← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 128

Sashe 39

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Saida suka fara tsayawa sukai isha'i sanan suka shiga asibitin, sallama sukayi tareda bude kofan dakin har lokacin Ammi na zaune kan kujera tana kallon Aneesan, zama sukayi abakin gadon sunama Ammi sannu, ahankali Ammi tace "nakawo abinci Alhaji?" girgiza mata kai Baffa yayi yace "bari tukunna yanzu akwai maganan damuke so muyi" dan gyara zama Ammi tayi tace "to Baffa" dan shiru Baffa yayi saikuma yace "Maman Aneesa tsawon wanan shekarun damukai tare tun ina miki kallon matar kanina yanzu kallon kanwata na jini nake miki wacce nakeda iko da ita koba hakaba?" gyadamai kai Ammi tayi tace "hakane Alhaji" gyadakai Baffa yayi cikin nuna gamsuwa da amsan data bayar yace "tsawon wanan shekarun dakika nuna kezaki rike Aneesa bazaki bamu itaba dudda naji haushi amma ban takura mikiba, kikazo kikace ke zaman rainon yarki zakiyi bazakiyi wani aure ba shima ban takura miki ba na barki, ayau nakawo miki wata babbar magana da bazan boye mikiba sonake yau kibani girmana a matsayina na mahaifin yarki sanan waliyinta, kimin biyayya sanan kisani kome nakeso nayi abu mai kyau ne agareki sanan abinda zai ban kwanciyan hankali ne kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali gabanta nadan faduwa, dan shiru Baffa yayi yana kallon fuskarta ganin yanda ta natsu duk tabashi hankalin ta tana sauraronshi yasa yace "sonake kiyi aure maman Fateema" da sauri Ammi tadago kai ta kallai cikin wani irin yanayi na damuwa tace "aure Alhaji?" "e, aure maman Fateema nakeso kiyi, aure rufin asirin mace ne, yarinya dake duka dukan ki nawane da zaki ce zaki zaune ahaka ke bazakiyi aureba zaki dinga kula da yarki ne angayamiki hakan zaiyu ne? Banda ma haka amusulunce hakan baida kyau, kin taba tunanin yanayin da zaki shiga duk randa zaki aurar da Fateema kiyi watanni shekaru baki ganta ba kintaba tunanin yanayin da zaki shiga yanda zakiyi coping?" shiru Ammi tayi tana kallonshi takasa magana, dan murmushi Baffa yayi yace "to kingani, gwara kiyi aure duk randa zatai nata auren kina gidan mijinki karkashin mijinki akwai wanda zai dinga debe miki kewa kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali, murmushi yasake yi ganin batamai gardama ba, ahankali yakira sunanta "Maman Fateema" ahankali tace "na'am Alhaji" anatse Baffa yace "Alhaji Muhammad Ibrahim wanan mutumin daya taimaka miki yakawo Aneesa asibiti dazu yasame mu da wata magana da tamin dadi ainun, ya nunamin shi daga ranan daya fara ganinki yaji yana matukar sonki ainun" wani irin murmushi Aneesa da tun dazu dasuka fara magana yatashi tayi cikeda jin dadi, da sauri Ammi ta kalli Baffa, gyada mata kai Baffa yayi yace "inaso kiyi tunani sosai bazan takura miki ba, gobe nakeso kibani amsa kuma ko kadan banso adau lokacin dazaran an sallami Aneesa za'a daura auren dan zanzo mu daura auren kafin mubar garin nan, Inaso ki natsu kiduba lamarin da kyau, kuma namiki alkwari gobe ni nan da Na Sani zamu fantsama garin nan muje muyi binciken halinshi inmun dawo zamu fadamiki maimuka gano sanan saimuji amsan ki saimu kirashi, inamiki kwadayin aure sosai, so kiyi tunani kinji karki takura ma kanki, Allah ya sadamu da alkhairan shi" gyadamai kai Ammi tayi ahankali tace "Ameen" murmushi yayi yace "to bamu abincin muci mutafi" plate tadauka ta zuba musu tavasu sunaci ana hira sama sama saida suka gama sanan suka mata sallama suka tafi.

Tagumi Ammi tabuga tana tunani sosai sai hango fuskan Dady take, dan motsin da Aneesa tayi yasa tadago kanta ta kalleta ganin idanunta abude yasa ta tashi da sauri tareda daura hanunta kan goshin Aneesan tana murmushi tace "Aneesa na kin tashi zakiyi fitsari nakaiki bayi?" girgixa ma Ammi kai tayi tana murmushi, murya chan kasa tana lum lumshe ido tace "Ammi ki yarda ki aureshi ni inason shi wlh, inason Abba Ammi, please ki yarda kinji" Aneesa tai maganan tana murmushi sosai baki Ammi tabude cikeda mamaki tana kallonta tace "ke, so dama idanunki biyu kinajin duk abinda muke cewa ko" gyadama Ammi kai tayi tana murmushi sosai tarike hanun Ammi tace "Ammi please kinji ki yarda, dan Allah" hararanta Ammi tayi tace "Common kimin shiru anan, zakiyi fitsarin ko bazakiyi ba" turo baki tayi tace "ni banaji, kuma inyazo gobe sainace mai Ammi na ta yarda su Baffa su daura auren" haba Ammi tarike tana kallon Aneesan cikeda mamaki tace "kaman rashin lafiyan nan yasamiki rashin jine ko Aneesa wanan magana haka" dan murmushi Aneesa tayi tace "inda ni namiji ne dani zan badake Ammi" daka mata duka kadan Ammi tayi acinya hakan yasa tafashe da dariya sosai Aneesan tana safe kanta dake mata ciwo Ammi tace "ahh lallai lafiya tasamu, zanci gadanku ne" rungume cikin Ammi tayi tace "please Ammi na ki yarda kinji for me Ammi na, ni inason shi" shiru Ammi tayi tana sauraron ta kafin tadan sauke ajiyan zuciya tace "to shikenan, zanyi tunani in sha Allah" matseta Aneesa tayi tace "yauwa Ammi na, my Ammi najin magana ta, my Ammi is a good girl" dariya sosai Ammi tayi tana shafa kanta tace "Allah shirya" haka suka dinga hira kasa kasa harta sake komawa bacci.

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

3️⃣0️⃣
Chapter 39 · 0% Book details