Sashe 34
In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abakin asibitin ta sauka rike da katuwar jakan dake hanunta takarasa cikin asibitin da saurinta har dakin su, bude kofar tayi tana kallon manya manyan ledoji data gani kan kujera saikuma kwalin yogurt data gani da cup kan drawer ga Aneesan na bacci peacefully, karasawa ciki tayi bayan ta mayar da kofan tarufe ta ijiye abubuwan datazo dashi tana bude ledojin data gani manya manyan madara da milo ne sai kellogs cornflakes da manya manyan chocolates da biscuits harda minti mai tsinke da wasu abubuwan ma da batasan mesuba, maida ledojin tayi ta ijiye inda suke takai hannu tashafa fuskar Aneesan ahankali, bude ido Aneesan tayi ta daura kan fuskar Ammi da sauri tai yunkurin tashi taimaka mata Ammi tayi tana murmushi tace "oyoyo Aneesa, nadawo" ta rungume ta tana shafa bayanta kafin ta dagota ta jinginar da ita da bangon gado tace "meke miki ciwo yanzu?" murya chan kasa kaman na wacce ke mura ta nuna cikinta tace "cikina Ammi" dan murmushi Ammi tayi tace "sannu kinji hala yunwa ce, bari na kawo roba ki wanke baki na soyomiki kazanki kici , su Baffan kima na hanya zasuzo anjiman nan" Ammi tai maganan tana shiga bayi tadauko wani roba tabude jakan datazo dashi taciro brush da maclean da kanta ta wanke mata bakin tass sanan takoma bayi ta zubar da komi tareda wanko hannu tafito tana sake kallon kayan tazo gaban gadon ta zauna tana dauko kulan abincin da takawo tace "waye yakawo kayan nan Aneesa?" manyan ledojin Aneesa ta kalla kafin ta dauke kai tace "wani ne" shiru Ammi tayi bata kara cewa komiba dan atunanin ta mutumin jiyane yakawo, ta zuba shinkafa a plate tasa mata tsokan soyayyen kajin har guha uku tamika mata ta ijiye kulan akasa tareda daukan spoon takarbi plate din daga hanunta tasa chochalin tadebo abincin zatakai bakinta akai knocking kofar tareda shigowa. Dady ne ya shigo dakin yana sanye da manyan kaya shdda bugagga da hula sai kamshi yake Dr biye dashi murmushi yayi sosai cikin ba'a yana kallon Aneesan dake tanuna shinkafan ahankali yace "lallai y'ata tasami lafiya tunda gashi har baki yabude tanacin abinci" dan murmushi Ammi tayi tana gyara hijabin jikinta Allah yasa bata cireba tace "ina kwana Alhaji" kafin ma ya amsa ta kalli Aneesa dake cin abincin da Ammi tasamata abaki ahankali tace "bazakiyi gaisuwaba, Alhaji shiya taimaka mana jiya yakawoki asibiti" hadiye abincin Aneesa tayi ahankali tadago dara daran idanunta cikin dan karamin muryanta tace "ina kwana Abba" wani irin murmushi Dady yayi yanda Aneesan ta kirashi Abba saiyaji ta masifan burgeshi daga gani anbama yarinyar tarbiya mai kyau zuba yay har gaban gadon yace "lafiya lau y'ata ya jikin?" ahankali ta gyadamai kai. "lafiya lau Abba" murmushi Dady yasake yi yace "gud girl, babu abinda ke ciwo ko? Ko asakeyin allura ne?" da sauri ta girgiza kai tai kaman zatai kuka, dariya Dady yayi hakan yasa Ammi ma tadan murmusa koba komi maison naka abun kaji dadi ne, dariya Dady yayi ya kalli Dr daketa murmushi yace "tokanaji ko likita Ya'ta batason allura karka kuskura kamata" ya kalli Aneesa yace "idan Dr yamiki alluran zan dawo anjima kinfadamin kinji" da sauri ta gyadamai kai tana murmushi sai taji inama shi baban tane tanason Baba sosai tana bala'in son Baba, dan juyawa Dady yayi ya kalli Ammi da kanta ke kasa yace "cigaba da bama y'ata abinci ai baki koshi ba ko?" gyadamai kai tayi tana murmushi, Dady ya juyo ya kalli Ammi datamai kyau sosai dan tasaka wani maroon hijabi yace "kinji ko" dan dago kai Ammi tayi ta kallai hada ido sukayi da sauri tasauke nata tana kokarin debo rice din a spoon tace "angode Alhaji, Allah yasaka da alkairi, Allah yabiya bukatu yasa damu duka a gidan Aljanna" atare daga Dr har Dady sukace Ameen, Dady yasake kallon Aneesa daketa kallonshi tana murmushi yace "zan tafi anjima zan dawo nasake dubaki kinji, ki dinga jin maganan mahaifiyar ki kinji sanan kowani nagani aka baki kisha ki warke sabida kar mahaifiyar ki taitai shiga damuwa kinji" dago kai Ammi tayi ta kalleshi yanda yay maganan yatabata har zuciya, gyadamai kai Aneesa tayi ahankali tace "saika dawo, Allah yabada sa'a Abba" murmushi Dady yayi yanaji kaman yamaida yarinyar yarshi yace "Ameen nagode da Addu'an, muje Dr" Dr ya kalle Ammi yace "idan tagama ci ki danna alarm din gefen gadon nan zanzo" to Ammi ta amsa Dr yabi bayan Dady da sauri har wajen mota yarakashi Dady yamai kyauta mai tsoka sai godiya yake sanan ya shiga motan bodyguard yarufe yakoma gaba yatada motar suka bar asibitin, Dady sai tunani yake dan yaje shashin Aliyu bayanan ina yaje this early morning? Sai kirashi yake baya shiga.
_duk shegiyar data fitar min da littafi waje Allah ya isa, duk kuma wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, ban kuma yafeba_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
2️⃣6️⃣
Wuraren biyar na yamma wayar Ammi tai ringing ganin Baffa ne yasa tai picking da sauri tace "to bari nafito" katse wayan tayi ta kalli Aneesa dake bacci ana mata karin ruwa ta zura talkamta tana gyara hijabi tawuce tafita, a reception din asibitin tagansu Baffan Aneesa dakuma dayan Baffan kawu Sani tsaye suna kalle kalle, suna hango ta suka taho itama tana tahowa tsayawa duk sukayi bayan sun iso tace "sannunku da zuwa, kunsha hanya, muje" tai gaba suna biyeda ita har dakin da aka kwantar da Aneesan shiga duk sukayi Baffa da sauri yakarasa gaban gadon yana kallon Aneesan gidansu su uku maman su ta haifa shine Babba sai mahaifin Aneesa dasuke kira da mai Kwato saikuma Sani autan su dasuke cema Na Sani, dasuka taso mahaifin Aneesa shi Allah yafima arziki danshi harkan gona yake yana noma sosai yanada gonaki sunfi goma sha biyu, idan yay aikin gona ya sayar da amfanin gona saiya saro shanaye yana bashi yana tayashi kiwo duk yaran da matayen shanun zasu haifa na shine yace yabashi haka suke rayuwan su suna rufama juna asiri haryazo ya auro Ammi, Ammi batada iyaye sun rasu tun tana yarinya a hannun kakan ta ta taso, bayan wata uku da bikin ta kakanta tarasu itama, shekara daya da aurensu Ammi ta haifi yarta mace kyakkyawan gaske dayasa mata suna Fateema sunan maman mahaifiyar kakansu kenan, sai ana cemata Aneesa, Aneesa nada shekara biyu aduniya wata rana yaje gona maciji ya sareshi shinefa yadinga ciwo dudda an zuke dafin macijin sai ciwon yadawo babban gaske akace yanada ciwon sugar ne saisa yaki warkewa, haka ciwon nan yadinga cin kudi yadinga cin kudi, saida aka saida gonakin shi kakap aana maganin turenchi ayi na hausa amma ba'a ganin chanji duk ba'a daceba kafin Allah yazo ya amshi ran abinshi, bayan yarasu babu yanda basuyi da Ammi ba sutafi da ita kaduna chan family house amma Ammi tace ita bazata bisu kaduna ba, basu takura mataba suka barta a gidan har Aneesa tai shekara biyar Baffa yazo zai karbe ta dan kyan ya mace ta tashi akulan mahaifi amma Ammi tace bazata bayar ba, babu yanda basuyi da ita ba taki basu ko ranan nan maganan dayazo mata kenan zai tafi da Aneesa amma taki yarda harda kukan ta wai mesa sukeson rabata da yarta.
Addu'a yagama tofama Aneesan dake bacci ya juyo ya kalli Ammi yace "ai yanzu hankalin ki ya kwanta ko Maman Fateema? Yarinya babu wuyan duniya dabaki bata, yau tana kasuwa, gobe tana gidan chan yin lalle, wanchan garin yin lalle, ketai aiki takawo miki kudi, kaganta tana shagon chan tana shagon nan, babu kalan Iskan duniyan nan da yarinyar nan bata shaka, ba baki barin yarinya tahuta ya za'ayi bazatai rashin lafiya be eh? An gayamiki ita injin ce?" da sauri Kawu Sani yace "ya isa Yaya yanzu ba lokacin fada bane muna asibiti" cikin fushi Baffa yace "sai anyi fadan, ka barni nafada mata gaskiya tazaci tsoronta akeji, ni uban yarinyar nanne" ya nuna Aneesa dake kwance kan gado yace "ni mahaifin tane, duk duniyan nan a yanzu babu wanda keda iko da ita kaman ni, koko idan aka barki da ita zaki iya aurar da ita ne iyye?" ya tambayi Ammi cikin fushi, yace "tabani yarinya natafi da ita kaduna ta shiga cikin yan uwanta su Rukkaya, da Asiya, da Maimunatu amma taki koko ance miki idan natafi da Aneesan cutar da ita zan dinga yi ne kokina ganin zan zauna nabude ido ina gani ana cutar da Aneesa agida nai shiru ne? Ballema nasan inhar ina raye babu wanda ya isa ya cutar da ita" dan shiru yayi yana kallon Ammi data saukar da kanta kasa yace "wlh kawai banson na tauye miki hakki ne, amma inhar baki shirya kula da yarinyar nan da hannu bibbiyu ba karbanta zanyi kome zai faru yafaru kina jina" dan murmushi Ammi tayi aranta tace "maza kenan su kullum gani suke baka kula da yara da kyau" kujera Baffan yaja yazauna shikuma Kawu Sani yazauna abakin gadon, dago kai Ammi tayi ta kallesu dan murmushi tayi koba komi Baffa tsoho ne kuma yayan baban yarta ce dole tabashi hakkin shi tasan ya isa da ita bawai bai isa bane kawai bataso ya karbe mata abu daya datake gani taji dadi ne aduniya, ahankali tace "kayakuri Baffa, kuyakuri dan Allah, zan kara kiyayewa" shiru yayi baice mata komiba ahankali tace "akwai abinci Baffa nazuba muku" girgiza kai yayi tareda saukar da ajiyan zuciya yace "kibari muyi magriba tukunna, inane ofishin likitan muje maganshi musan nawa zamu biya?" "kana fita ka mike gun zakaga ofishin" kallon sani Baffa yayi yace "kaimuje sabida kome aka rubuta ka karantomin naji" tashi yayi suka wuce suka fita koda sukaje wajen likita cemusu yayi wanda yakawo su jiya asibitin yabiya kudin komi addu'a suka dingamai su Baffa, Dr yace karma suji komi anjima zaizo zasu ganshi saisumai godiya atare duk suka wuce masallaci danyin sallan magriba.