← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 128

Sashe 65

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau asabar yaune second week din Ammi agidan Dady, wani irin rayuwa take ginawa itada Dady dako Aliyu abin burgeshi yake, tuni Dady yamata kyautan wata dalleliyar mota, dan Ammi is every with a plus arayuwan shi, she gives him happiness, kwanciyan hankali da komi, kome yace yanaso shi zai ci idan yanacikin matsala he don't need to say it Ammi na ganin fuskanshi zata gane ta lallasai, in bed kuwa kullum saiyay sumbatu saisa ko kadan baya iya daga mata kafa, gurxanta yake kaman ba gobe.

mai fitarmin da littafi waje, wlh ban yafemiki ba, Allah kuma yana kallonki
Wani irin soyayya Aneesa da Aliyu sukeyi asirrace na fitan hankali, yanda take juya Aliyu yanda takeso ko saika rantse tamai asiri ne kowani abun, idan tacemai tanaso yay kaza she don't need to repeat it zaiyi saisa itama ko kallon maza batayi dan she really really love Aliyu da duka zuciyanta, Sosai Dady ke bala'in mamakin chanjin Aliyu all of a sudden dudda yaso dagowa kaman soyayya suke da Aneesa amma dai ya share yasan komeye zaiyi tsami watarana suji, yanzu yaronshi aiki yake zuwa office ba fashi and he's so good dan yanada ilimi kan business sosai, ga training dayake yi babu kama hannun yaro all in the name of abinda Aneesa kesone so zaiyi.
Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa, keda Allah, kibiya anan duniya ko a lahira, littafina na kudi ne.

Agurguje Aneesa ke hada breakfast dan kar azo ita kadai direban su ke jira sutafi hadda tariga tai wanka ta shirya tsaf, shigowa kitchen din Ammi da dawowan ta daga dakin Dady kenan danyau itace mai girki ganin yanda Aneesa dabama ta lurada ita ke sauri ba yasa tace "ke lafiyan ki wanan saurin fa" kaman zatai kuka tace "Ammi banso nasa muyi lattin hadda ne kinga takwas saura fa" shigowa kitchen din Ammi tayi tareda dan sauke ajiyan zuciya tace "bakuda hadda yau harma gobe I think, mai makarantan ku yarasu da asuban nan aka kira babanku aka sanar dashi kar yara suzo ba makaranta karfe Tara ma za'ai jana'izar shi babanku ma yaja Aliyu sun tafi gidan rasuwan" ahankali Aneesa tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ammi na sanshi fa shiyamin interview da Abba yakaine, yanada kirki wlh, Allah ya jikanshi ya gafarta mai yasa yahuta" ahankali Ammi tace "Ameen" tasa mata hannu suka hada breakfast din sanan suka kai dining, divan wanda zataci Aneesa tayi taci sanan takoma sama duk jinta wani iri take, Al Qur'ani ta dauka tacigaba da haddan ta a abinta har wuraren 12, tana zaune kan dadduma adaki Dady ya kwala mata kira da sauri tafito ta sauka kasa atsaye taga Dady hakan yasa takarasa wajenshi tace "ina kwana Abba na ya hakuri" kanta ya shafa yace "hakuri Alhamdulillah, je kitchen kima yayanki pancake kinji zansa mamanki wani aiki a part dina" ya kalli Ammi datake murmushi kasa kasa yace "kitahomin da breakfast dina part dina Ummu Aliyu bari naje nadan watsa ruwa" gyadamai kai Ammi tayi tace "Tom" Dady yawuce yafita, Aneesa kuma tai kitchen tashi Ammi tayi zuwa dakinta asama wasu yan magunguna taciro tasha sanan ta sauko tadau basket mai kyau thada breakfast din Dady akai sanan tawuce tafita daga flat din.

Fitan Ammi bayan fitan Dady da Mama tagani dan tuntuni take tsaye jikin window dan tasama flat din ido kowani motsi sukayi akan idanunta. Ahankali tabude kofa da saurinta tai backyard tana gyara daurin wani abu a haban zaninta, ta wajen window kitchen dinsu Aneesa ta tsaya tareda rage tsawo kafin ahankali tai knocking kofar, da sauri Aneesa dake tsiyaya coffee a mug ta kalli kofan, kara knocking da akayi yasa tai kofan da sauri tace "waye?" cikeda fara'a maman su Rauda tace "nice, maman su Hajar ce Aneesa" ahankali Aneesa tabude kofan cikeda mamaki amma dai ta boye mamakin ta, shigowa kitchen din Maman su Rauda tayi tana kallon ko ina tace "nazo shanya ne shine naji kamshi duk ya cikamin hanci me kike dafamana haka Aneesa?" dan murmushin yake Aneesa tayi danko kadan bata saba da matan ba hasalima koda taganta ta gaida ta bata amsawa itace yau harda mata murmushi, matsowa kusada ita Maman su Rauda tayi tana kallon non stick pan din dake kan gas da pancake ke ciki tace "wa kike soyama pancake haka?" ahankali tace "na Ya Aliyu ne" murmushi Maman Rauda tayi tace "wow yarinyar kirki, toni baza'a sammin bane dan kamshin shi yakado ni nan" murmushi Aneesa tayi tace "to" plate ta janyo da sauri Maman Rauda tace "guda daya ya isa ma basai kin samin a plate ba".

4️⃣4️⃣

_duk wacce ta fitar min da book waje batare data tuntubeni akan hakan ba Ban yafemiki ba_

Ahankali ta debi guda biyu tasa mata a plate din tabata karba Maman su Rauda tayi tace "wow Allah amfana Aneesa, gako pancake din so fluffy daga gani yaji su baking powder, naji gidan na kamshin kunun gyada kunyi kunan gyada ne?" ganin yanda Aneesa ta tsaya tana kallonta yasa tace "don't mind me fa, abinki dame karamin ciki Alhaji baya barinmu mu sarara wlh yanzu haka mamaki ma nach....." da sauri Aneesa tace "Ak....akwai kunun gyadan, uhmm munyi" danko kadan batason taji karshen maganan banzan da Maman su Rauda ke mata, murmushi Maman su Rauda tayi ganin tai accomplishing abinda takeso tayi tace "to ina kunun yake nadan diba?" ahankali Aneesa datai flipping pancake din dake wuta tace "yana kan dinning a falo" da sauri Maman su Rauda tace "dan dauki kofi ki debomin kinji yar albarka yabiyabimin rai karkima yaron cikina rowa yafito sa tabon rowan ki" murmushi Aneesa tayi tace "to" cup tadauka tawuce tafita daga kitchen din.
_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa_

Da sauri da sauri Maman Rauda ke warware kullin zanin ta taciro wani katin magani dakeda kwayoyi yan mitsi mitsi, ahankali ta ballo guda daya ta jefa a coffee da Aneesa ta zuba a cup wanda tasan na Aliyu ne, balle wani kwayan maganin tayi ta jefa cikin kullin pancake din ta danna ciki da sauri ta tura maganin cikin zaninta daidai Aneesa ta shigo rikeda cup din kunun gyadan da sauri ta tare Aneesa ta karba tana murmushi tace "Allah yamiki albarka, bari naje dashi nagode, wanan kamshi haka" bude kofan backyard din tayi tafita ranta fess agaban babban bin dinsu ta taka marfin yabudu ta jefa pancake da mug din kunun ciki tai gaba abinta tana kakkabe hannu tace "yauce ranan ka ta karshe aduniya Aliyu, lemme go and call Nazif akwai muhimmin abinda nikeso yamin".
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, zaki iya turo katin MTN dari uku idan bakida banki_
Chapter 65 · 0% Book details