Sashe 35
In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shigowa sukayi dakin harda likita har lokacin bacci take, Baffa yace "likita wanan baccin baccin lafiya ne daiko" dan murmushi Dr yayi yana zuba wani allura a drip din yace "eh na lafiya ne, wanan ruwan da ake karama ta shike sata wanan baccin shizai sa magun gunan subi jikinta" "to masha Allah" bude kofan da akayi yasa daukan su harda Ammi duk suka juyo suna kallon kofan, Dady ne sanye da manyan kayan dake jikinshi tunna safe sai bodyguard dinshi daya dake biye da shi yariko manya manyan ledoji bin kowa na dakin Dady yay da kallo kafin yakara so ya babbasu hannu suka gaggaisa ya kalli Ammi dake gaban gadon yace "yamai jiki bacci takene" gyadamai kai Ammi tayi ta kalli su Baffa tace "Baffa kutaya mu godiya shiya kawomu asibiti shiya taimaka mana" ta kalli Dady tace "Alhaji ga kawun nin Aneesa daga kaduna suka zo yau" kafin ma Dady yay magana Baffa yakara bashi hannu suka gaisa yace "angode, angode, angode, munji duk abinda kamana daga bakin likita, ubangiji Allah yasaka da alkairi bamu da abin biyanka saidai muna rokon Allahu Subhanahu Wata'ala ya sakamaka da alkhairi" murmushi Dady yayi yace "kudena godemin dan Allah inda ace d'ana baida lafiya koyana neman taimako na tabbatar zaku taimaka mishi kuma ai koba hakaba?" da sauri Baffa yace "maganan ka gaskiya, zamu taimaka mai, ai shi d'a dakake gani nakowa ne, Allah dai ya shirya mana su sanan ya raya mana zuri'a yakare yakuma tsare mana su" atare duk sukace Ameen, Dady ya kalli Ammi yace "tom saida safe, agaidamin da y'ata inta tashi" dan murmushi Ammi tayi tace "Allah yasaka da alkhairi mun gode da dawainiya" Dady ya kalli Baffa da Kawu sani yace "bismillah Alhaji" da sauri Baffa yace "to, to, to, bismillah muje" bude kofa Dady yayi yafita Baffa da kawu sani suka bishi a baya har zuwa wajen asibiti, wani eatry Dady ya shiga suna biye da shi suka zauna kan table, Dady yace "meza akawo mana Alhaji" hannu Baffa yadaga yace "masha Allah akoshe muke, mungode" murmushi Dady yayi still yasa aka kawo musu drinks sanan ya gyara zama yace "masha Allah inamai tsananin farin cikin ganinku ayau, da farko dai sunana Alhaji Muhammad Ibrahim Darham, ina aiki amatsayin senate president of Nigeria, matana uku sanan yarana ashirin, namiji daya gareni wacce matata tafarko wacce Allah yama rasuwane ta haifamin shi" atare Baffa da kawu sukace "Allah yamata rahama" "Ameen, Aliyu sunan yaron saikuma sauran yarana mata, bazan muku karyaba Jiyan nan nafara ganin mahaifiyar Aneesa wuraren sha biyun dare wanda nafi yarda kaddara ce yahada mu dan bancika yin dare a anguwan hakaba na taimaka mata mukakai Aneesa asibiti, Alhaji" yakira Baffa ahankali, amsawa Baffa yayi yace "na'am Alhaji Muhammad" dan murmushi yayi yace "muba yara bane munriga mun manyanta munyi kwana biyun, tun ajiyan dana fahimci kaman mahaifin Aneesan yarasu ne naji mahaifiyarta ta kwanta min arai ainun inata tunanin yanda zan bullowa al'amarin sai gashi kicibus Allah yahadani daku yau kaga yanda Allah ke abunshi ko" yafada yana murmushi yace "da izinin ku amatsayin ku na yan uwan mahaifin marigayin mijinta nakeso inhar kun yarda inason mahaifiyar Aneesa so na aure, auren sunna, kuma karkuji komi Aneesa nariga na dauke ta amatsayin ya inada yara mata guda goma sha tara karata cikin yarana su zama ashirin abin alfahari ne agareni, wanan ce daman maganan danake so namuku da fatan banyi laifi ba bankuma yi karambani ba" washe baki Baffa yayi murmushi fal fuskarshi yace "masha Allah, masha Allah, Alhaji Muhammad ina cikin tsananin farin ciki da wanan batu naka badan komi ba dan shi auren nan dakake ganinshi rahama ne sanan rufin asirin y'a mace ne, tun Fateema na yar shekara biyu mahaifi ta yarasu amma mahaifiyarta taki yarda tai aure, bazan boye makaba banji dadin yanda take rayuwa daga ita sai Aneesan, banji dadi sabida Aneesa yanzu ta tasa wata rana dole tai aure idan tai aure haka takeso ta cigaba da zaman kadaici? Aisai wani ciwo yakamata, abinda za'ayi shine zan sameta da maganan nan yau yau dinan kome tace zan sanar dakai gobe dan zanso ayi auren kafin nakoma kaduna to anriga an girma me za'a wani daga biki kaman bikin yara? To kagani dazaran ta yarda ana sallaman Fateema daga asibiti gobe ko jibi zamuje masallaci adaura auren, zaman su gida su kadai hadari ne gwara yanzu dazaran tadawo karkashin ka saika killace ta nima hankalina zaifi kwanciya nasan cewa na sauke nauyi na lura sanan nakula da iyalin kanina nabada matar shi aure gun kamilin namiji, sanan abu na karshe dazan fadama Alhaji Muhammad shine nayaba da hankalin ka dakuma mutuncin ka yasa kaga na amsa maka maganan nan siteret, dan haka karike amana, karike su amana, kai babba ne, kanada yara mata ka rike Aneesa da mahaifiyarta amana, idan Aneesa na rashin ji kotama badaidaiba ka kirani ni dinan zanzo har gida na lallasa maka ita, ina kuma rokon Allah daya sanya alheri da albarka ciki, mahaifiyar Aneesa kuwa karka damu zamu shawo kanta" murmushi sosai Dady yayi kaman anmai kyautan Aljanna yace "nagode Alhaji, in sha Allah bazaku taba samuna dacin amana ba" murmushi kowa yayi suka mimike bayan Dady ya biya kudin suka fito daga wajen Dady yamusu sallama yatafi.
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
2️⃣9️⃣
Zama sukayi akan gado Abdul zai fara masifa da sauri Aliyu yace "please jekai wanka inaso karakani hospital ne" da sauri Abdul yadaura hanunshi kan goshin shi yace "bakada lafiya ne Leo? Mekema ciwo?" girgiza mai kai yayi yace "am fine" "tome zakaje kayi a hospital?" kaman baiso yay magana yace "I wanna go see someone" kallonshi Abdul yayi irin anya Aliyu ne yay maganan nan kuwa dan yasan baida abokanai shi yanama shiga mutane ne dahar yasan wani dazaije dubawa a asibiti, ahankali kaman mai koyan magana yace "s...o..meo..ne? Someone Leo, waye someone kuma?" dan shiru Aliyu yayi yana kallonshi yarasa taya zai fadamai, dariya Abdul yafashe dashi yakoma kan center table yazauna yana daura kafa daya kan daya yana facing dinshi yace "shegen gora, koka fadamin gaskiya kokuma ko nan da chan like chan fa kofar dakina dinan da sunan rakaka wani wuri bazani ba, so tell me d truth" dan yatsine fuska Aliyu yayi yace "please now, kaga nagaji ni nai driving har nan hannuna duk sun sage karakani mana," da sauri Abdul yace "naji to tell me, who is someone, mace ne ko namiji?" hararan shi Aliyu yayi kafin yadauke kai murya chan kasan makoshi yace "mace" huuuuuu! Wani irin ihu Abdul yyi da ko Aliyu saida ya firgita yakoma cikin gado da sauri yace "are you okay me haka" hawowa gadon Abdul yayi da sauri ya dafa cinyar Aliyun yace "who is she? Yaushe kuka hadu Leo?" shiru Aliyu yayi kaman wanda ke tunani saikuma yadan numfasa yace "I just like her, she's just a unique being, her uniqueness yasa zuciyata zabota" kallonshi Abdul yakeyi yanda yake magana a yangance yana fitar da kalaman daidai dan murmushi yayi yace "itace batada lafiya saisa duk ka rame haka?" lumshe ido yayi kafin ahankali yabude idanunshi harsun dan chanza launi sunyi ja murya chan kasa cikeda damuwa yace "please tashi ka shirya" yanda duk yay wani iri yasa Abdul yaji tausayin shi dan yaga son yarinyar a idanunshi hakan yasa yasauka kan gadon ahankali yawuce ya shiga bathroom baiwani jimaba ya watso ruwa yafito ayanda yabarshi yazo ya tarar dashi yawuce wajen wardrobe dinshi shiryawa shima yayi cikin manyan kaya kaman na Aliyun yay kyau ya feffesa turare yajuyo yace "let's go" tashi yayi ahankali hannu Abdul yamika mai yace "car key karkazo ka kashe ni ahanya hakanan banyi aure na more ba" dan murmushi yayi saikuma ya yatsine fuska yazaro key yabashi karba yayi suka wuce suka fita, kallo Momma tabisu dashi kafin ma su karasa saukowa daga stairs tace "sai ina haka yan samari?" Abdul zaiyi magana Aliyu yarigashi yace "yanzun nan zamu dawo Momma" tabe baki Momma tayi tace "kwaji dashi kayan tusa, intai tsami maji, adawo lpy" wucewa sukayi suka fita suka shiga Abdul ke driving har asibiti, saukowa sukayi sukai ciki suka shiga reception, nurse din jiyace tana ganin Aliyu tagane shi da sauri tafito daga bayan kanta tasha gabansu tace "Sir barka da zuwa, kunsha bambam ne da patient din koba ita kazo nema ba?" gyada mata kai yayi ahankali, da sauri tace "ai bamasu dade da tafiya ba, an sallame su, wlh ansalame su suntafi gida, saida ma nataya namanta daukan jaka namusu rakiya har mota" shiru Aliyu yayi duk yaji ba dadi, ganin yama kasa magana yasa Abdul yace "thank you bari mubisu" ya kalli Aliyu yace "let's go" binshi abaya Aliyu yayi suka fita ganin duk yanda Aliyun yayi yasa yace "kasan gidan sune?" gyadamai kai yayi. "inane?" ahankali yace "Suleja, Sulejan mu?" gyadamai kai yayi daidai sun karaso mota suka shiga Abdul yay reverse suka fita daga gidan.