← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 128

Sashe 98

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bala'in gudu Aliyu yake yana kalle kalle har idanunshi suka sauka akan shagon da ake saida hijabi tsayawa yayi yafito yana tafiya ahankali yacema mutumin shagon "Malam hijabi nakeso kaman wanda zaima mai tsawona har kasa yanajan kasa" kallonshi mai shagon yayi yace "okay yadi shidda da kusan rabi kenan" zama Aliyu yayi kan kujeran ahankali yace "OK ayanka adinkamin yi sauri, kuna saida nikabi ne?" "eh muna saidawa yallabai" gyadakai Aliyu yayi ya daga agogon hannunshi na rolex yana kallo about 1 :15 yanzu, ganin yanda yayyafin da akeyi ke zuba kanshi yasa mai shagon yace "ka shigo ciki Alhaji kar ruwa ya jikaka" dan shigowa ciki Aliyu yayi yana kallonshi, cikin minti baifi gomaba yagama dinka hijabin sanan yace "a dauko nikabin ne yallabai" gyadamai kai Aliyu yayi yadauko yace "kudinka ya tashi biyu da dari takwas" zaro kudin dabaimasan yawansu ba yayi yamikamai yajuyo yashiga mota da gudu haryakai wajen daidai gidan man danaban kafinma ya shiga unguwan ya hango motoci shiga yayi yayi parking daga baya baya, tareda kashe motar, ajiyan zuciya ya sauke ya kalli hijabi da nikabin da aka dinkamai, ahankali yajawo hijabin ya warware yasaka daga zaunen, sanan yadauko nikabin yana gyara madubin gaban motan ya daurashi tsaf, farin glass din mai karamin lens daya daukone yasaka a idanun sanan yabude motan yafito yana numfashi sama sama dan baisababa jiyayi kaman nikabin ya shakemai wuya, kallon kanshi yayi ta jikin glass din motar yanda hijabin ya saukanmai danko takalmin shi ba'a hangowa yay kato cikin sanan yay kato ciki, kulle motar yayi yafara tafiya ahankali kaman mace yana shiga anguwan sosai ruwa na sauka akanshi yana kallon tulin mazan dake cikin wata runfa an tsaitsaya ana magana za'aja daurin auren zuwa karfe uku sabida ruwan da akeyi ga Baffan ta na zuwa dan sun fita dole ajirasu, wasu yan mata dayagani sunci gayu suna sanye da anko sun fito daga wani gida ya tare tareda lankwasar da muryan shi kaman wata mace yace "yan mata dan Allah wani gida amarya take zanganta ne is urgent" daya daga cikin yan matan ne tanunamai gidan dasuka fito daga ciki tace "nanne tana dakin su salamatu" baima tsaya musu godiya ba yashiga gidan da sauri gabanshi nawani irin faduwa ya kalli yan matan da sukacici gayu ana kwalliya, falon dayagani abude ga takalmomin yan mata yafada, yan mata ya gaggani zaune wasu nacin abinci wasu na rawa dan sun kunna wakan Zee baby a speaker falon yacika da hayaniya, wajen wata dayaga tanata kallonshi yayi tunda ya shigo da sauri yace "dan Allah ina Aneesah Ammi ta aikoni wajenta" murmushi tayi tace tana dakin su salamatu kaya ake chanza mata" da sauri yace "inane dakin?" Corridor ta nunamai hakan yasa yay corridor da sauri gabanshi nafaduwa har wani lumshe ido yake his eyes are eager to see her, kofar dakin dayagani abude surutu natasowa daga ciki yayi ahankali yakarasa bakin kofan tsayawa yayi chak yana kallon Aneesah dataci gayu sosai an mata hadadden makeup tasaka hadaddiyar doguwan riga na maroon and golds an mata daurin gwaggwaro daya mugun yimata kyau gashin gaban goshinta sun wani irin kwanta, tayi kyau kaman wata Celebrity, kayan jikinta sun mata kyau sunbi jikinta sosai, wata yarinya da ita kadai ke dakin tana daura mata agogo ahannunta dayasha wani hadadden lallen amare, chak numfashin shi ya tsaya kafin ahankali yadawo yawani irin sauke ajiyan zuciya, wani irin sanyi Aneesah taji ajikinta dayasa tadago kanta da sauri danji tayi kaman anbude fridge idanunta ne suka sauka akan wata katuwar doguwan matan dake tsaye abakin kofar dakin dasuke tana sanye da hijabi dakuma nikabi tasaka wani farin glass tana kallonsu, dan taba Salamatu dake samata agogo tayi hakan yasa salamatu ta dago kanta da sauri tace "menene Aneesah?" ganin inda Aneesah ke kallo yasa tawaiga ganin mata danikabi ta tsaya chak tana kallonsu itaba tai magana ba yasa tace "Anty lafiya wakike nema? Mama na gidan biki mune kawayen Amarya kawai ke fati a gidan nan" dago kafa ahankali Aliyu yayi yana wani irin kallon Aneesah data cigaba da gyara sarkan wuyanta tana kallon madubi tana murmushi da kanta dan ita kanta tama kanta kyau, lankwashe murya yayi da kyau gudun kar Aneesah ta dago ta yace "Ammi ta aikoni wajen Aneesah" da sauri Aneesa tadagokai ta kalleshi jin ya kira Ammi tace "Ammi na" gyadamata kai yayi yace "eh tace na kawo mata Ke yanzun nan komin hayaniyan dakuke na tabbatar nazo dake, Baffan ki dawani bakonshi da Ammi ki keson ganinki su uku, dauko hijabi kisa muje, ni muna girki ne ankusan daurawa" da sauri Aneesah ta kalli salamatu tace "ina hijabina salamatu?" hijabinta salamatu tabude wani jaka taciro tabata karba Aneesah tayi tasa hannu ta zare gwargwaron kanta dogon gashinta da aka daure dawani hadadden ribbon dayasha gyara ya sauko saida numfashin Aliyu yakusan daukewa ta zura hijabin tareda mikewa ta kalli salamatu tace "muje ki rakani" hararanta salamatu tayi tace "Inna biki wazaiji da bakin? Nidai kiyi sauri" juyawa Aliyu yayi yana tafiya ahankali Aneesah na biyeda shi suna fitowa falo akadau guda ana Amarya ina zaki, dariya Salamatu tayi tace "to iyayen gulma Ammi ke kiranta" suka fice lokacin ruwa yaragu saidai yayyafin da ake, sanin waje da maza yasa taja hijabinta gaba sosai suka fito tana biye dashi, ganin sunyi hanyar wajen layi yasa da sauri Aneesah ta cinmata tace "Ammi bata gidane?" gyadamata kai yayi yana make murya yace "gida da mutane suna gidanmu, chan layin dake kallon layin mu, motama sukasaka na dauko danna kawoki dawuri tace tundazu take kiranki dan salamatu tarakoki kizo baki dauka" da sauri tace "ayyah wayata na purse din salamatun ne saisa" ahankali suke tafiya haryakai wajen motarshi sai kallon hadaddiyar motan take yabude motar yace "yi sauri kinga wayana ma na vibration nasan ita ke kira" ko tunani Aneesah batayiba ta shige ya maida kofan ya rufe yazagaya da sauri ya shiga wajen direba ya zauna yay locking motar gabaki daya, sanan yatada motar batare daya ciro hannunshi daga hijabi ba yaja motar da mahaukacin gudu dahar saida Aneesah ta firgita gabanta nafaduwa sosai sai kallonshi take.

6⃣9⃣ & 7⃣0⃣
Chapter 98 · 0% Book details