← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 128

Sashe 79

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina take Mum ta iso ne? Yay maganan yana waige waige ko ina kozai ganta kafin ahankali yajuyo da kanshi ya kalli Ammin kaman yanda take kallonshi yace "Mum tadawo? Kodai Dad baisa asaketa bane? Bari naje nasame shi" yay maganan yana mikewa tsaye zaitafi yaji ankama hannunshi, ahankali yajuyo ya kalli Ammin, ganin yanda take kallonshi yasa ahankali ya tsugunna yace "Mum, menene Mum? Baisakota bako kibari naje nasame shi" girgiza mai kai Ammi tayi ahankali tace "yasaketa Aliyu, amman Aneesa da gidan nan har abada tagama zaman shi" wani irin faduwa gaban Aliyu yayi yace "wat! Mum! Ina kikasa taje? Mum bazan iya rayuwa babu Aneesa ba, am sorry Mum bangaya miki ba, I love Aneesa sosai, I want to marry her, please Mum kisata dawo gida I promise you zan wanke Aneesa agaban kowa I will prove her innocent" tunda ya ambaci kalman so Ammi ke kallonshi jitayi kaman ya sosa mata inda ke mata kaikayi ko kadan bataso ta tsaneshi but idan tacigaba da zama tana tuna abubuwan da mahaifinshi yamata zata gaggasamai maganganune hakan yasa tamike tsaye ahankali tareda daukan bowl din fruits dinta zata wuce da sauri Aliyu dayakeji kaman zai zare yace "Mum dan Allah ki tsaya, please just tell me ina kikasa Aneesan taje? Mum dan girman Allah kifadamin wlh Mum kaman zuciyata zata fashe dan Allah karki rabamu, I love Aneesa and she loves me too, Mum aure zamuyi, Mum inason Aneesa sosa......." "Aliyu!!!" Ammi tawani irin juyowa tareda kiran sunanshi ta hanyar dakamai tsawa, da yatsa ta nunashi tace "karna karajin, karna karajin ka furta kanason y'ata, karna sakejin kace y'ata na sonka, Aneesah bazata taba aurenka ba har abada, bazan taba bada y'ata ga yaron wanda ya kulle min itaba, Aneesah tama barmuku garin gabaki daya bazaku kara ganinta ba that I promise, sanan ka tashi kafita daga flat dinan kafin raina ya mugun baci, get out! " Ammi ta dakamai tsawa tareda mai pointing kofa, ja idanun Aliyu sukayi kallo daya zakamai saiya baka tausayi kaman kamishi kuka, baki yabude zaiyi magana Ammi tace "I said out Aliyu" juyawa ahankali Aliyu yayi saida yakai bakin kofa ya tsaya yajuyo ya kalleta yace "nasan kina fushi Mum, and you have the to be, no body wish yaga an kulle mai da agaidan yari bama police station ba, Mum kisani ko banyi danke ba nothing is going to stop me daga wanke abin sona Aneesa, I will prove to everyone that Aneesah na is very very innocent someone putted everything, saina wanke Aneesah, and flat dinki kike korana ko saina dinga zuwa Mum, saidai in kiyita korana kullum" yay maza ya share hawayen daya zubomai yajuya yafita.
Da sauri Ammi tajuya tai sama maganganun Aliyu sun tabata ba kadan ba, takusa kuka daurewa tayi ta zauna akan gadonta tana goge kwalla.
Duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, duk wacce ta fitar da book dinan waje Allah ya isa ban yafeba.

Tunda yay nisa a tafiya take bacci, har Baffa yakira sukai magana yacemai a express road zai tsaya ya jirasu dan gidansu na danaba ne duk batasani ba bacci take kaman wacce tai shekaru batai bacci ba, taji dadin AC sosai, sosai yake gudu ana kiran sallan magrib ya shigo kaduna-Abuja express road, wayarshi yaciro yay dialing number Baffa, ringing daya Baffa ya dauka yace "sannu Malam, sannu da kokari kun shigo express road dinne?" "eh Abba mun shigo" da sauri Baffa yace "to shikenan ka karaso ina tsaye bakin titin zaka ganni nasaka jallabiya mai ruwan goro da bakar hula, akwai carbi a hannuna dan daga masallaci nake" "to" ya katse wayan yacigaba da tukin yana kallon gefen titi, yay tafiyan kusan minti uku sanan yahango Baffa dattijon kirki yana tsaye bakin titi yanajan charbi yanabin kowacce mota daya wuce da kallo, horn ya danna mai hakan yasa Baffa yadaga hannu da sauri, yadan karyo kwana ya parking daidai baki bakin anguwan da Baffa ke tsaye ya kashe motan tareda fitowa, Baffa da sauri yamikamai hannu yace "sannu danan, Allah yasaka da alhairi" kasa karban hannun Baffa yayi saidai ya tsugunna yace "barka da warhaka Abba daftan mun sameku lpy" murmushi Baffa yayi yace "Alhamdulillah, tashi, tashi, Allah shi albarka" tashi tsaye yayi yace "bacci take tunda muka shiga hanya gatanan" yay maganan yana bude dayan door din Baffa biyeda shi abaya, Aneesa yagani babu ko dankwali akai gashin nan yarufe fuskanta yabar kadan, tana sanye dawata koriyar riga tagidan yari da koriyan dogon wando, sai kambas fari daya dawo brown shima duk na gidan yarin ta takure jikin kujera tana bacci wani irin tausayi data bama Baffa ko baisan lokacin daya tsugunna gaban motar ba, ahankali yakai hannunshi ya yaye gashin fuskar nata yadaura hannunshi kan fuskanta zafi rau yaji kaman wacce ke zazzabi, murya chan kasa yakira sunanta "Aneesah, Fateema, Fateema" ahankali take motsi da ido jin ana kiranta kafin tabude idanunta duka ta saukesu kan Dr zaid dake bayan Baffa tsaye ya rungume hannu a kirji yana kallonta. "Aneesah" kiranta dataji an sakeyi yasa tasauko da kanta kasa ta kalli gabanta, Baffan ta tagani a tsugunne yadaura hannu kan fuskarta kaman yau yafara ganinta yama kasa cewa komi, ahankali tace "Baffa" kallonta Baffa ya tsaya yi yakai almost 2min abubuwa da dama nakai komo a zuciyan shi kafin yamike tsaye yamika mata hannu yace "sauko mutafi gida wanda yakawo ki karmu tsareshi dare nayi" yunkurin tashi tafito tayi taji kanta kaman zai cire sabida ciwo, tashi tayi ahankali tana dafa kujera idanunta na jujuyawa cikeda karfin hali tafito daga motar, kafafunta ne suka fara rawa kafin tasa hannunta ana Baffa tai baya luuu zata zube da sauri Baffa yatareta yana salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesa" da sauri Dr yazo wurin yatsun shi biyu yadaura kan wuyanta yace "ta sume batada lafiya, Inane gidanku Abba" da sauri Baffa yace "kasan layin nanne kadan" "shigo mota da ita na sauke ku inada kayan aiki mukaje saina dubata" adan rude Baffa yace "kai likita ne?" gyadamai kai yayi Baffa ya shiga motar ahankali rike da ita yarufo musu kofan ya zagaya ya shiga yatada motan Baffa na nunamai harsuka karasa wani gida dakeda dogon dakali agaban gidan, sai wata yar Honda da tayoyin gabaki daya sukai less pake a kofar gidan, parking yayi yafito Baffa yafito rikeda ita yace "mushiga ciki likita" boot Dr Zaid yabude yaciro wani akwatin aiki sanan yabiyo bayan Baffa shiga gidan sukayi babban gidane sosai mai fili daga ta wuraren zauren kiwo ake awurin shanaye da awakai ne da aka garkame su dayawa, sai kuma tsakar gidan sai dakunan dakenan ajera guda shiga, sallama Baffa yadoka yana kwalama matarshi kira yabude wani daki dababu komi ciki saiyar katifa akan gado maidan kyau ahankali ya kwantar da Aneesah ya kalli Dr Zaid dake tsaye yace "zoka dubata likita" karasowa Dr yayi yana sanya stethoscope a kunne yazo yadubata sanan ya dago kai yace "abani ruwa Abba" da sauri Baffa yafita, ganin Baffa yafita yasa da sauri Dr Zaid yaje wurin kafarta wando nta yaja sama nan yahango wukake har guda biyu a jikin safanta kwashesu yayi duka yajefa cikin aljihun wando shi hakanan yaji bayaso susan tana yawo da wukake ko ahaka ma jibi yanda tsohom nan da mahaifiyar ta suka dawo ai zasu shiga damuwa sukaga abinda tazama, drip yadauko da allurai yay aciki sanan yamakala mata yana cikin makala mata Baffa ya shigo tareda matarshi datadan mayyanta rikeda ruwan tace "subhallahi Aneesa ce haka, Allah yabaki lpy" takaraso tace "ga ruwan likita salla nakeyi ne dazu dakika shigo" karban ruwan yayi bayan yagama samata drip din sanan yay dipping hand dinshi inside the water yaciro yakai kan fuskarta yana shafawa wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin ahankali tabude idanun dasuka kankance ta daura akanshi, wani irin faduwa gabanshi yayi da sauri yatashi tareda rufe akwatin shi yadauka tareda juyowa ya kalli Baffa yace "zan tafi Baffa jikin zai sauka dan nai allurai a ruwan danake karamata, inhar jikin bai saukaba ka kirani gobe da safe saika kawota asibitin danake aiki, amma yanzu abata abinci taci sanan tai wanka ta tsaftace ko ina harda wanan gashin nata zataji dadin jikinta" "baza'a yiba din m we ruwan ka dani eh?" cewan Aneesa data farka cikeda karfin hali, dukansu juyowa sukayi suna kallonta barinma Baffa daida gabanshi yay mummunan faduwa dayaji yanda tai magana, tashi tayi ta zauna cikeda karfin hali tana kallon drip din cikin fushi tace "kazo kacire abunan ko wlh na tashi saina fedeka" ahankali Zaid yajuyo yazuba mata idanu kallo daya yamata yagane dudda uban karfin halinta inta tashi tafiya biyuma sunmata yawa saita sake zubewa ta sume dan babu abinci acikinta, Baffa daya kasa magana yana kallonta Zaid ya kalla yace "abata abinci Abba da madara tasha, saida safen ku" wani irin yunkurin tashi Aneesa tayi da sauri inna tace "a'a mutuniyata ihakuri zauna bakiga bakida lafiya ba" ta kalli Baffa cikeda saiyasa tace "Mai gida aje asayomata madaran, likitan mu gode" "niban godeba wlh" Aneesa tafada tana ballamai harara juyowa yayi ya kalleta kafin yadauke kai tafice daga dakin yana mamakin masifan yarinyar.

5⃣5⃣
Chapter 79 · 0% Book details