Sashe 88
In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi tayi ahankali yana kallon fuskanta tafice, wanko fuskar nata tayi ta shigo dakin ta zauna abakin gado tana wasa da yatsunta, tasowa yayi yana gyara statoscope din dayake rikedashi yazo gabanta yace "meke miki ciwo yanzu?" batare data kallai ba tace "babu komi" hannunta yakama ahankali yay placing statoscope din yana sauraran heart beat dinta, sosai Aneesa ke kallon yanda yarike hannunta wani iri taji kaman shima ya lura da haka ne ya saki hannun yazauna a gabanta yana kallon fuskanta batare dayace mata komiba, dagokai tayi ta kallai kaman dama abinda yake jira kenan ahankali yace "kinjima yan uwanki rauni sosai, promise me zakije kibasu hakuri kinji yar kanwata" , gyadamai kai tayi da sauri yace "zakije da gaske?" gyadamai kai tayi alamun eh, murmushi yayi yace "ashedai kinajin magana kanwar nan tawa" murmushi tasakin mai for the first time tunda suka hadu jiya da mugun sauri ya janye kanshi sabida wani irin lotsawa da dimples dinta sukayi saida yaji kaman numfashin shi zai dauke yakuma rasa maisa hakan, mikewa tsaye yayi ahankali ya kalleta yace "gobe nazo nadubaki kanwata?" da sauri ta gyadamai kai, dan hararanta yayi cikeda wasa yace "waike baki iya magana bane, common talk to me, nazo nadubaki give?" murmushi tayi kafin ta juyar da kanta akunyace tace "kazo yayana" "shikenan I will come tunda kanwata nason ganina, bye" dagamai hannu tayi itama harzai fita sanan yasake juyowa da hannu ya nunata yace "No more fighting okay, promise me bazaki kara fada da kowa ba you will control your anger and d temper kome aka miki innazo kifadamin promise me" ahankali tace "I promise" murmushi yamata yace "and don't worry nasan duk inda Ammin ki take tunanin ki takeyi dan yarinyar ta akwai shiga rai, zata kiraki am sure" murmushi tamai sosai fiyeda nada sabida yanda yabata assurance cewa Ammi zata kirata, hakan yasa yajuya da sauri yafita hango fitowarshi yasa! Baffa yafito daga dakinshi, hannu Baffa yabashi bai karba ba saidai dukar dakai dayayi kasa yace "zan tafi Abba" cikeda da so Baffa yace "nagode sosai likita Allah yay albarka kaji likita, mun gode, wai ya sunan ne inata kiranka da likita" Baffa yay maganan yana dariya irinta manyan nan, ahankali Dr yace "sunana Hafiz Abdulwahab Zaid, saisa Dr Zaid yabini but Zaid din sunan kakanane" gyadakai Baffa yayi cikeda gamsuwa yace "masha Allah ba shakka, sunan mai dadin gaske, Allah yayi albarka Hafiz, Allah ne kawai ya aiko mana dakai, nagode sosai Allah yay albarka" sosai yakeso yama Baffa maganan Aneesa amma yana mugun jin nauyi hakan yasa yajuya yatafi Baffa yarakashi har kofar gida, bude motan yayi ya ijiye akwatin kayan maganinshi sanan ya zauna yatada motar yana tunane tunane Aneesa ta shiga ranshi ta zauna daram yarasa mesa tunko jiya dan bacci rabi da rabi yayi yana tunanin ta saisa yazo da wuri danda yay niyyan sai da daddare zaizo amma yakasa daurewa ya shiryo yataho yana zuwa kuma hayaniya da ihu dayaji yasa yafada gidan nan yaga aika aikan da Aneesa takeyi, Allah ya gyara yarinyar nan she seriously need therapy and insha Allah kadan kadan ahaka zaita bata har saita gyaru.
Gaban wani tangamemen gida a GRA yay horn budemai kofanBudemai kofan akayi yaja motar ya shiga ciki gidane babban gaske irin na yan gayun nan, parking motar yayi yasauko yana tafiya ahankali har zuwa flat dinsu bude kofa yayi, wata yar matace dakana ganinta zaka gane mahaifiyar shice a zaune sabida mugun kaman dasuka yi tana binshi da kallo wata mata haka na gyara mata kumban hannu, maida kofar yayi yarufe yace "Mum sanunku" hararanshi tayi ta kalli matan datake gyara mata kumban tace "please excuse me Charity" da sauri matar tabar falon, ganin haka yasa yafasa zuwa saman ya zauna kusada ita zaiyi magana ta kama lips dinta tace "kamin shiru I didn't ask you to talk" shiru yayi yana kallonta, cikeda masifa tace "zan sabamaka fa Hafiz, Allah inhar kana wasa da cikinka bazamu shiryaba, now just silenty stand up ka wuce dinning ka zauna nazo nabaka abinci, breakfast bakayiba kafita, jiya da daddare dudda uban hanyan dakashawo ga tuki all the way from Abuja lipton kawai kasha ka kwanta eh wani irin abune ina fama da little Fareeda taci abinci kaima ina fama dakai are you a baby" dan dariya yayi cikeda tsokana yace "to what I am before? Am your baby Mummy amman big baby ki" dariya Mummy tayi ta tallabemai keya tace "common tashi" tashi yayi ahankali yabita tana tafe tana mitan rashin cin abincin shi yana murmushi yace "Mum where is Princess?" kujera Mum tajamai yazauna akai tace "sunje saloon itada Rumana yin kitso" dan gyadakai yayi batare dayace komiba ba, lafiyayyen abinci ta zubamai jellof rice dayaji kaza sanan ta zauna kusada dashi ya turamai gabanshi kallon abincin kawai yake dan yasan bazai iya gamawa dashiba ko kadan amma yana tsoron magana Mum ta haushi da bala'i, spoon yajawo ya shiga ci ahankali kaman wani dan jariri.
*********************
_Bayan Sadakan Bakwai_
Yau kimanin kwana tara da rasuwan Rauda. Tun ranan da Rauda tarasu rabon da Ammi tasa Daddy a ido amma ko ajikinta dan ta tsani ganinshi daman, Alhamdulillah tsawan Kwanaki taran nan bata waniyi wahalan laulayi ba banda aman safe da kullum saitayi daganan kuma ko ciwon kai bataji, cikinta yafito sosai kaman cikin dayakai wata biyar, kullum saita kira Baffa yahadata da Aneesa su gaisa dudda daidai daso daya baitaba gayamata cewa ga wani abu dangane da Aneesan ba, kullum gayamata yake lafiyan ta kalau karta damu tacigaba da rayuwan gidan mijinta tana aikin lada domin aljanna ta na karkashin kafanshi ne, sunan zasu cigaba da kulamata da Aneesan.
Yau tunda ta tashi take da niyyan zata wanke kayan ta da sukayi datti dudda tanada yar aiki bazata taba bama yar aiki kayan ta ta wanke mataba, iyakan aikin yar aikin shine share tundaga dining har falo sai sharan gaban flat dinsu dakuma share kitchen da wanke wanke dudda uban laulayin datake daidai daso daya bata taba bari yar aikin taje sama ta gyara mata bedroom dinta ba da kanta takeyi hakama girki saidai randa batada karfin yi saita cema yar aikin tadafa mezataci da yamma saita tafi gidansu.
Hada duka kayan dazata wanke tayi a basket yawacinsu hijabai ne saikuma dogayen riguna datafi sakawa kwanan nan dansu sukafi mata dadin sawa, hijabi ta daura akan riga da zanin dake jikinta na atampa tabude kofar dakinta tafito ta sauko downstairs tana shakan kamshin hadadden turaren wutan da dakinta keyi wanda yar aiki ta kunna a burner ko ina yadau kamshi, kofar flat dinsu tabude tafito rikeda basket din tana zura slippers dinta ahankali.
Tunda tabude kofa Dady dake cikin mota da tundazu yadawo yakasa fita sai tunane tunane yake ya kafeta da ido yana kallonta, yarame sosai kana ganinshi kasan yanacikin damuwa bana wasaba, ga rasuwan Rauda, ga Aliyu na fushi dashi sosai, gakuma Rukayya da wani irin nauyinta da kunyan ta yakeji dako lokacin dayazo neman aurenta baijin yaji kunyanta da nauyinta hakaba, yagama wulakantar da yarta akan abinda ba ita ta aikata ba, baimasan tayaya zai fara bata hakuri da neman gafarar taba, shikadai yasan abubuwan dake damunshi arai, tunda tafito yake binta da kallo ya kafe cikinda dayadan fito ta hijabi da ido yanajin wani irin sonta da kewanta na ratsa kowani bangare dajijiya na jikinshi, ahankali yaga take tafiya da kafafunta dasuka sha Jan lallin gargajiya na salatef gwanin van sha'awa harta shiga laundry dinsu.
Matan Dady biyu tagani a laundry suna dan fira suna jiran kayan dasuka saka a washing machine din yagama wanke musu yasa taji kaman tajuya sabida ganinsu datayi saikuma tafasa ganin akwai washing machine har guda biyu dat are free, dan 4 manya manyan washing machines ne a gidan, ahankali takarasa ciki saida takai daidai wurinsu sanan tace "sannunku" wani irin banzan tsaki amaryan Dady taja ta kalli Amina matar Dady tabiyu tace "Amina ana magana fa" dan dariya Amina tayi tajuyo takalli Ammi daga sama zuwa kasa ta tabe baki sanan tajuya ta kalli Amarya tace "kinsandai ninafi karfinta wlh tayi kadan tasa akaini gidan yari kokuma tahadamin wani makircin saidai ke Amarya" wani irin dogon tsaki Amarya taja tace "wutsiyar rakumi tai nesa da kasa itama tasan nafi karfinta takowanni fanni, bana maulan abama y'ata aiki a bakery, bana tura yarana gantalin duniya ana zuwa ana lalle ana nemo kudi, gidan hutu na tashi ko anjiman nan nakira babana nacemai inason kaza zai aikomin dashi, tafitar da Kareema da makircin ta kullum sai uban saka hijabi kaman mumina ni tai bala'in kadan, tagama makircinta bata isa ta fitar dani daga gidan Alhaji ba tai kadan ne ina gayamiki, kuma kigayama yar agolanki ko an sakota daga gidan yari ta tafi gidan ubanta bazata zo tanacin kudin ubanda banata ba taje taci na ubanta mai gona, matsiyaci mai bar........" tass Ammi ta zuba mata wani irin mahaukacin mari kirjinta namata zafi ta nunata da yatsa tace "ki zageni dagayau har jibi ko tak bazan cemiki ba, wlh kika zagi marigayin mijina saina chanza miki hallita da duka, ki kama kanki" wani irin shafa inda Ammi ta mareta Amarya takeyi da sauri Amina tace "wlh bazaki yardaba saikin rama, duk abinda zai faru yafaru karki damu zan shigan miki, wlh saikin rama, ke tsaran wasanta ne dazata mara, haukace mata amarya" Amina tafadi cikeda zigi tana taba Amarya, cikin fushi Ammi tace "zoki rama mana" cikin zafin nama Amarya ta fizgi omon dake gaban washing machine din wajen kafin Ammi tace me Amarya ta watsama Ammi omon a fuska kadan yashiga idanun Ammi cikin ikon Allah hakan yasa ta shiga sosa ido, kallon Amina Amarya tayi, Amina tawani irin kashema Ammi idanu kafin atare suka sa hannu suka hankade Ammi ta bugu da bango Ammi tai yar karan azaba.