk color pyjamas ya kashe wutan dakin yarage saura bedside lamp kadai yazo yazauna bakin gado, kasa hakura yayi yadau wayarshi ya shiga contact din Aneesa dayay saving da Boldest yana kallo, bala'in son yakirata yake at the same time kuma baiso yakirata abinda yafaru dazu na mugun bakanta mai rai, kwanciya yayi ahankali kan gadon yadaura wayan kan kirjinshi tareda fuzar da iska dan lumshe ido yayi yana tunane tunane ahaka bacci yay awon gaba dashi.

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
2️⃣4️⃣

_duk wacce takaranta bata biyaba Ban yafeba_
Wuraren karfe biyar na asuba Dr dawata nurse rikeda paper suka shigo dakin, Ammi dake rikeda hannun Aneesa dahar lokacin ke bacci bata tashi ba hancin ta har lokacin da oxygen dan she's really finding it difficult to breath shike bata support, ganin Dr sun shigo yasa Ammi tasaki hanunta ta mayar ahankali ta ijiye ta mike tsaye tana kallon Dr tace "Dr har yanzu bata tashi ba, meke damunta dan Allah kufada min?" karasowa gaban gadon Dr yayi yana mikama nurse din papers din hanunshi yana cire stethoscopes daga wuyanshi yace "don't worry Ma, your daughter will be fine, tana bukatan baccin nan dakikaga tanayi" yay maganan yana sauraran heart beat dinta saida yagama dubata tsaf sanan yadau wani allura dasuka taho dashi yama drip din da aka makala mata alluran sanan ya karbi paper hanun nurse din yana rubuce rubuce, saida yagama sanan yajuyo ya kalli Ammi tareda yimata murmushi yace "karki wani damu maleria ne ke damunta mai karfin gaske dan maleria ta yakai 4+, thank God kun kawota asibiti on time dazamu iya rasata but karkiji tsoro yanzu zamu barta on admission muna bata care nan da 2days muga yanda zata kasance, karki damu yarki zata sami lafiya saidai akwai abubuwa da dama daza'a kiyaye dazaran tasamu lafiya" ajiyan zuciya Ammi ta sauke bata iya cewa komiba sai kallon fuskan Aneesan datake yi, Dr yace "muje na nuna miki masallaci kije kiyi salla saiki dawo" gyadamai kai tayi tawuce tabisu suka fita yakaita masallacin asibitin dake kusada Gate, bangaren mata tawuce tai salla.
Shida saura yatashi daga bacci da kyar shima sabida Dady daya ta dashi ne ta hanyar kiran wayan shi, sauka daga kan gado yayi ya shiga bathroom baiwani jimaba yadauro alwala yafito ya shimfida dadduma dan anriga an idar da salla.
Idar da sallan yayi ya jingina da gado yana azkar yarasa mesa every single breath dazaiyi taking sai Aneesa tafado mai arai, dan fuxar da iska yayi yamika hannu yadau wayarshi dake kan bed yadauko yay dan jim yana kallon wayan kafin ahankali ya kunna yay dialing number Aneesan.....
Wuraren shidda tana zaune a masallacin asibitin tana lazimi wayar Aneesa dake tareda ita ya shiga ringing, da sauri ta danna gefe tai muting ringing wayan tana kallon number dake kira danba suna ajiki, bata daga kiran ba harya katse, aka sake kira akaro na biyu da sauri tai muting ringing din tana kallon number still number dazu ne shima bata dagaba harya katse, sake kira akayi akaro na uku yasa Ammi ta tashi tafita daga masallacin da saurinta tana kallon number tokodai yan lalle ne? Dan sune suka iyama Aneesa kiran safen nan dansu tambaya ko tana nan bazataje aikiba zasuzo, danna wa tai tai picking takai kunne cikin muryan ta irin na wacce tadan manyanta tace "Assalamu Alaykum" shiru Aliyu daya rasa sukuni so kawai yake yaji muryanta yayi jin ba muryanta bane, muryan babba ce, ciro wayan daga kunne Ammi tayi ta kalli wayan ganin har lokacin ba'a katse wayar ba yasa tasake maidawa kunne tace "Assalamu Alaykum, hello, hello banaji, waye? mahaifiyar Aneesa ne, batada lpy yanzu haka muna asibiti a asibiti muka kwana idan yan lalli ne karkuzo gida dan bama nan"
Wani irin faduwa gaban Aliyu yayi da inda yanada history heart problem saiya iya collapsing....
Jin still shiru ba'ace komiba yasa Ammi taciro wayan daga kunnenta tace "ba'aji network nada matsala wlh" tasake maidawa kunnenta tace "bama nan karkuzo lalle muna asibiti" tacire wayan daga kunnenta ta katse wayan.
Chapter 30 · 0% Book details