← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 128

Sashe 82

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ban yafema duk wacce ta karanta batare data biyaba.
Dady na kishingide akan kujera yana kallon yanda Maman su Rauda ke kadamai shayi yaji karan motocin police da sauri ya yunkuro jin ana bude gate din gidan, da sauri Maman su Rauda ma ta tashi tace "to lafiya Alhaji ko Aneesa ta tona cewa uwarta ce tasata tasama Aliyu guba a abinci" wani mugun kallo Dady yamata yay hanyar fita daga dakin cikeda jin dadi maman Rauda tace "bari nabiyoka nabama idanuna abinci Alhaji, nima nasha kallo" tai shewa tana fita daga dakin Dady tai tsakar gidan inda polisawan harsunyi parking sun fito su kusan goma sha daya, sojoji guda uku, sai Aliyu dake tsaye agefensu, daidaya ake fiffitowa, ahankali Ammi tabude dakinta tafito sabida yanda jikinta kemata ruwa Aliyu ya zuba mata idanu yanda ta rame sosai tai zuru zuru ga mugun laulayin ciki ga damuwa, zama tayi akan dakalin bakin kofanta da bazata iya tsayuwa ba, tana mamaki dame kuma Alhaji yazo yau? Ko ita zaisa akama yau tunda Aliyu yasa yasaki Aneesa.kin karanta ko to wlh Allah zai tambaye ki akan hakkina.

Baki da kudi to karma ki karanta dan wlh banyafe mikiba harsai kinbiya kudinshi. Karasawa gabansu Dady yayi yamika musu hannu yana satan kallon Aliyu ta gefen idanu yace "barka da zuwa officer, ince dai lafiya meya kawoku nan? Karan motan ku duk ya dagama iyalina hankali jibi yanda yayana da mataye na sukai zuru zuru ince dai lafiya ko? Meke tafe daku?" Dady yay maganan yana gyara tsayuwa yana kallon su Rauda dasukai zuru zuru suna kallon polusawan. Murmushi officer yayi yakalli sojan gefenshi yace "bring him out sajent" da sauri sojan yabude bayan mota kafin ya fizgo wani saurayi da bayanshi kawai suke gani sanan yawani irin juyo dashi da sauri Hajar da Rauda atare sukace "Ya Nazif" ganin yanda dagashi sai dogon wando fuskarshi afarfashe idanunshi sun kumbura tsabagen dukan da akamai Sajent ya kawoshi gaban Dady ya tsayar dashi, cikeda mamaki Dady yace "Nazif, mekayi haka? officer kuje kusami babanshi Nazif bayajin magana ai yaron yayan matata ce, me yayi haka? Allah dai ya kyauta" Dady yafada cikin bacin rai dan bai manta yanda yaso yay raping Rauda ba haryana yunkurin dukanmai Aliyu.

Da idanu officer yama Sajent wani signal hakan yasa sajen yadaga kafarshi dake sanye da wanan makeken booth din sojojin.

Booth din sojojin nan ya daki bayan guiwan kafarshi daidai saitin jijiyoyinshi wani irin ihu Nazif yayi na azaba har majina nafitowa tsabagen wahala yana ihu, wani irin tausayi yabama Maman su Rauda da gabanta ke faduwa tace ubanme kuma yaron nan yayi ko ankamashi yana shaye shayenshi ne.
Cikin wani irin ihu officer yace "kafadi abinda kafada mana a station ko in datse kafar nan gabaki daya" da sauri kirjinshi na bugawa bim bim bim yace "wlh zan fada, wlh zan fada, kuwa Allah karku sake dukana wlh zan fada" officer yace "ohon go on muna jinka" zufan wahala Nazif ya share yakalli Dady dake kallonshi yace "ranan uku ga watan April ina zaune agida, Maman su Hajar takirani" wani irin masifaffen faduwa gaban Maman Rauda yayi take wani fitsari yatarun mata a mara. Yace "ina zaune agida takirani tace na shiryo nazo idan zan taho nazo da laptop din aikina yanzun nanfa, nace mata to, nazo ina zuwa tajani zuwa sama gaban wani daki nagga tasa password tabude muna shiga naga computer ne dayawa na CCTV aciki, tacemin dakin Aliyu nada CCTV tatabaji kafada so tanaso nahada mata fake video Aneesa tazuba poison a abincin Aliyu, cikin yan awanni kadan nahada mata shi tsaya nasaka a CCTV footage din sanan tabani kudi dayawa natafi" innalillahi kawai Dady yake ambata a ranshi bairiga yakaiga magana ba Officer yace "karfe bakwai tama danka a police station Alhaji yabamu labari daga A zuwa Z binciken dayayi jiya (yabama Dady labarin komi da Aliyu yayi) after munyi verifying footage din duka daya nunamana ta wayanshi muka kira specialist ya tantance mana da tabbas wanan video karyane, sanan Aliyu yanuna mana asalin video gaskiyan inda matarka ta shigo har kitchen dinsu Aneesa lokacin datake girki ta tura yarinyar kawo mata kunun gyada tazuba guvan a abincin ka, specialist dinmu yaduba video ya shaida mana da cewa wanan ba fake video bane, ga videos din ka kalla da idanunka" Officer yamikama Dady babban police ipad da video ke ciki, Dady hannunshi har rawa yake ya karbi video ya shiga kallo kasa tsayuwa yayi ya zauna a kasan tsakar gidan matayenshi suka taru da yaranshi suna kallo banda Maman su Rauda da gabanta ke faduwan da tunda aka haifota batajin yataba irin faduwan nanba.

_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

5⃣7⃣

*_Bonus_*

Tun Dady na kallon video yana salati a ranshi harya farayi abayyane yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, Innailaihi wa innailaihi" he could not believe what his eyes is seeing right now, is he dreaming or what. "lahaula wala quwata illabillahil Aliyul azeeem" zama kawai Rauda tai akasa kusada Dady ta kifa kanta aguiwa tana kuka sosai, all this while tana tsitsinema Aneesa dataso kashemata Yayanta ashe mahaifiyarta ce, Hajar kam idanunta yay jajir ta juyo ta kalli maman tasu irin kallon nan na bana fadamiki ba, kome zakiyi kiyi banda kissa, banda kissa, akwai wani abu da kisan kai da no matter how long it takes asirin ka natonuwa one day one day. Hawaye ne yataru a idanunta sosai, sauran matayen Dady ma jikinsu yay sanyi iya sanyi, sun tsani Aliyu suma sunsan hakan but bazasu taba iyayin abinda Kareema tayiba, basu tabamai tunanin kisa ba ko wani abu makamancin hakan, burin su kawai su kuntata mai, su ganshi cikin kunci koda yaushe, suga shida Alhaji na fada always shikenan kawai nasu, Maman su Rauda ta dauko da zafi.
Chapter 82 · 0% Book details