← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 128

Sashe 29

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wani babban private asibiti Dady yasa aka kaisu anan cikin Abuja dan Suleja babu wani asibitin kirki, suna parking kafin kaceme ma'aikatan sun gunguro gado suka cirota daga mota akai ciki da ita da sauri Ammi har zuwa gaban dakin daza'a shiga da ita aka shiga da ita zata bisu ciki a rude Dr yace "sorry Ma, don't worry your daughter will be fine" ya kalli wata nurse yace "give madam water and sit let her calm down" yawuce ya shiga ciki tareda rufo kofa, tsayawa Ammi tayi jikin kofan tana lekawa duk jikinta na rawa ganin ana janyo oxygen ana makalama Aneesan yasa ta daura hanunta abaki tarufe bakinta kuka na zuwan mata hawaye ya shiga fitowa, memory ranan da baban Aneesa ya rasu yadawo mata fresh dan shima haka aka makalamai oxygen dan he was finding it difficult to breath, hanunta tadaura akan glass din kofar arude tace "no Aneesa don't leave me kinji dan Allah, babanki yabarni please karki barni Kinji Fateema please" Ammi tai wani irin breaking down da kuka, Dady da tuntuni yake tsaye agaban receptionist yana son yamusu clearing bills dan yasan basuda wani karfi sosai ya tsaya chak yana kallon Ammi data bala'in burgeshi he so much sees kanshi in her, yadade rabonshi dayaga mahaifiya dake nunama yaranta so haka karara, jibi dai matan shi har uku, barin ma Kareema jitake kaman ta kashe Rauda kaman ba ita tahaife taba, shi wani irin mutum ne dayake bala'in so yaga mata na nunama yaransu so karara agaban kowa, saisa yakasa mantawa da Maman Aliyu yar baturiyan shi, yanda Ammi ke magana yasa yaji ta masifar burgeshi sanan ta bala'in bashi tausayi. Wani paper receptionist din ke mikomai ya daga mata hannu yace "wait am coming" ahankali yataka yakarasa har inda Ammi ke tsaye tana kuka, kallon dakin yayi yaga yanda aka sama Aneesan oxygen ana bata taimakon gaggawa, ahankali yace "karki damu Allah zai tashi kafadar Aneesa bazata mutu ba, kidena kira mata mutuwa kimata addu'a ne banji kinmata addu'a ba tun dazu" da sauri Ammi tadago jajayen idanunta ta kalli Dady kaman wacce batasan metake cewaba tace "addu'a?" gyadamata kai Dady yayi yace "kinga zomuje chan ga kujeru nan kizauna akawo miki ruwa kisha ki kwantar da hankalin ki kimata addu'a, kin zaci idan ta farka yanzu taganki ahaka idanunki sunyi jajir zataji dadi ne?" da sauri Ammi ta girgiza mai kai hakan yasa yadanyi murmushi aranshi yace kibace kawai amma batada wasu shekarun kirki, ahankali yace "muje kizauna" yay gaba, ahankali ta daga kafa tabishi abaya kujeran daya nuna mata ta zauna daidai lokacin Nurse ta fito da ruwa mai sanyi na gora takawo mata karba Dady yayi yana budewa yace "yauwa kingani ga ruwan to kisha" yamika mata Goran karba tayi tadan kurbi kadan tareda sauke ajiyan zuciya tana sake goge fuskarta da bayan hannu ganin haka yasa Dady yakoma wurin receptionist din sabida ba'a riga an gama mata treatment ba yasa basusan nawa zasu chajeshi ba, dubu dari yasa bodyguard yadauko daga mota ya ijiye musu yace abasu kome suke bukata zai dawo gobe da safe sanan yajuya zai koma wajen Ammi daidai lokacin Dr yabude dakin da Aneesan ke ciki ya fito da sauri Dady yay wurin Dr ya mikamai hannu, murmushi Dr yayi yadan duka yace "sir kaine da kanka, please let's go to my office anbarka a tsaye" girgiza kai Dady yayi yace "noo don't worry am actually about to leave ma, ya jikin Y'ata? How's her condition now?" daidai lokacin Ammi ta iso wajen kalman Y'ata da Dady yafadi yasa taji her heart was heavy, ahankali tadan kalli fuskar Dady dabaima lura da zuwanta ba yana kallon Dr, anatse Dr yace "for now we've manage to stabilize her condition, andau sample of her blood we will run some test dan munsan meya jawo mata ciwo haka" gyadakai Dady yayi yace "alright thank you Dr, please ka kula da ita sosai kome kuke bukata just let me know, am coming in the morning to check up on them, need to hurry up nima d'ana bai waniji dadi ba yasami bruises a hanunshi".

Da sauri Dr yace "hope is not serious" girgixa kai Dady yayi yace "ahhh nothing much, anyway can she see her ko hankalin mahaifiyarta ya kwanta?" Dady yay maganan yana juyawa dan yakira Ammi tazo taga Aneesa, hada ido sukayi da Ammi dake tsaye abayanshi tana wani irin kallonshi, dan murmushi Dady yayi yace "karki kara kuka Aneesa ma kaman ta warke kinajina, yanzu muje ki ganta, ai Dr she can see her ko?" dan dariya Dr yayi yace "yes sir" murmushi Dady yayi yace "muje to" har gaban kofan yaje yabude mata kofa yana kallon Aneesan dake bacci yace "karki tadata she needs this sleep nizan tafi gida" zama tayi ahankali kan kujera ta kalli Dady tace "Allah ya saka maka da alkhairi, Allah kuma ya taimakeki adukkan Al amuranka, Allah yabiya maka bukatun ka na alkhairi, nagode sosai Alhaji" washe baki Dady yayi ya bala'in jin dadin addu"o"in ta, shidai arayuwan shi yana bala'in son appreciative woman wacce bakamata wani abun kirki ba amma inta fara maka godiya saikajika on top of the world, wani sassanyar murmushi yasaki tareda dan dauke kai dan bajson yanda yake kallonta karyasa tai feeling insecure yace "don't mention, Allah kara sauki, saida safen mu" gyadamai kai Ammi tayi yarufo kofan yawuce yafita daga asibitin bodyguard suka Budemai mota ya shiga suka tafi.
Suna parking Dady baima tsaya jiran bodyguard su budemai kofaba yafito yay hanyar dakin Aliyu dan gabaki dayan tunanin shi nakan dan yaron shi rabonshi dashi tun dazu daya barshi yay bacci, ahankali yabude kofan sitting room din akan dogon kujera ya ganshi zaune da dan singlet fari sai wani 3quater ya rungume filo yana kallon sama, da sauri Dady yamaida kofan yarufe yakaraso ciki zama yayi gefenshi ya karbi filon ya ijiye yatada shi zaune tareda cupping face dinshi yace "Gadanga na are you okay? Naga kai shiru menene" girgiza ma Dady kai yayi murya chan kasa yace "am feeling somehow Dad, bansan meke damuna ba, sanyi nakeji" da sauri Dady yace "sanyi kakeji shine kaki saka kayan kirki" shiru yayi yana kallon Dady, bin jikin shi Dady yayi da kallo kafin ya kalli kan center table din gabanshi yaga tissue akai saikuma kasa ga tissues dayawa da jini ajiki yace "blood? Meya faru daga ina jinin nan yake? Hanunka ne?" Dady ya karbi hanunshi dayaji ciwo yana dubawa, yatsine fuska yayi yace "is not my hand, I had a nose bleed dazu?".

[
2️⃣3️⃣
Chapter 29 · 0% Book details