← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 128

Sashe 92

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Janye wayan Dady yayi daga kunenshi ya kalli Abdul dake tsaye gefenshi da baturen Dr Aliyun dayake tsaye shima duk suna jiran suji me Dady zaice amma yakasa magana sai Aliyun dake kwance kan gado an makalamai wasu irin abubuwa akan kirjinshi na asibiti yana numfashi sama da Kasa yake kallo, lumshe ido Daddy yayi alhakin Aneesah ke kamashi saisa abubuwan nan ke faruwa dashi, Rauda tarasu, Aliyu gashinan shima rai a hannun Allah, matayenshi dukya rabu dasu dan sune silan matsalolin shi, Rukayya tama tsani ganinshi, ga yaran shi duka agida Nannies daya dauko musu ke kula dasu, shi kanshi daurewa kawai yakeyi amma ko kadan baida kwanciyan hankali, dafa kadarshi da akayi yasa yadago kai Dr Aliyu ne, murmushi yamai yace "calm down Sir, I promise I will do everything in my power naga danka ya warke I promise you, just be strong for your Son" gyadamai kai Dady yayi yama kasa magana Dr yajuya yatafi, ahankali Abdul ya matso kusada Dady yace "Dady rana aka samata wai?" gyadamai kai Dady yayi ahankali Abdul zai saka wani maganan Dady yamike tsaye kaman wanda baida lpy yace "Abdul kazauna dashi ina zuwa" yafita Abdul ya bishi da kallon tausayi, a mota yasami bodyguard dinshi suka jashi sai gida, wuraren karfe goma da rabi suka shigo gidan, parking sukayi baima jira sun budemai ba yafito, flat din Ammi yawuce kofar yasa hannu zai bude yajita a kulle da sauri yay flat dinshi ba'a jimaba yadawo dauke da makulli yabude kofar, ahankali ya shiga babu kowa sai wanan mayen kamshin dakin nan nata dake tashi yay upstairs, ahankali ya tura kofar bedroom din Ammi da sauri Ammi dake kan dadduma tana addu'o'i ta dago kai ganin Dady ne idanunshi sunyi jajir yasa tadauke kai, ahankali ya shigo dakin tareda maida kofar yarufe yakaraso wajen dadduman yana kallonta, shafe addu'a Ammi tayi tamike tsaye tareda zare hijabin jikinta ko damuwa da yanda Dady ke kallonta batayiba gaban gadonta taje ta zauna tana kokarin cire dan kunnin kunnenta danso take tai bacci, ahankali Dady yazo wajen, zama yayi akasa tareda daura kanshi kan cinyarta yasaki wani irin kuka, to yama rasa mezaiyi abun duniya sunmai yawa, cikin kuka sosai yace "haba Rukayya, baki yafiya bazaki yafemini ba, nina miki laifi, ninama Aneesah laifi, please ki raba wanan zancen sa ranan Aneesah, don't punish my son over the mistake of his Dady, am sorry, bansan tayaya zan baki hakuri, kiyakuri badanniba badan halina ba kiyakuri dan Allah, ki tausayama Aliyu Rukayya, wlh natuba, nai nadaman abinda nayi" dago kanshi yayi da sauri suka hada ido da Ammi dake kallonshi kyam, ahankali yakama hannunta yana goge hawayen dake zubomai yace "naji ki rama dukan danama Aneesan, ki rama dan Allah kinji" ko alamun daga hannu batayiba hakan yasa yasaki wani irin kuka yana kallon yanda Ammi ke kallonshi yace "Rukayya wlh ina sonki kema kinsan hakan, kiyakuri for the sake of wanan cikin namu dakike dauke dashi kiyafe mini kibama Aliyu Aneesah" wani irin murmushi Ammi tayi tace "Alhaji kenan katuna sanda nake kuka haka ina rokonka ka sauraren? Ina ciwo ina fama da laulayi ina rokonka ka sauraren kamaji tausayina? Karabani da y'ata na kimanin sati hudu da kwana tara bansa abin sona araina ba kaji tausayina? Saidai kullum ka kama uwarta kana haiketa ba dare ba rana ba safiya ka maidani abinci amma y'ata nachan ka kulle ta agidan yari kaji tausayina?" lumshe ido Dady yayi wasu irin hawaye na zubomai masu bala'in dumi, tabe baki Ammi tayi tace "wlh d'a baifi d'a ba kaji yanda akeji, ciwo kuma Allah ne yadaura ma Aliyu shine kuma zai yayemai inyaga dama amma ko Aliyu na kakarin mutuwa ne bazan taba bashi y'ata ba kaje kajika dan gwal dinka kasha duniya daman fadi gareta dan hakin daka raina shike tsolemaka ido, danka baimin komiba yatace dai bazan bayarka kai amfani da kudaden ka da power ka kaje akero maka wata Aneesa ka kaima dan gwal dinka, sanan katashi please ka fitarmin daga daki cikin nan baison sautin kukan babba please saida safe" sosai yake kallon Ammi jikinshi yay sanyi yasan anacewa idan mutum mai hakuri yay fushi yanada wuyan sha'ani baitaba sanin abin yakai hakaba sai akan Ammi, tadau zafi bana wasaba, ko kallon rahama batamai kuma yasan shiyaja dan shima baimata kallon rahama ba. Yanaji yana gani tai kwanciyan ta tareda Jan bargo haka yadinga kallonta har bacci yay awon gaba dashi awurin.

_Kaduna_
Wuraren 9 bayan Baffa shida Na Sani suka fito daga masallaci ne sukai gida, afalon Baffa suka zauna sanan ya kalli Inna data shigo kawo musu abinci yake kiramini yarki Maman Hamma, murmushi Inna tayi tace to. Fita tayi ko minti uku ba'ayiba tadawo tareda Aneesah dake sanye da dogon hijabinta, tabarma Baffa ya nuna mata yace "zauna anan" zama Aneesah tayi ahankali tace "sannunku da zuwa Baffa" "yauwa Aneesa sannu" yay maganan yana karban ruwan da Inna ke bashi akofi sanan yace "kema zauna ayi maganar dake" zama inna tayi shikuma Baffa ya kafa ruwan abaki yasha iya shanshi sanan ya ijiye yace "masha Allah" kwalaye kwalayen dasuke jere afalon Baffan ne kusan guda ashirin da uku yay pointing yace "kinga wayan nan kwalayen Aneesah" gyadamai kai Aneesah tayi yace "kayan auranki ne, su goro ne, sweet dadai sauran su na saka ranan aurenki" wani irin faduwa gabanta yayi dahar saida Baffa ya gani yay murmushi yace "karki damu Aneesah, bazan miki karyaba wlh kinyi mugun sa'an miji, dan munje munyi usulin bincike abinki da haifaffen dan kaduna babu abinda bamu juyoba, Dr Zaid yaron kirkine shekarun shi talatin da shida aduniya, 36. Yataba aure sunyi zaman lafiya shida matarshi awurin haihuwa bayan ta haifomai yarshi mace Allah yamata rasuwa, sunan yarinyar Fareeda yanzu shekaran ta biyar, tun bayan matarshi ta rasu bai sakeyin wani aureba mahaifiyar shi ita ke tayashi rike yarinya, dudda an dameshi an dameshi yayi aure yaki dan acewanshi baiisamu wacce ta kwantamai araiba sai akanki, tun tuni yazo yanemi izini awurina akan yanaso ya nemiki idan babu kowa akasa na nunamai babu kufara fahimtar juna kafin jiya da daddare mahaifinshi ya kirani yace in sha Allah zasuzo yau mugana, shine gashinan babu maganan da mahaifiyar ki batasani ba, dudda tabarmana komi mune mahaifanki dama mukeda iko mu zabamiki miji sanan mu aurar dake bamu tauye mata hakki na matsayinta da uwa ba, dan har da baban yaron nahadata sun gaisa itama tai na'am dasu tace kome nayi gaskiyane, Ke mace ce Aneesah, rufin asirin kowace y'a mace shine gidan mijinta, baki komi agida, baki lalle, baki kitso, baki zuwa shago sanan baki boko, jamb dinki kuma sai shekara ta zagayo saisa naga tunda ga yaronan mai hankali, mai abin yi, kuma mai kaunar ki mizan jira gwara mu aurar dake dani da Nasani, da Innan ku, da mahaifiyar ki muka yanke wanan sharawaran nasan kuma aduk inda marigayi mahaifinki yake nasan yana farinciki da wanan lamarin na zani aurar dake, na rike amanar shi da kyau, yanzu ansa rana wata daya da sati biyu, muna fatan Allah ya kaimu lapiya sanan Allah ya sanya albarka a wanan auren" su Inna suka amsa da Ameen, Na Sani dake gefenshi ya kalla yace "kawo wanan kudin?" wasu yan dubu daidai Nasani yazaro daga aljihu sababbi yamikama Inna karba tayi yace "gawayan nan kudin, dubu dari uku ne, dubu dari iyayen yaro suka kawo kudin gaisuwan iyaye, sanan dubu dari mahaifiyar Aneesa tamin transfer dinsu dazu da yamma, Inaso kihada kudin nan ku mata kune kukasan kan kafintocin ku, kidau dubu dari da hamsin kisami kafinta daya iya gado da kujeru masu kyau kidau Aneesah kuje tare gobe in Allah yakaimu tazabi kalan kujerun datake so saiki bada deposit tunda kaman gobe ne zakiga wata daya tayi babu lokacin, daya dubu dari da hamsin din kuje kasuwa kusayo kayan kitchen da sauran kayayyaki da amarya ke bukata kindaisan yanda zakiyi dasu duk kiyi, in sha Allah kuma nida Na Sani zamu saida shanayen ta inhar an siya saimu karasa biyan kudin capita sai ayi wasu abubuwan da sauran kudin kinji" da sauri Inna tace "shikenan Baban Hamma Allah ya taimaka" kallon Aneesah da kanta ke kasa har lokacin Baffa yayi yay murmushi yace "dawani abunne Aneesah inkinada magana kiyi kinji banso na tauye miki hakki, kinada magana?" ahankali ta girgiza kai tace "a'a Baffa nagode" cikeda jin dadi Baffa yace "yauwa yar albarka, Allah yamiki albarka kinji, tashi kije ki kwanta gobe kinada zirga zirga keda Innan ku" tashi tayi ahankali tafita zuwa dakinsu fadawa kan gado tayi kuka kawai taji tafara yanzu so ake a aurar da ita, harda Ammi acikin maganan, shida tuntuni bai fadamata yana sonta bane sai yaune zai wani kame ya aureta wlh saiya sani Allah yakawo shi gobe. Sosai take kuka tama rasa meke bakanta mata rai, sosai Aliyu ke fado mata arai amma saita danne tunanin shi sabida maganganun da Ammi tamata, banda hakan ma haushin kowa na gidansu Aliyun take, shikuma Hafiz zai sani.
Inkika karanta baki biyaba banyafe mikiba.

Wasa wasa lokaci ke tafiya yau kimanin sati uku kenan batama saka Hafiz din a ido ba tun ranan dasukayi fada, ashe tafiya yayi yaje Sudan wani medical workshop na four weeks, kullum cikin gyaranta ake Inna tabata wanan tabata wanchan, yau amata farfesun ganda, gobe na cicibi, gata na azzakarin doki, haka dai take ci da kyar danba yanda zatayi idanunta sunyi zuru zuru duktabi tarame tarasa ita kanta meke damunta.
Chapter 92 · 0% Book details