← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 128

Sashe 110

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mikewa tsaye Hafiz yayi da taimakon Mahaifin shi shi kanshi mai Martaba saida yaji wani iri dan yaga so kwatankwacin irin son dayagani a idanun Aliyu shima haka Hafiz ke sonta, ahankali yake daga kafa wasu fadawa biyu suka budemusu kofa juyowa mahaifin shi yayi cikeda murmushi yace "to mun barku lafiya, Allah yadawo daku kuma gida lpy" wani iri Aneesah taji kaman zata haukace batasan lokacin data dago idanunta dasukai jajir ba tsabagen kuka, hada ido tayi da Hafiz da Mahifinshi ke rike da shi zai fitar dashi waje, tunda take da Hafiz bata taba ganinshi a irin yanayin nan ba idanunshi sunyi jaa sun cika da kwalla sai kallonta da Aliyu yake ahankali Babanshi yajawo shi da baya baya yafita daga dakin yana kallon Aneesah har lokacin mahaifiyar shi tabisu tafita sanan fadawa suka rufo kofa wani irin fizge hannunta Aneesah tayi tamike da sauri tana kuka kowa nadakin yabita da kallo bude kofar fadan tayi daidai Hafiz na shirin shiga mota a parking space din dasukai parking motarsu dake facing fada, tsayawa yayi chak yakasa shiga ciki maman shi zata kirashi taga abinda yake kallo saitai shiru, dawani irin gudu Aneesah ta taho har gaban motan, tsayawa tayi gab dashi kaman zata shige jikinshi tafashe dawani irin kuka tama kasa bude baki tamai magana sai kuka, lumshe ido yayi yay shiru sai chan yabude idosu yana kallon yanda jikinta ke bari tanamai kuka kaman zata sume, murya chan kasa da bata fita sosai yace "bakimin komi ba Fateema I know how much Aliyu means to you, shine suna na farko dakika fara kiramin a healing process dinki, who am I nace zan shiga TSAKANKANIN SOYAYYAN gaskiya eh? Tayaya ma nazo harna shiga ATSAKANIN SOYAYYAn ku?" yadanyi shiru yana kallon yanda take kuka sosai tana kallonshi murmushi ya sakin mata ahankali yace "stop crying okay, ga mijinki chan yafito yana kallonki go and meet him, ina miki fatan alhairi arayuwan aurenki, Bissalam" yana maganan ya shige cikin mota tareda rufo kofa yana goge hawayen dasuka zubomai da sauri, Maman shi tace "mutafi Alhaji" kunna motar Mahifinshi yayi yaja sukabar wajen Aneesah ta duka akasa tana kuka sosai, she's feeling way to bad, super bad ma, ahankali Aliyu da idanunshi sukai ja yatako har zuwa inda take tsugunnawa yayi ahankali gabanta tareda daura hannunshi akan bayanta, murya chan kasa kaman zaiyi kukan shima yace "is okay, stop crying, let's go back inside wife" cikin wani irin masifa danji tayi mugun haushin Aliyun takeji ta ture hannunshi tareda mikewa ta kalleshi da jajayen idanun nan nata dake fitar da hawaye tace "don't call me wife am not your wife Ya Aliyu, kazo kaja kowa fushi yake dani, mesa baka barni anyi aurena da wanda yan uwana kesoba haaa, Ammi na fushi take dani, wanda yakamata na aura haushina yakeji all because of you Aliyu, wayace kasato ni, why did I even meet you in this life eh? To wlh bari kaji baruwanka dani dagayau sai yau, kadai aureni ba toni ban aureka ba, and bazan zau....." wani irin fizgota Aliyu yayi cikin fushi harsaida tafada jikinshi fuskarta yay cupping idanunta sunyi ja, cikin wani irin yanayin fushi yace "this should be the very last time kike dagamin murya kina magana, watch your tongue, and duk randa kika karamin maganan wani namiji ko wani ma at all that will be the first time I will so punish you da saikin raina kanki, you are my wife my property a yanzu duk duniyan nan ko Ammin ki batakaini iko dake ba, and am your husband give me my respect, the next time you talk to me in this manner I will show you who the man is" yafada cikin wani irin fushi da saida gabanta yafara faduwa, sakinta yayi cikin rashin wasa dan mugun haushin yanda tazo tanama wani kato kuka yake yanuna mata kofar fada yace "let's go" dudda yanda bakinta ke kumfan tamai tsiwa kasawa tayi danji tayi tana wani irin shakkan shi, ahankali tadaga kafa tafara tafiya yana biyeda ita abaya kaman ance za'a sacemishi ita, bude kofan yayi tareda rikemata hannu suka shiga ciki suka koma inda suke zaune tana kuka.

Gyaran murya Mai Martaba yayi yace "Alhamdulillah sun dawo, Fateema" yakira Aneesa da kanta ke kasa tana goge hawaye.

Ahankali Mai Martaba yace "inaso ki yafema baban mijinki, yay kuskure, ya cutar dake dakuma rayuwanki, mahaifinki ne mahaifinki will always be mahaifinka no matter what, kuskuren dayayi kuskure ne da kowa anan cikin mu kan iya aikata shi and am sure yanzu yay nadama sanan yadau darussa da dama game da lamarin sa'an nan wayanda suka hada miki wanan shairin suna chan gidan yari suna biyan bashi, sunyi hakane dansu raba kawunan ku ku tsani juna ku yanzu inaso you people should shame devil ku koma Abuja as one big family, kiyakuri kinji Fateema" gyadama mai Martaba kai tayi tana goge hawaye, Mai Martaba ya kalli Ammi datake share hawaye yace "kiyakuri Rukayya kiyafe ma yayanki ki sanya ma auransu albarka, ki koma gidanki kicigaba da bautan aure Allah kuma ya saukeki lpy" da sauri Dady yace "Ameen" Baffa da Inna ya kalla yay murmushi yace "Baffan Aneesah yanzu lokaci yayi dazaka ce wani abu dukkan abubuwan nan nada fadi nafadesu ne amatsayin na sarki wanan dole ne kuma hakkina ne na tabbatar da zaman lafiya a alumman dasuke karkashina kaine mahaifin Aneesah kace wani abu" murmushi Baffa yayi irin tasu ta manya yace "ai kariga kagama komi Allah ya taimaki mai Martaba, wlh dama tun farko ban riki mahaifin Aliyu dakomi ba sabida ni nasaka kaina amatsayin shi na kimanta Al amarin da ace nine shi still abinda yayi shine zanyi, makircin mata babu abinda baya haddasawa saidai kawai anemi tsarin Allah daga hakan, zancen auren Aliyu da Aneesah kuma banda wani ja da lamarin ubangiji shi rabo dakake gani har kissa yana iyayi dan haka muna addu'a ubangiji Allah yawa auren albarka yakuma basu zaman lpy, nasan halin Rukayya tun kafin ta haifo Fateema mace ce mai hakuri shiru shiru batada fushi amma intai fushi abin bakyau, Rukayya inaso kaman yanda mai Martaba yace kiyakuri babu wanda ya isa ya ketare abinda Allah yace zai faru, ki manta dakomi sanan kitashi daga nan fada, dake da mijinki da yaranku kutafiyan ku gidan ku a Abuja aje asha biki y'ay'a, Allah ya gafartama magabatanmu sanan Allah ya yafemana kurakuran mu, iyakan abinda zance kenan" ahankali Mai Martaba yace "Alhamdulillah, daga yanzu ninace komi yawuce matsala yakare ko Rukayya" yay maganan yana kallon Ammi da kanta ke kasa, dago kai Ammi tayi ahankali idanunta sunyi ja, ahankali tace "hakane Mai Martaba yawuce in sha Allah" murmushi yayi yace "zansa akaiku har Airport, kai Aliyu kabisu inyaso zansa a aiko da motarka gida, Allah yamuku albarka gabaki dayanku, sanan Allah yamaida ku gida lafiya" sanan yarufe taron da addu'an da annabi ya koyar sanan yakira wasu fadawa aka fito da wani jeep sanan Mai Martaba yace sufito, karasawa kusada Ammi Dady yayi da sauri yana kallon fuskanta, ahankali yamika mata hannu alamun ta rikeshi ta tashi batare data kalleshi ba takama hannun har wani irin ajiyan zuciya ya sauke ganin takama hannunshi alamun ta hakura kenan sanan sukayo waje, Baffa dasu Nasani ne suka shiga motarsu bayan Mai Martaba yasa ancika musu mota da tsaraban zazzau sanan Dady da Aliyu da Ammi da Aneesah suka shiga babban jeep din da Mai Martaba yabasu inda fadawa ke tukasu har Airport din kaduna.

Kafin Aliyu yasai musu ticket din first class na Air peace airlines dayake 2 za'a tashi yasa sukaje sukayo salla Aneesah takasa yarda su hada ido da Ammi Ammi kuma na lurada ita amma ta share ta koma menene saisun koma gida, karfe 2 daidai jirgin su yadaga zuwa Abuja.
Koda suka sauka Airport din Abuja babu mai cema wani abu kowa yay shiru Aliyu ya fuske kodan kunyan Ammi yaje ya sace yarta ya aure bayaji saima wani nishadi yake yana saton kallon fuskan Aneesah dayaga taki daga kai balle yasaran zasu hada ido.
Chapter 110 · 0% Book details