← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 128

Sashe 26

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

2️⃣0️⃣ & 2️⃣1️⃣

Sosai tunanin Aneesa ya addabi zuciyar shi, ahankali yabude ido ya kalli yogurt din dake hanunshi ahankali yace "she's a Nubian princess" knocking kofar da akayi tareda shigowa yasa yadaga kai ya kalli kofa, Rauda ce ta shigo tanamai murmushi, rabonshi da ita tun ranan daya kwatota daga hannun Khamis, tsareta da ido yayi ganin ta ramemai duktai wani iri, shiru yayi baice mata komiba dan haushinta yakeji danta mai karya ranan, karasawa cikin dakin tayi ta zauna gefenshi ahankali tana wasa da yatsunta ahankali tace "good afternoon Ya Aliyu" gyadamata kai yayi batare dayace komiba ya cigaba da kurban yogurt yana kallon TV, shiru tayi tana wasa da yatsunta saikuma takara dago kai ta kallai ganin yaki kallonta yasa duk taji wani iri, ahankali tadaura hanunta kan nashi takama hannun shi tarike, dago kai yayi ya kalleta, lankwashe kai tayi murya chan kasa tace "am sorry Ya Aliyu bazan karama karyaba wlh, kunyan fadama da Khamis zamu fita nake saisa ban fadama gaskiya ba, am sorry kaji please" ganin yanda duktai wani iri tana shirin mai kuka yasa ya gyadamata kai dan ko kadan baijin surutu yau baijin dadin kanshi shima, bedroom dinshi yanuna mata yace "daukomin wayana" tashi tayi da gudunta tai bedroom dinshi, bata wani jimaba tafito rikeda wayanshi karban wayan yayi yaduba yaga ba miss calls ba message, baida any notification, dan lumshe ido yayi zuciyarshi namai badadi ya ijiye wayan ahankali kan kirjinshi, Rauda dake kallon fuskanshi ne tace "menene Ya Aliyu? Are you expecting something ne awayan?" batare daya bude ido ba murya chan kasa yace "nevermind" ji yayi ma yogurt din ya isheshi hakan yasa yamikama Rauda kofin, karba tayi tawuce kitchen tana shan ragowan daya rage, ta ijiye ta fito tadawo kusada shi ta zauna, yanda taga duk yay wani iri yasa takama hanunshi tace "Ya Aliyu wai menene? Bakada lafiya ne? Kai wani iri sosai wlh yau, are you okay Ya Aliyu kona kira Dr?" girgiza mata kai yayi yana mikewa tsaye yace "go and pray ana kiran salla" daya daga cikin sweet din dake cikin wani flower bowl dake kan center table dinshi ne tadauka tana folding legs dinta akan kujeran shi tace "ni am off salat" yatsine fuska yayi ya dungure mata kai batare dayace komiba, dariya tayi tana jefa sweet din abaki ya harareta yawuce ya shiga bayin falo ya dauro alwala yafito yabude kofa yawuce mosque yana tafiya ahankali.

Karfe biyar daidai ta tattara komi tawuce backyard ta wanke kafa da hannayenta tadawo ta zare riga da hijabin tadau dogon hijabin ta tasaka tadau jakanta ta rataya tafito, ko kallon inda su Fatima suke batayiba tawuce bude mata kofa da sauri Yusuf yayi tafito yana binta da kallo yana murmushi kaman wani wawa yace "sai gobe Fatima" ko kallonshi batayiba tawuce ta shiga keke napep har zuwa anguwan su, yau gabaki daya ranta ajagule yake tarasa meke mata dadi sauka tayi daga kan keken tana dafa kanta dataji yafara mata ciwo taciro kudi tabashi batare datai magana ba tajuya ta shiga gidansu da sallama, a kitchen ta hango Ammi na tuka tuwo bamata ji sallaman taba sai aiki take abinta, jingina tayi da bango tana kallon Ammin, tana mugun son Ammin ta bana wasaba, she just wish tasan baban ta, dudda bata sanshi ba tasan Ammi was just the best wife he could have ever had, tanada kirki, gashi ta iya girki, ta iya kula da lura da yara, Ammi is everthing to her, she just wish zata sami second Dad dat will take care of her Ammi, ajiye jakanta tayi ahankali abakin kofa ta cire hijabin ta ta wurga afalo, sadaf sadaf ta shiga yin tafiya, ko kadan bataji shigowan Aneesa kitchen dinba dan hankalin ta yay nisa kawai jitayi an rungumeta tabaya. "oyoyo Ammi na" ajiyan zuciya Ammi tasauke tana murmushi cikeda so tana shafa hannayen Aneesan datai wrapping around her chest, ahankali tace "harkin dawo Aneesa, banmaji shigowan kiba" dago kanta tayi tana leka fuskar Ammi tace "yanzu nadawo Ammi, tashi nakarasa tuka tuwon inya salala na kwashe" girgiza kai Ammi tayi tana dauko mara daga cikin ruwan dake gefenta tace "a'a kibarshi keda kika daga wurin aiki kin gaji, ga ruwanki nan dauka kije kiyi wanka ki sa kaya marasa nauyi, jeki cire kayan kizo kijuye ruwan" gyadama Ammi kai tayi tajuya ahankali tawuce tsayawa tayi tadau jakanta dake bakin kofa sanan ta shiga daki, dakinta tawuce ta shiga, zama tayi akan gado tai shiru ko kadan batajin dadin komi gatanan ne kawai, jakanta tabude taciro wayarta tsayawa tayi tana kallon wayan kafin ahankali ta danna side button din wayan ya kunnu, tsayawa kallon wayan tayi tarasa mesa hakanan saitaji wani iri dataga batada miss call kodaya, kwanciya tayi akan gado ta ajiye wayan tareda lumshe ido wani bacci mai shegen dadi ne yay awon gaba da ita.
Chapter 26 · 0% Book details