← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 128

Sashe 28

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bodyguard din Dady ne dake tuki ya kalli dayan bodyguard din dake gefenshi yace "who is that woman? Get your gun" da sauri Dady dake bayan mota yana daddanna laptop idanunshi sanye da medicated glass jin suna magana get the gun yasa yadago kai, idanunshi ne suka sauka kan matar daya hango kan titi tana kuka sosai tana musu alamun su tsaya, ganin bodyguard din yakara gudu sosai yana shirin ya kwashe ta yasa yace "slow down Jeff, slow down" da sauri yace "what if is a trap sir" cikin fushi Dady yana kallon fuskan Ammi yace "slow down, Allah shine ke kare kowa, slow down let's listen to wat she have to say, most time inna biyo ta Sulejan nan haka nake ganin mutane alot of them are the poors talakawa basuci abinci bane, let's listen if is help we can offer then we help her" Dady yay maganan yana kallon Ammi still, rage gudun bodyguard din yayi har suka iso inda Ammi take da sauri Ammi ta zagayo tana kwan kwasa glass din motar.

_Duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba ban yafeba wlh, saikin biyani a lahira_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
2️⃣2️⃣

Tana share hawayen dake zubowa daga idanunta da hijabi tana leka motar ta glass duk arude tace "hello, hello, salama alaykum, dan Allah taimaka min za'ayi, dan Allah taimako nake nema, y'ata batada lafiya tana gida unconscious, please kutaimaka ma Y'ata asibiti zaku kaimu" Ammi tai maganan tana sake share hawayen dake zubowa, kallon bodyguard din Dady yayi bayan sun gamajin maganganun da Ammi takeyi yace "wind down" saukar da glass din kasa bodyguard din yayi Ammi tayi tana tsaye wajen mazaunin driver ganin bodyguard sunci bakaken suit da bakin glass, idanu Ammi tadan zaro tabude baki zatai magana bodyguard din yamata pointing baya da hannu yace "talk to my boss" gyadamai kai Ammi tayi arude takoma tabaya, hada ido sukayi da Dady dan wutar cikin motan a kunne yake, da bayan hannu ta goge fuskarta daya kara jikewa da hawaye tace "dan Allah ka taimaka min y'ata batada lpy, tana gida nabarta ita kadai, please dan girman Allah kutaimakamin karta mutu she's my only daughter ita kadai gareni dan Allah kutaimakamin, dan Allah, dan Allah" yanda jikinta ke rawa hawaye na bulbulowa daga idanunta tana sharewa yasa Dady yaji ta bala'in bashi tausayi, he just relate to her condition he just can't imagine yaga Aliyu na ciwo yana ganin rudewan shi saiyafi nata times 8, dan ajiyan zuciya ya fuxar ya kalleta yace "ina ne gidan naku?" da sauri Ammi tamai pointing layinsu tace "wanan layin ne" dan jim Dady yayi yana tunani hakan yasa Ammi tace "wlh da gaske nake ba amanan ka zanci ba, trust me my girl is dying please, dan Allah" ajiyan zuciya Dady yasake saukewa yace "alright I trust you karkici amana, shigo cikin motan" gyadamai kai Ammi tayi bata damuba dan matsalan datake ciki yafi komi ta shiga motar Dady ya matsa dayan gefen itakuma ta zauna kusada kofa tarufo kofan, Dady ya kalli gaban motan yace "let's go" ya kalli Ammi yace "nuna musu gidan" gyadamai kai tayi ta nuna musu layinsu suka shiga har zuwa kofar gidan nasu, akai parking da sauri ta sauka daga motan ta shiga gidan da sauri tana kunna torchlight din wayan Aneesan dake hanunta, dakin Aneesan ta shiga da sauri ganin Aneesan kwance akasa tana convulsing sosai ga nose dinta na bleeding yasa tai wajen da sauri ta dago kanta tana girgizawa ta kurma uban ihu. "Aneesa, Aneesa, ke Fateema haka zakimin eh? Barina zakiyi kaman babanki eh Aneesa, please don't leave me baby girl ke kadai gareni a duniyan nan, banda iyaye banda yan uwa, u are my everything Aneesa, wayyo Allah! Jama'a" Ammi tasake kurma uban ihu not knowing what to do, bama tasan metake ba.

Kallon cikin gidan Dady yayi da Ammi ta bari abude jin ihun Ammi yanadan girgiza kafa, sakejin ihun Ammi akaro nabiyu yasa yabude kofa zai fita da sauri bodyguards dinshi suka fito sukace "is not safe sir, let's go in first" baima tsaya sauraron su ba yashiga gidan ya shiga falon straight yana haska wayanshi cikeda damuwa, da sauri ya shiga dakin Aneesan dayake jin kuka sosai ya yaye labule, ganin yanda Ammi ta rike fuskar Aneesa dake convulsing sosai tana shushure kafa kaman zata mutu yasa ya shiga da sauri bodyguards dinshi biyeda shi yace "subhanallahi" tsugunna wa gaban Ammi yayi yakai hannu shi yataba wuyan Aneesa da sauri yadaga kai ya kalli bodyguards dinshi yace "get me a cold water she's running serious temperature that's why she's convulsing haka" yamikama Ammi dake kuka sosai hannu yace "lemme have her, bani ita nan" ganin Ammi bama tagane meyake cewaba yasa yasa hanunshi ya karbi Aneesan yasa finger shi yana bubbuga kumatun ta kozata dawo normal, daidai lokacin bodyguards din suka shigo da katon bucket da ruwan sanyi suka ajiye kusada shi ya kalli kofan su ya nunama bodyguard din yace "give me that wrapper" zarowa sukayi suka bashi karba yayi yay dipping zanin cikin ruwa gabaki dayanshi yaciro ya daura mata akan fuska ya kalli Ammi data rude yace "don't worry your daughter will be fine" gyadamai kai tayi tana share hawaye takama hannun Aneesan tarike gam tana kiran sunanta. "Aneesa, Aneesa tashi gani nan, kinji ga Ammin ki, bude idonki kigani" ganin bata dena convulsing dinba yasa Ammi tafashe da kuka sosai ta matse hanunta data rike gam tace "dan Allah karki barni Aneesa ke kadai gareni, banda kowa, I don't wanna be alone, kece nake gani kullum naji dadi, Fateema karki tafi ki barni kaman mahaifinki kinji" tafashe da kuka, tsayawa kallonta Dady yayi yanda take kuka sosai tanama yarinyar maganganun, ahankali ya ijiye zanin yasa hanunshi yadebo ruwan a hanunshi yay bismillah ya shafa mata a fuska yana goge jinin hancin nata yana tapping fuska, jin Ammi takirata da Aneesa yasa ahankali yace "Aneesah, Aneesah, ga mamanki nan nakiranki bude idanunki kiganta" ahankali ta shiga rage motsin hartazo tadena convulsing din saida sauke ajiyan zuciyan datake yi da karfi da karfi kaman ma da kyar take kamo numfashi, numfashinta namata wuya, ganin tarage yasa ya kalli Ammi dahar lokacin take goge kwalla yace "bani hulanta mutafi asibitin" da sauri Ammi tamike tsaye tadauko hulanta data rataya akan kofar sip takawo da sauri, karba Dady yayi yasama Aneesan hulan Ammi tamiko hannu takarbeta shima yatayata suka fita da ita daga dakin bodyguards biye dasu har waje, abayan mota aka zaunar da ita Ammi tace "ina zuwa" cikin gida takoma da sauri ta shiga dakinta kudadden Aneesan da aka biyata a lallen datayi na bikin nan ta dauko tadau jaka ta chusa ciki sanan tadauko makulli tafito da sauri ta kulle gidan da kwado sanan ta shiga motan tarufe kofan tana shashafa kan Aneesan dakeda mugun zafi gatanan ne kawai batamasan inda kanta yakeba, jikinta kaman garwashin wuta.
Chapter 28 · 0% Book details