← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 128

Sashe 21

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gudun kar Ammi taji karan ringing wayar daya cika dakin da kara tafito tace me takeyi da waya ware haka, wayake kiranta this night yasa tai picking wayar da mugun sauri hana kokarin hadiye kuka datakeyi takai wayar kunnenta batare datai magana ba, ajiyan zuciya Aliyu daya kasa bacci tun dazu dudda mugun baccin da yakeji yakasa sai tunanin ta yakeyi yasauke ajiyan zuciya ganin tadauka, murya chan kasa mai kunshe da sakonni da dama wanda shi kanshi baisani ba yace "Aneesah are you sleeping?" girgiza mai kai tayi kafin ahankali muryanta narawa sosai tace "a...a'a" tashi yayi zaune daga kan gadon jin yanda muryanta ke rawa kaman wacce ke kuka, murya chan kasa yace "Hey, are you crying?" girgiza mai kai tayi tace "a'a" jin yanda muryanta kefita yasa yaji wani irin damuwa ya dira aranshi, cikeda damuwa yace "are you sick?" "no" ajiyan zuciya yasauke jin lafiyanta kalau yace "is Ammi sick?" girgixa mai kai tayi tace "n...noo" cikeda damuwa sosai yace "why are you crying then a irin wanan lokacin eh Friend?" magana takeso tayi saikuma tafashe da kuka sosai sabida yanda ta tuna mugun mafarkin datayi, tashi hankali shi yayi da sauri yace "kidena min kuka yana dagamin hankali, talk to me" kaman bada ita yakeba ta cigaba da rera kuka ahankali, katse wayar yayi da sauri danjin kukanta yake har jijiyoyin zuciyan shi, ya lumshe ido tareda jinginar da kanshi jikin gado ya fuzar da iska, he's so damn worried sabida kukan dayaji tanayi zuciyarshi batada natsuwa, shi baimasan lokacin da zuciyarshi tafarajin damuwan wata aranshi ba sai akan Aneesa, tsaki yaja ya kalli wayan dayaketa jujjuyawa a hanunshi, sake dailing number ta yayi kaman zai katse saikuma ta dauka, murya chan kasa dake cikeda damuwa sosai yace "wats wrong with you Aneesa? Why are you crying?" murya chan kasa tace "babu komi" girgiza kai yayi yace "a'a, akwai abinda ke damunki tell me we are friends remember" yanda yake mata maganan ataushashe kaman mai lallshin ta shikuma ba lallshin yakeba yasa taji zuciyata ta natsu sosai. "tell me friend what is wrong with you? Why were you crying? Kinyi laifi ne Ammi tamiki fada?" hawayen fuskarta ta share tass kafin ahankali ta girgiza mai kai kaman yana gabanta tace "mafarki nayi" dan murmushi yayi for the first time tunda suka fara wayan yace "wat!! Mafarki kikayi kikema kuka haka?" dan murmushi yasake yi maidan sauti dayasa ta lumshe ido tabude su yace "you are one hella wired girl friend" yadanyi dariya kadan kaman ba Aliyu ba dat u hardly see him laugh, tsayar da dariyan yayi cikeda tsokana yace "tell me mafarkin mekika yi friend nima natayaki kukan to" juya idanunta tayi tareda dan turo baki a shagwabe tace "ai namiji baya kuka, kuma mafarkin tsoro ne sosai shiyasani kuka" cikin wani irin murya na shagwaba kaman yanda tayimai shima yace "frienddd come onnn is just a dream, just a dream" shiru tayi tasa hannu tadafe kirjinta heart dinta is beating way too fast sabida yanda takejin muryan shi, jin shima yay shiru kaman yana sauraron bugun zuciyan natane yasa tace "scary dream, very scary" gyara kwanciya yayi tareda jan bargo yana lallube kanshi dan sanyi yakeji gashi yakara karfin AC sosai, ahankali yace "scary how? Mafarkin is about wat?" da sauri tace "about you" hannu tadaura akan bakinta surprisingly dan bama tasan lokacin data fadi hakaba, gyara kwanciya yace "about me?" yay murmushi sosai yace "my friend had a scary dream about me, tell me about the dream, dodo nazama nazo nacinye ki kome am eager to know" girgiza kai tayi tana turo baki tace "ance babu kyau fadin bad dream" "but ai am your friend right Aneesah?" yatambayeta ahankali, faduwa gabanta yayi sabida yanda yay maganan, batasan lokacin data gyadamai kaiba tace "eh" murmushi yayi yace "alright, tell me, am all ears" shiru tayi na kusan 2min kafin tace "ni bansan meya faruba amma nai mafarkin na kasheka, but baka mutubafa amma nakasheka kumani bansan how ba, kumfa dai nata fitowa daga bakinka kana cemin mesa na tsaneka, maisa na tsaneka nakeson kasheka nikuma sai kuka nakeyi shine nafarka inata kuka" dariya yafashe dashi sosai harda dan dafe ciki, kaman zatai kuka tace "da gaske nake fa stop laughing" jin yanda tai magana kaman zatai kuka yasa yahadiye dariyan yace "okay, lemme ask you some questions" gyara zama yayi yace "kin tsaneni ne?" girgixa mai kai tayi tace "a'a, niban tsani kowaba" dan lumshe ido yayi yabude yace "kin kasheni but ban mutuba, kumfa nafita daga bakina my God wat if kumfan brush ne na toothpaste kinyi tunanin hakan?" yakara kyalkyacewa dawata yar karaman dariya, yanda yake dariyan bakaramin burgeta yakeba hakan yasa tadanyi murmushi, dan shiru yayi yace "worried not, is just a dream kinji Boldest" gyadamai kai tayi ahankali kafin da sauri tace "waye Boldest?" murmushi yayi yace "you mana my friend, Aneesah the fearless lady maima mutum zanen mage a fuska" dariya tayi mai sauti kafin tai shiru shima shiru yayi yana listening to the sound of her laughter kafin chan murya chan kasa yace "inzo gobe?" ware ido tayi tace "kazo kayi mene? Ni Ammi bata barina fita naje wurin kowa, banda hakaba gobe bananan" dan shiru yayi hakanan yaji baiji dadin maganan datayi ba, baiso taje ko ina yafison yaga koda yaushe tana gida akillace, ahankali yace "ina zaki friend?" "zanje shagon danake aiki sanan zandau permission naje nai registration din jamb" da sauri tarufe bakinta tace "laaaa banfa sanka ba inata maka surutu and is not good kaitama strenger surutu?" girgiza kai yayi yace "am not strenger, kin sanni, and I know you, you helped my sister once, and am your friend, your brother dabaki dashi from today, so allow me to do my duty okay" gyadamai kai tayi ta kwanta tareda lumshe ido, ahankali yace "inzo gobe? Inaso na sake ganin kine" ahankali tace "to bari mugani goben to idan Allah yakaimu, saida safe" takatse wayar da sauri, zaro wayar yayi daga kunenshi yana kallo jiyayi kaman ta katse zuciyarshi baiso ko kadan yadena jin muryanta, fuzar da iska yayi ya ijiye wayan ya kwanta yay shiru yana kallon saman dakinshi tunanin Aneesa yake banawasa ba, he really like the girl, yanason everything about her, he just wanna be her friend and take care of her and always support her kaman yar kanwar shi, tunanin Aneesa ya dinga yi har bacci yay awon gaba dashi.
Chapter 21 · 0% Book details