← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 128

Sashe 22

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Da kyar Ammi ta tadata da asuba tazo tai salla sanan tai karatun Al 'Qur'ani, saida gari yawaye sanan ta wuce tadauko tsintsiya ta gyaro dakunoni ta sharo tafito da sharan waje sanan ta wuce kitchen tahura wuta tasa ruwan wanka awuta sanan tadau tsintsiyan ta sharo tsakar gidan, ta gyara ko ina sanan ta koma kitchen ruwan wankan tahada ta daura shinkafar da Ammi ta dafa jiya jiya dan dumamawa tawuce tafita daga kitchen din dauke da bucket din ruwan zafi taja ruwa daga rijiya tahada tawuce daki tacire kaya tafito tadau bucket din tai bayi bata wani jimaba tai wanka tafito sanan ta shiga kitchen ta sauke abincin ta daurama Ammi ruwan wanka tazuba nata abincin a plate sanan tafito tawuce kitchen afalo ta ijiye abincin kusada Ammi sanan tawuce dakinta ta shafa mai, shiryawa tayi cikin Riga da skirt nawata maroon atampa dayay mata kyau sosai ajiki sanan taciro gogagen hijabinta maroon tafito falo kafeta da idanu Ammi tayi tanabin kayan jikinta da kallo harta karaso wajen zama kusada Ammi tayi dake kan dadduma tace "Ammi na bazaki yi karin yanzu ba muyi tare" girgiza mata kai Ammi tayi tanajan charbi hakan yasa ta shiga cin abincin cikin yan mintoci kalilan tagama ta tashi takai plate din kitchen sanan tadawo daki tadau hijabin ta tasaka ba karamin kyau maroon din yamata ba ta dau jakanta ta sagala tana kallon agogo karfe bakwai da minti arba'in da biyar tace "Ammi natafi" gyadamata kai Ammi tayi dan bataso ta katse zikirin datakeyi juyawa tayi tai hanyar fita daga dakin harta sa kafa zata fita saikuma tadawo a shagwabe tafada jikin Ammin tace "nikimin addu'a Ammi" shafa addu'a Ammi tayi ta ijiye charbin tadan buge bayanta tace "inkin karyani aisaiki nemo wata Ammin ko" dariya tasaki tana tashi daga jikin Ammin tace "Ammi nifa banida nauyi fa" hararan ta Ammi tayi takama habarta takai yatsarta gefen idonta tace "jibi kwansa a ido, bakisan idan zakisa kwalli zaki ciccire kwansa bako" turo baki tayi Ammi takarasa cire mata harda na dayan idon sanan tasaki fuskarta tace "saikin dawo to, Allah ubangiji yabada sa'a, Allah ya tsaremin ke" wani irin cute smile dake mugun karama fuskarta kyau tasakin ma Ammi tace "Ameen Ammi na, nagode natafi" tashi tashi ta wuce tafita Ammi tabita da kallo zaure tayi tabude kofar gidansu tafita tana tafiya anatse as usual tana kallon hanya tana fatan Allah ya kado wani mai keke napep danyau jinkanta take bata da karfin daddarawa har express road da kafa.
Bata wani yi nisa da tafiya ba saiga keke napep tsareshi tayi ta shiga tace "express road Malam" kunna keken yayi yace "dari da hamsin ne Hajiya" "to muje" Jan keken yayi sukai gaba har gaban shagon su yasauketa tun kafin ta sauko Yusuf security dake bakin kofa ya tsareta da ido kaman zai hadiyeta dauke kai tayi ta sauko taciro kudi ta bashi sanan ta rataya jakanta back tafara tafiya tana dosan gaban shagon nasu, washe mata baki Yusuf yayi yana binta da kallo tundaga kan kafafun ta dake sanye da black socks har zuwa kan hulan hijabin ta daya kwanta akan fuskanta, numfashin shi har neman daukewa yake sabida tsananin bugawa da zuciyanshi keyi sabida ganin ta dayayi karasawa tayi jikin kofan kafin ma ta gaidashi yarigata. "barka da zuwa Aneesa gimbiyan mata, sarauniya mai farin jini" bayabo ba fallasa tace "ina kwana" tasa hannu zata bude kofan da kanta da sauri ya tare yace "tsaya nizan bude miki Gimbiya ai ba'a barin gimbiyoyi suyi aiki da kansu baki saniba?" Yay maganan yana lashe baki yana kallonta cikeda da dan masifa tace "kabude min zanje naga Madam ne Yusuf" da sauri yace "karki damu Madam batariga tazo ba akwai abinda nakeso nafada miki ne" jitayi kaman ta kwasa mishi mari mugun haushi Yusuf yake bata hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ko damuwa baiyiba yacigaba yace "Aneesah dan Allah sonake kibani dama naturo gidanku wlh ina bala'in sonki, wlh matukar burgeni wlh narasa yazanyi da raina kiwa Allah kibani dama naturo" juyowa tayi tamai wani irin mugun kallo tace "Yusuf kaga ina baka girman ka ko to kakama kanka, babu wani na shagon nan dabaisan kana soyayya da Fatima ba, banson rigima kadena shigar dani harkan ku kuma kacire hanunka ka matsamin na shiga shago inba hakaba idan madam tazo tace maisa banfara aikiba zancen mata kaine kahanani shiga shago tun dazu" washe mata baki yayi yana wani irin mahaukacin murmushi masifan Aneesa na masifar burgeshi dan matsawa gefe yayi yace "Allah huci zuciyar gimbiyar raina ki......" bude kofar Fatima tayi daga ciki da fushi tana ma Aneesa wani matsiyacin kallo.

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

1️⃣7️⃣
Chapter 22 · 0% Book details