← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 128

Sashe 91

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

In kika karanta baki biyaba Allah ya isa.
Tafi minti goma sha uku a tsaye tana tunanin kalaman da Hafiz yafadi mata, ita Hafiz keso? Dama abinda yasa kullum yake zuwa gidansu kenan? Tadade tana tunane tunane kafin tafice kitchen, ahankali ta shiga kitchen din ta tsugunna kusa da Inna dake gindin murhu tana tukin tuwo tace "kawo in tuka tuwon Inna" dan waigowa Inna tayi ta kalleta ganin yanda muryanta yay sanyi tace "nariga nagama kya kwashe, naga Likita yafita cikeda bacin rai meya hadaku? Kindai san samari na wuyako kwanan nan, kin sami yaro mai hankali ga aikin hannu mai abinyi, gashi yanason yan uwanki ya daukemu kaman iyayenshi kinamai wulakanci karki baridai ya subuce miki kinajina ko" tunda Inna ke maganan take kallonta towai waya fadamusu soyayya suke daman, dan juyowa Inna tayi ta kalleta jin tai shiru tana ciro muciyan daga tukunya tace "kinmin shiru bakiji minace bane?" girgixa kai Aneesah tayi ahankali tace "ba soyayya mukeba Inna, kawai yayana ne" dawata irin dariya inna ta kwashe tace "hohoho su Aneesah an girma nikikema karya, mutumin daya shigo dakin Baffan ki yace yanason Baffa yamai izinin yafara neman nakine saisama kike ganinshi yana shigowa gidan nan kai tsaye danmu mukamai izini mun yarda da tarbiyanshi shine kikemini karyan kunya sannu kinji zulliya" Inna tafashe da dariya tamike tsaye tasa hannu ta dungure kan Aneesan datai shiru tace "tashi nidai ki kwashe min tuwon bari naje na kwaso daddawan da Mubarak yadakamini a turmi nazo na hada miya" fita Inna tayi tabar Aneesah cikeda mamaki da yakasa boyuwa daga fuskanshi.

Kika fitarmin da littafi ban yafemiki ba.
Washe gari misalin karfe shabiyu Baffa da Kawu Nasani da tuntuni suna gida basu fita ko inaba sukai baki wasu manyan mutane ne maza sunci kayan alfarma, falon Baffa aka shiga dasu sanan taji anata zancen dudda batajin me suke cewa but tanajin hayaniyan su sama sama, saida ana kiran sallan azahar ne suka fiffito tareda su Baffa aka tafi, itadai tana daki jinta take wani iri kawai takasa mance maganganun Hafiz.

Kika karanta min littafi batare dakin biyaba ban yafemiki ba, littafin nan nakudi ne pay 300 access fee.
Sallame sallan isha'i da akayi yasa Baffa yamike da sauri yafito wajen masallaci tun araka'an shi na farko ake kiranshi yarasa wake kiranshi haka, ciro wayan yayi daga aljihu ganin Alhaji Ibrahim Muhammad ne yasa wani irin mamaki ya kamashi harsaida yace "Alhaji!" wayar ya tsaya yake kallo ganin kiran na neman katsewa yasa yace bari yadauka yaji kuma dawacce yazo kara wayan yayi a kunne. "Assalamu Alaykum" Dady yamai sallama anatse, Baffa baikawo komiba ya amsa kaman wani abu baitaba hadasu ba. "waallaikumu sallam Alhaji yau agarin, ya aiki? Ya yara yakuma Iyali da fatan kowa lafiya?" shiru Dady yayi yana wani irin jin nauyin Baffa sabida rashin mutuncin daya musu tayaya ma zai fara ga yamai abinda yake tafe dashi? Baitaba abinda yakejin danasani dakuma kunyan kanshi ba kaman wanan kuskuren dayayi akan Aneesa, he is so ashamed of himself, jin shiru Baffa yace "naji shiru Ince dai lafiya ko?" ajiyan zuciya ya sauke dahar Baffa saida yaji sanan yace "Alhaji nasan hausawa nacewa rama mugunta ga mugu ibada ne, amma nasan muminai masu zukata mai kyau bakwa amfani da wanan karin maganan al'adan mu na hausawa, Alhaji ni mai laifi ne ninasan da hakan, amma ban isa na chanza abinda Allah ya tsara cewa zai faru ba, Alhaji ayau nazoma da gingima gingiman zancen guda Biyu dan Rukayya taki kallona kokuma saurarena, Alhaji kiyafemin laifin dana aikata akan Aneesa, na tafka shirme da shirin mata yasa nai hakan, ka yafemin, ka yafemin dan girman Allah, wlh nai nadama, nai nadama matuka ban kyauta ma amanan Aneesah daka damkamini a hannu ba na kuma karbeta a matsayin mahaifi ba, Alhaji kiyahakuri dan girman ubangiji" da sauri Baffa yace "haba Alhaji kadena rokona bakamin komiba tuntuni na yafema, Allah kuma ya yafemana gabaki daya, amma komi yawuce babu wanda ya isa ya ketare jarabawan Allah, so komi yawuce wlh" ajiyan zuciya Dady ya sauke yace "sai magana ta tabiyu, Alhaji Aliyu baida lafiya sosai wlh yau kwanan shi hudu a asibiti kenan yana fama da mugun ciwon kirji, Alhaji Dr yace zuciyanshi yadan kumbura wlh" Dady yakarasa maganan kaman zai saki kuka dayasa Baffa yaji yamugun tausayamai yace "ubangiji Allah yabashi lpy, karkadamu kaitamai addu'a, ammadai wanan batu baimin dadi ba, ciwon yaro babu dadi ko kadan" cikin wani irin yanayi Dady yace "Alhaji alfarma nazo nema wajenka, Aliyu na matukar kaunar Aneesah batun yauba, nasan nai kuskure shima bada sanin shi nai hakanba da bazai barni ba lokacin baya cikin hayyacinshi, Alhaji ku taimaka mini badanni ba bakuma dan halina ba sai dan Allah kubama d'ana auran yarku, karna rasa Aliyu dan girman Allah, Alhaji nina muku laifi please karkuyi punishing d'ana for the mistake of his Dady dan kaunar ubangiji ku dubeni da fuskan tausayi badanni ba dan girman Allah" yanda muryan Dady yasauya kaman wanda ke shirin kuka yasa Baffa yagane lallai lallai kam Dady na cikin masifaffen tashi hankali amma kuma a yanzu ahaka babu abinda zai iya mishi. Dan ajiyan zuciya yasauke yace "Alhaji mu manya ne, ba'asan manya da magana biyu ba ko kwana kwana kokuma yin karya ba, karkuma kazaci abinda zan fadamaka kodan ban hakura bane kokuma wani abun uhm uhm wlh ko daya, ciwo yawuce komi, Alhaji bazanma karyaba a yanzu haka kudin auren Aneesa ma akanwo shi, yau dinan akai komi nasaka mata rana wata daya da sati daya sabida mijin likita ne zaije PhD a Cuba 🇨🇺 anaso dazaran anyi aure saisu tafi Cuban tare, kayakuri amma a gaskiya babu abinda zan iyamaka da kaman kazo dawuri ne, ina maka fatan alkhairi sanan Allah yatashi kafadan Aliyu yasa kaffara ne, Allah kuma yabashi lafiya yabashi wata matar tagari, nabarka lafiya agaida mai jiki saida safe" Baffa ya katse kiran.

6️⃣5️⃣
Chapter 91 · 0% Book details