← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 128

Sashe 77

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yanda yabita da kallo yasa tace "relax, am not going to spoil your expensive phone" tana maganan tana saka number Ammi kafin tai dialing number takara wayan kan kunenta, saida wayar ta gama kuka ta katse Ammi bata dagaba, akaro na uku ne Ammi tai picking takai wayar kunne tareda sallama. "Assalamu Alaykum" wani irin lumshe ido Aneesa tayi heart dinta na girgixa after couple of days da aka kawota prison dinan tadinga kuka tanajin bakin ciki daga baya tazo ta hakura, this is the second time dataji wanan kukan bakin cikin na zuwan mata, she promised her self bazata kara kuka ba, she's a fighter, a strong girl, her mother's daughter da with or without Ammi she can live anywhere and survive.
"Hello waye banaji, helloooo waye?" wani irin ajiyan zuciya Aneesa ta sauke tana danne kukan datakeji yana tasomata da duka karfinta rabon dataji muryan Ammin ta harta manta, karan ajiyan zuciyanta da Ammi taji har cikin zuciyanta yasa kirjinta yawani irin buga, da sauri ta nemi gefen gado ta lallaba ta zauna kirjinta nabugawa sama da da, bakinta har rawa yake tace "A....Anee....s....sah.....na!" lumshe ido Aneesah tayi da sauri jin yanda Ammi ta takirata, cikin wani irin murya kaman na wacce ke shirin kuka Ammi tace "Aneesa talk to me, kece? Fateema na?" bude idanu Aneesa tayi ahankali kafin cikin dakewa da taurin zuciya da wanan muryan nata daya dawo kaman na wata rikakkiyar yar daba tace "Ammi!" wani irin fashewa da kuka sosai Ammi tayi ta wayan jin muryan Aneesan tace "Aneesah meya sami muryan ki? Me suka miki mutanen nan eh, mesa kike magana haka? Innalillahi wa innailaihi raji'un, Ya Allah gani gareka ka karemin yarinyar nan, Aneesah na what happens to you are you okay my baby?" lema leman dataji akan idanunta yasa ta sauri ta taba fuskanta hawaye taji da batasan tayaya ta fitar dasuba, da sauri ta goge fuskan cikin dakewa da wanan muryan nata tace "lafiyata kalau Ammi, kefa? Bakida lafiya ne? Kinyi wani iri menene Am....." bata karasa maganan ba Ammi tasake fashewa da kuka, bata ganin Aneesa amma hakanan tasan tanada babban aiki a gabanta, hankalinta yatashi wanan ba Aneesan ta data bama tarbiya mai kyau bace, this is anew Aneesa, yanda taji tana magana yasa taji zuciyarta ta tsinke kawai kiran sunayen Allah takeyi a zuci, da kyar ta daure ta share hawaye ta tareda tashi da sauri ta kulle kofar bedroom dinta da key sanan tadawo ta zauna ta share fuskanta tass, anatse tace "Aneesah na?" "uhm" ta amsata ahankali, sake daurewa Ammi tayi ta hana kanta kuka tace "kina ina yanzu haka a ina kika samo wanan wayar dakike kirana da ita? Tuntuni kina inane eh? Ina polisawan nan suka kaiki?" dan shiru tayi kaman bazata ce komiba saikuma ta dake zuciyarta nawani irin tafarfasa tace "prison! Ina gidan yari Ammi!" wani irin kuka dayazo ma Ammi yasa da sauri tadau pillow gefen gadon ta taushe bakinta tana kuka sosai, yarta ne Alhaji zaikai gidan yari? 20yrs old mace Alhaji zai aika prison? Me Aneesa tamai? Mai Aneesa tamai? Jibi yanda gidan yari yadawo mata da y'a? Dudda bata ganinta amma jibi muryan yarta, Alhaji ya cuceta bazata taba yafemai ba, Aneesan ta ce yanzu tai rayuwa a gidan yari? Tai wahala taga ukubobi na rayuwa haka? Ko hanyar gidan yari batasani ba amma tanajin labarin gidan yari tunko tana Amarya. Takai almost one minute ba tace komiba kafin ahankali ta janye pillow ta ijiye cikin wani irin muryan ban tausayi Ammi tana girgiza kai tace "how are you Aneesah na? Are you fine? Are you okay? Me suka miki achan? Sun wahalar dake?" gyadama Ammi kai tayi kaman tana gabanta cikeda dakewa tace "lafiyata kalau karki damu Ammi" gyadamata kai Ammi kawai tayi kaman tana ganinta tana mugun mamakin Aneesan, tasan she's just forming tasan karya take mata, tanaji a jikinta yarta ta wahala, tasha azaba, murya chan kasa tace "kina ina yanzu?" kallon hanya tayi tace "ina hanya ansakeni daga gidan yarin suka jefar dani wani mutumi yadaukeni zai kaini asibiti saikuma na farka yanzun nan" da sauri Ammi tace "kika farka? Suma kikayi?" girgixa kai tayi tace "Ammi karki damu, lafiyata kalau" "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesah, Aneesah, Aneesah wayyo Allah na zuciyata zan mutu" Ammi tama rasa natsuwarta sai sambatu kawai take tana kuka sosai da sauri Aneesa ta katse wayar dan inta cigaba da sauraron yanda Ammi ke kuka Ammi will just break her heart ne, kifa kanta tayi ahankali kan cinyoyinta mutumin nan nabinta da kallo, dudda wayan ba'a speaker takeba yana tsintar some maganganun Ammi cikima harda yanda Ammi ke kuka tana tambayanta meya sameta sosai yaji sun mugun bashi tausayi dudda baisan wacece itaba but hakanan yaji ajikinshi something da kuma situation ne yadawo da ita wanan yar daban.

Ringing da wayar ya shiga yi Aneesan taki dagokai balle ta dauka yasa ahankali yace "answer the call, ur Mum is calling again" katsewa wayar tasake yi wani wayan yakara shigowa ganin batada niyyan dauka yasa ya matzo ahankali ya karbe wayan daga hannunta ya kalli screen din kafin yay picking yakara a kunne. Cikin kuka sosai Ammi tace "Anee....sah na" ahankali guy din yace "Assalamu Alaykum" da sauri Ammi tace "bawan Allah waye kai? Ina y'ata?" ganin yanda duk Ammi ta daburce yasa yace "calm down Mum relax, sunana Dr Zaid, a per-term Dr prison din da yarki take, I only come idan akwai any surgical issues daza'ama prisoners, yau na shigo nai surgery bayan nagama naga anyi releasing yarki a sume, I could not leave her that way is against my professional code of ethics shine na dauketa with the hope nakaita asibiti aka dubata tana farfadowa saita nemi iyayen ta but kafin nakai saita farka, relax am not a bad person bazan taba cutar yarki ba dan nima inada kanwa mace sanan inada y'a mace shekarunta biyar aduniya bazan so wani ya cutanmini su ba, yanzu tell me kina ina nakaiwo miki ita nasan Abuja sosai dan wurin zuwana ne" ajiyan zuciya Ammi tasauke ta goge fuskarta tace "bawan Allah nagode maka, yanzu taimako daya nakeso kamin so nake ka tayani kaita Park, kasata a motar kaduna gidan kanin babanta zata" da sauri yace "kaduna Mum, ai am going back to kaduna yanzu haka, kin yarda dani natafi da ita kokuma na kaimiki ita Park din?" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali ta nisa tace "na yarda dakai kodan diyarka dakacemin kanada, ka kaimini ita kaduna zan sanar da Baffan ta zai sameku ya karbeta ahanya" ahankali yace "to shikenan" zai katse wayar Aneesa tadago kai ta fizge wayar daga hannunshi ta kara akunne cikin wani irin murya tace "nace miki inaso naje kaduna ne Ammi?" shiru Ammi tayi kafin tace "keda gidan nan har abada Aneesa, ki tafi wurin Baffan ki nima zanzo nasame ki a wajen, duk wanda ya cutar mini dake nabarsu da Allah, Allah baya bacci no need for you to come back here and cause issues nasanki, ki barsu da halinsu, watarana sai labari kinji, kiyakuri, kije wurin Baffan ki kijirani anan, am coming for you okay" gyadamata kai tayi ta katse wayar ahankali tana huci. Kunna motar yayi yaja ta gefen ido yake kallonta ta mugun bashi tausayi ganin yanda take goge kwalla tana fighter tahana kanta kukan amma takasa, ganin yanajin tausayinta over yasa ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi baisake kallonta ba.
Chapter 77 · 0% Book details