← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 128

Sashe 36

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda suka isa gida Ammi ta shiga kitchen tafara hada musu abinci itakuma Aneesa dasu Baffa suna falon su suna mata fira danji da ita suke bana wasaba Baffa ma da kanshi yafita yasiyo mata gyada dafaffa gwangwani biyu aiko sai ci take aranta sai murna take ashe haka akeji da mutum idan yay rashin lafiya ko wash tace sai an tambaye ta meke damunta.
Shigowa Ammi tayi da manyan kulolin tuwo ta kalli su Baffa tace "akawo miya Alhaji kuci yanzu" girgiza mata kai yayi yana tashi saga gefen Aneesa yana kakkabe riga yace "bari mudan shiga gari nida Na Sani, bayan isha maci kokai zakaci yanzu?" girgixa mai kai Na Sani yayi yace kinji ko, yajuyo ya kalli Aneesa yace "mezan siyo miki inzan dawo?" washe baki tayi tace "Baffa kashu nakeso" hararanta Ammi tayi tace "aikin kenan kwadayayya" rufe fuska tayi da hannu tana murmushi Baffa yadaga ma Ammi hannu yace "kinga, kinga ki barmin diya tahuta yaushe duka duka tafarfado dan haka dole taci tasha abinda takeso, zan taho miki dashi, anjima ai wayanki kinada kati ko" gyadama Baffa kai tayi tace "to kimin flashing danna tuna" da sauri tace "to saikun dawo Baffa" wucewa sukayi suka fita ta kalli Ammi tareda kyalkyalcewa da dariya kwafa Ammi tayi tace "zan cinmiki ne" tawuce tafita daga murya tayi tace "Ammi nazo nataya ki?" daga kitchen Ammi tace "sha zamanki, nama gama kaye kayen kitchen zanyi" Ammi tadau tsintsiya tana gyara kitchen din dan ansoma kiran magrib, turo kofar gidansu da akayi yasa ta ijiye tsintsiya ta leko tsakar gidan wani dan yaro ne yakara so tsakar gidan, fitowa Ammi tayi daga kitchen din tana kallon yaron tace "kai lafiya baka iya sallama bane" murmushi yaron yayi yana jan hanci yana share majinan kan hancin shi yadaga murya yace "Assalamu Alayyykummm wai ance Aneesa tazo awaje" da sauri Ammi tace "injiwa ye?" "nima bantaniba" yay maganan yana goggoge majina da hannu tsumman dake jikin window kitchen dinsu Ammi taja tadan barki kadan tazo gaban yaron tace "zo ashare majinan" sharemai majinan hancin tayi dana hannun shi sanan ta wanke mai hannun da ruwan dake cikin bucket din gaban rijiya tace "wai ance waye?" da gudu yaron yajuya yafita, yaye labulen bakin kofar su Ammi tayi tadaure fuska tace "waye yazo neman ki?" zuru zuru tayi tace "nima bansaniba Ammi" baki Ammi tabude zatai maganan saiga yaron ya shigo da gudu yace "wai yace Yusuf security ne" dan zaro ido Aneesa tayi tace "laaa Yusuf, Ammi mai budema mutane kofan shagon mune, security, hala Madam ta aikoshi" dan jimm Ammi tayi kaman mai tunani kafin tace "dauko hijabi kije kecemai rashin lafiya kikayi saisa basu ganki ba" gyadamata kai tayi takoma falon tadauko baby pink hijabinta har kasa dayay mata kyau fuskanta yay dan fayau aciki ta zura kafanta a slippers batare data tsaya saka safa ba tawuce tafita ahankali tabude kofa tafita, a kofar gidansu taga Yusuf Security zaune kan dan machine dinshi dama uniform dinshi bai chanza ba zuwa kayan gida, ganin Aneesa tafito yasa yasauko daga kan machine yana murmushi yana kallonta daidai lokacin Abdul yayi parking next to kofar gidansu Aneesan daga shi har Aliyu sun zubama on Aneesan data fito daga gidansu tana tafiya ahankali ido, karasowa gabanta Yusuf yayi cikeda damuwa yace "lafiya baki zuwa aiki Aneesa? Maiya same ki fuskan ki duk yay wani iri haka kin kumkumbura idanunki sun fada ciki" ahankali tace "rashin lafiya nayi yau aka sallamoni daga asibiti, ya akayi kasan gidanmu" cikeda damuwa kaman zai hadiyeta danso yace "innalillahi Aneesa rashin lafiya, no wonder tunda nadena ganinki nadena jin dadin rayuwana wlh ko aikin bayamin dadi sam sam, na damu iya damuwa shine nace bari kaga ko bango duniya kike inhar a Sulejan nanne saina nemo gidanku naji ko lafiya" dan murmushin yake tamai koba komi yay kokari tunda har yay tattaki yazo yaji ko lafiya, dan murmushi tasake yi tace "nagode" yanda tai murmushin tana dan juyakai yasa yaji zuciyar shi ya narke ahankali yace "wayyo Allah na, murmushin ki na haukata min zuciya da kwanya" gimtse fuska tayi tana kallonshi ganin haka yasa yasaki dariya yana daga hannu yace "maida wukan to, haba Aneesa sarkin masifa, ke baki bari ta tafasa balle to kone ba'a dan zolayan ki"

Ahankali Abdul dake kallon su Aneesan batare daya kalli Aliyu ba yace "is she the one Leo?" jin shiru Aliyu bai amsashi ba yasa ya juyo ahankali ya kallai su ya gani yana kallo idanunshi sunyi ja sosai kirjinshi na bugawa da sauri sauri danko shi yana ganin yanda kirjin ke sama da kasa tagaban rigan, da sauri yace "Leo, Leo are you okay?" wani irin bude kofa Aliyu yayi yafita daidai lokacin Yusuf ya zura hannu a aljihun wandon shi yaciro dari biyar ya mikama Aneesa yana murmushi yace "ga wanan asai su lemu asha Aneesa" da sauri ta girgixa kai tajuya zata shiga gida tace "kabarshi nagode, saida safe" hannu yasa yakama hijabinta yace "a'a wlh saikin karb......" wani wawan mari aka dauke shi dashi dayasa Aneesa dake kokarin bude kofa juyowa da sauri dan bama tasan yarike mata hijabi abinka damai dogon hijabi, hada ido tayi da Aliyu da idanunshi sukai jajir yana wani irin kallonta, Yusuf dafe kuncin shi yayi dan marin ya mugun shigan shi yana kallon fuskan Aliyun, dauke kai Aliyu yayi daga kallonta ya fizge hijabinta daga hannun Yusuf din yanamai wani irin kallon tsana jiyakr kaman ya chakamai wuka, janye hannu Yusuf yayi daga inda Aliyu yamai marin ya kalli Aneesa yace "waye wanan Aneesa?" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun yace "kasan koni waye dakamare ni, kasan me tsakanina da Aneesa, kasan tun yaushe nasanta nake rainon sonta axuciya kasan koni waye? A whole chief security officer ka mara" cikin mugun zuciya Aliyu yanunamai machine dinshi yace "take your bike and get out of here right now and never come back" "baza'a bar nan dinba, kuma wlh zan nunama kai kuskuren mari na" hannu yadaga zai kodama Aliyu mari da sauri Aneesa ta shiga gaban Aliyun kirjinta na daukan uku uku hakan yasa Yusuf ya tsaya tsak batare dayay marin ba, dan juyowa Aneesan tayi suka hada ido da Aliyun dake kallonta da sauri ta dauke kai ta maida kanta kan Yusuf tama rasa mezata ce gabanta sai faduwa yake itadai kawai bataso Yusuf ya daki Aliyun dan tasan baida karfi, bakinta har rawa yake tace "uhmmm karka marai, yakuri katafi please" cikin fushi Yusuf yace "natafi Aneesa kikace?" gyadamai kai tayi da sauri kaman mai koyan magana tace "uhnnn.....eh, k...katafi" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun tareda mai pointing idanunshi da yatsu biyu yace "watch out, zakasan katabo haifaffen dan Suleja" yahau kan machine dinshi ya burga azuciye yabar wajen bin machine din tayi da kallo harsaida tadaina hango machine din sanan tajuyo ta kalli Aliyun cikin fushi tace "why did you slap him meruwan ka dashi eh?" cikin tsananin zuciya Aliyu yace "why are you talking to him? Nace kiyi magana dawani ne eh?" ganin yanda yake magana kaman zai daketa yasa ta saukar da kanta kasa batare da tace mai komiba shikuma abinda ya tsana kenan, tsawa yadaka mata kishi kaman zai hadiye zuciya yamutu yama manta da bata da lafiya yace "am talking! Mesa kikamai magana? How dare you talk to him haryana rike miki hijabi" faduwa gabanta yayi cikeda tsananin tsoro da sauri tajuya ta kalli kofar gidansu tsoron kar Ammi taji hayaniya tafito take gashi magrib yayi sai kallonsu masu wucewa ake, bakinta na rawa sosai cikin bacin rai tace "wai me ruwanka dani eh? Kadenamin ihu, karka sakemin ihu" tana gama maganan tai fuuu tabi ta gefenshi zata shige gida hanunta ya rike chak da sauri tadago kai ta kallai, fizgota yayi back azuciye.

_duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa_
2️⃣8️⃣

Tunda asuba ta tashi ganin tanada dan karfi yasa Ammi ta kaita bayi tamata brush tareda dauraye mata jiki da towel da ruwan zafi ta taimaka mata ta chanza kaya hakan yasa taji dadin jikinta sosai suka fito, a zaune tai salla sanan takoma kan gado Ammi tahada mata hot tea mai kauri tabata tasha dan yamata dadi sosai nan da nan tafara zufa dan sauki yasoma samuwa kafin daga bisanni tai bacci.
Chapter 36 · 0% Book details