Sashe 49
In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Haddan nada dan nisa da gidansu babban makaranta ne wanda yaran manyan mutanen abujan nan keyi, ga security agaban gate din dake tsare su dan yaran senators da sauran sune kafin azo ayi kidnapping a premises din wajen parking Dady yayi parking yafito yabude musu suka fiffito kowa yay hanyar ajinshi itakuma Aneesa Dady yace ta tsaya, saida duk suka tafi Dady ya kulle motar ya kalli Aneesan yanda yaga tai zuru tana kallon makarantan dan tamafi wani makarantan boko kyau yace "muje karkiji tsoro ba'a duka saidai in baka bada hadda ba, so you have to be serious kinji ko kidage inkika haddace Al qur'ani duk abinda kikeso inhar inadashi saina miki aduniyan nan" murmushi tayi cikeda jin Dady tace "to Abbana zan dage" daidai nan suka karasa principal office din ganin Dady yasa daga malamai ustazai guda biyu da principal din wanda yake tsoho gashi fari balarabe dan balarabe ne mai karantan duk suka tashi suna gaggaisawa. "Alhaji kaine da kanka" cikeda fara'a dan yasaba dasu yace "eh y'ata nakawo" "bismillah ku" zama Dady yayi yanunama Aneesa kujeran kusada shi zama itama tayi Dady yace "akaramakallahu ga y'ata nan, daga islamiyya har hadda nakeso asata" gyadakai malami yayi yana kallon Aneesa kafin ya kalli Dady yace "shikenan ba matsala, zamu gwada ta sai musan ajin daza'a sata" faduwa gabanta ya shiga yi, ya dauko form da sauran abubuwa yace "acike wanan agida gobe kokuma Ince sati mai zuwa sai abata takawo" "to, to shikenan" Al qur'ani yadauko yabude chan suratun Ma'ida shafi nabiyu yace "bismillah, karanta mini nan naji" karba Aneesa tayi ahankali hannunta har rawa yake, kafadanta Dady yakama yana murmushi yasan she's nervous which is normal ahankali yace "relax karkiji tsoro gani anan, karanta musu muji" gyadama Dady kai tayi tanajin natsuwa, ahankali tai gyaran murya tafara karantawa bata sauke ba amma t iya hada baki hakan yasa zata iya karanta ko ina a Qur'ani, shiru Dady yayi yana sauraran muryanta dake da wani irin dadi saida tagama karanta shafin sanan malamin yace "barakallahu fiki, masha Allah ina ganin zamu sata aji hudu dan tanada matsala da tajweed, mataki na biyar kokuma nace aji na biyar su sun kware a tajweed" gyadamai kai Dady yayi cikin gamsuwa yace "to to shikenan ba matsala" daya daga cikin malamin ya kalla yace "akaita aji" gyadamai kai yayi Dady yace "tashi kibishi ajinki za'a kaiki" gyadama Dady kai tayi tabi malamin suka fita shikuma Dady yabiya kudin komi both hadda da islamiyya almost 150,000 sanan yabiya kudin littatafan ta both na hadda da islamiyya dazasu bata kusan dubu talatin sanan yamusu sallama yawuce yatafi dama sabida Aneesa ne yasa yau yakawo su da kanshi direban dake kaisu makaranta yaje yadauko su daban me a gidan.
_duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa_
_duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa_