← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 128

Sashe 119

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

Ahankali Aliyu ya share hawayen daya zubomai yajuya ahankali dan baiso su ganshi yay hanyar stairs sauka yayi kasa, nauyin da zuciyan shi kemai ne ya sauka sosai he is super happy Aneesah ta yafema mahaifin shi, bude kofar falon yayi yafita ya wuce part dinshi zuciyar shi wasai, ahankali yabude kofar falonshi ya shiga Hajar daya gani atsaye a tsakar falonshi yasa ya tsaya chak daga wurin kofa ya mugun daure fuska yana kallonta, kafin ma yay magana da sauri ta saukar da duka kafafun ta kasa ta hade hannayenta batare data dago kantaba cikin wani irin cool murya tace "Ya Aliyu dan girman Allah badan niba bakima dan halina dana Mamata ba kadubi son dakake ma Rauda yau naci darajan marigayiya Rauda karka koran ka saurareni dan Allah wlh kainazo nema" Allah data kira dakuma darajan Rauda da takira taci yasa Aliyu bai kadataba, shigowa dakin yayi batare daya ko kalleta ba yawuce kitchen dinshi yogurt ya tittilo a kofi yafito rikeda shi yadawo kan kujera shi yazauna yana kallon TV dake aiki, kurban Yogurt din yayi sanan yadago kai ya kalleta from head to toe, tarame iya rama tai duhu dudda dama Rauda ce kadai mai haske adakin dan Dady tabiyo Hajar namanta tabiyo dan bakace ita daman amma bakin datayi yay yawa ga shegiyan rama tausayi sosai yaji tabashi ya kafe kafafun ta da kallo yanda suke rawa danta gaji da kneeling, da yatsa yamata alamu data tashi ya nunamata kujeran dake facing wanda take kai, tashi tayi ahankali sum sum taje ta zauna tana kallonshi yogurt dinshi yasake kurba sanan ya kalleta yace "ina jinki talk" shiru tayi gabanta nafaduwa kafin ahankali tace "Ya Aliyu zan fara da kaina, dan Allah Ya Aliyu ka yahakuri da dukkannin abubuwan danamaka abaya, sai yanzu da babu Mama babu Rauda nagane no matter yyaya kai wanmu ne duk inda za'aje adawo kai wanmu ne Ya Aliyu no body can deny this, I never knew a day like this was coming" tai shiru dan bakinta na rawa tace "Ya Aliyu dan Allah kacema Dady ya yakuri ya yafemin, baya amsa gaisuwana sanan gabaki daya ya kwashe kannina ya gyara flat din Amarya dama yariga yasa an fitar da kayansu an kai musu gidansu yamaida flat din dakin yara duka yaran suna flat din yakawo musu Nany kusan guda shidda kullum a musu girki amusu wanka a tafi dasu school da yamma haka sutafi islamiyya, ya Aliyu rabona danaga kainaina kona rike musu hannu na manta sainai na hangosu ana shiga mota dasu, Dady yace karya sake yaji labari nama shiga flat din so yake ya hada kan yaranshi bayason na batamishi su da mugun halina wai ni kadai naita zama a flat din Mamana ya barmin flight din, Ya Aliyu Dady ya tsaneni banda abinci baya bani komi yanzu baimason ganina nasan kawai sabida babu yanda zaiyi ne da wlh har korana zai iyayi, ni banda saurayi har yanzu danai aurena nahuta nima da wanan tsanar ta Dady, Ya Aliyu bansan mesa Dady ta tsaneni ba, wlh wlh Ya Aliyu katuba CCTV camera kaga na laundry ranan da Mama tacemin zata kasheka har fada munkusa yi saida nace mata kome zatayi tayi banda kissa, kisa babban abune dudda nasan banasonka den but I felt somehow da Mama tai wishing dead akanka, to Yaya zanyi? Nasan ba Aneesah tasama gubaba amma Inna tona Mama zata iya tsinemin albarka Yaya zanyi?" tafashe da kuka sosai kurban yogurt Aliyu yayi batare daya kalleta ba yace "inda Rauda ce ba tsinuwaba ko tsireta maman ku zatayi Rauda saita fadi gaskiya, Rauda is such a brave good sister, sometimes I use to wish dameke uwarki ta kashe ba Raudana ba" yay shiru zuciyar shi na zafi baiso yana tuna rasuwan Rauda dan injury din dawomai fresh yake he just wish tana alive, shiru yayi yana sauraron yanda Hajar ke kuka, in a very bitter manner yace "an bakin halinki ne yasa haryau baki da mashinshine, as small as u Are Hajar ur mind is so evil, am at the point of Death ga baiwar Allah dat has noting to do with evil dunku kukaja taje prison for selfish reason naku tayaya mace irinki zata sami miji eh? Ko my enemy I will never wish for him ya auri yarinya kamar kiba, Evil mind, evil character, mena taba miki in this world dakika tsaneni eh? Tell me?" fashewa dawani irin kuka Hajar tayi gwanin ban tausayi ta zamuyo daga kujera takara kneeling tareda hada hannayenta alamun Yaya hakuri tana kuka sosai tama kasa magana, dan tabe baki Aliyu yayi yace "yau ina uwar taki mai dauremiki gindi? Where is she now to protect you ta baki duk abinda kikeso? Mai koyamiki duk abinda kikeyi kinayi thinking all your life she will always be by your side protecting you tana ina yanzu?" Aliyu yamata tambayan yana daga murya kafin yay dan murmushi yace "tana prison" dan shiru yayi yana kallon yanda take kuka yace "kin manta lokacin ko ganina kikayi saidai kiyi tsaki, kiyi habaici, in Rauda tazo Gina kuhadu kumata duka, ki zagen kiyi dis kiyi dat, yau meya hanaki yin hakan Hajara? Is it because mahaifiyar ki bata gidan nan? Have you release your mistake? Bari kiji duk yaron dazai zauna ya dinga tapka iskanci, dakowace tsiyace thinking iyayenshi nanan zasu karemia they always have his back that child is mistaking nobody knows tommorow, idan Allah bai rabaka da iyayen ta hanyar daukan ransu ba to wani abu nanan faruwa, annabi yace ama iyaye biyayya quit sure but ba'ama iyaye biyayya awurin sabama Allah" shiru yayi yana kallon yanda take kuka tabashi tausayi but ina bazai taba nunamata hakanba is her time to ripe what she saw danhaka so be it, ajiye kofin yogurt yayi ya rungume hannunshi yace "kinzo kin samen kan inbama Dady hakuri? Listen and listen attentively, hear me loud and clear Hajara bakida matsayin dazanje na rokan miki Dady, problem dinki is u and him so deal with it alone, abu daya zan iya gayamiki shine go and ask Aneesah dakuma mahaifiyarta for forgiveness inba hakaba bakida komiba alhakin wani baya yafuwa sai inshi ya yafemaka, and lastly kitashi dust ur kneels and leave my room jejely before I loose my temper dan am not gonna be as nice as this Aliyu dakike gani sitting down haka" mikewa tsaye tayi ahankali tana kuka sosai tai hanyar fita daga kofa tana kallonshi ya rakata da harara harta fice. Ajiyan zuciya yasauke ya cigaba da shan tea dinshi. _how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa banki can also send MTN card 300_

_duk wacce ta karanta min wanan littafin batare data biyaba ban yafe mataba, in bakidashi don't even read_

_masu fitarmin da book waje kuda Allah wlh_

_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

8⃣5⃣

Ammi tadade jikin kofar dakinta tanajin draman Abba da Aneesah, Aliyu data hango ta hole din kofarta yasa bata fitoba tana kallon yanda yake goge hawaye sosai taji gabaki dayansu sun bata tausayi, Alhamdulillah komi yawuce yanzu sai new life, yanzu zata fara planning gagarumin bikin yayanta guda biyu, ganin Aliyu yatafi yasa itama takoma kan gado tazauna saikuma ta tashi ta shiga bayi ta watso ruwa tana fitowa ta chanza kaya tareda kwanciya ko minti biyu batayiba wani bacci mai nauyin gaske yay awon gaba da ita abunku damai ciki kaman ba itane tagama bacci dazun nan ba, ko cikin bacci taji anyi cuddling nata saidai takara shigewa jikin Dady batare data tashiba dan mugun bacci takeji.
Inkika karanta baki biyaba banyafe mikiba

Wani gagarumin shirye shiryen biki aka shigayi, fess Ammi tahana Aliyu shigowa part dinta Aliyu tsabagen rashin kunya harda kai karan Ammi wurin Dady, Dady ma yagoyama Ammi baya yace shida ran Saturday zasu tafi C.A shida Aneesah me abun damuwa, yahakura yanzu abun mata ake kuma dama haka yake a al'ada ba'a bari ango yaga amarya sai ranan biki ranan bakin ciki kaman ya kashe Aliyu. Tuni Momma da Abdul zunzo sun bama Ammi hakuri, Ihsan tadawo best friend din Aneesah, aka shirya aka manta komi, tunda Ammi ta lura Nani Dady ya kwasoma yaranshi tanunamai fushinta sosai akan hakan nan tasa akabar Nani daya sauran aka sallemesu ta karbe yaran duka tana bamu tarbiya mai kyau tana lura dasu kuma alhamdulillah yaran suna sonta saidai yan matsalan da ba'a rasaba yau da gobe, Dady na bala'in alfahari da ita, ga ciki ga nauyin yaranshi sanan ga hidimar biki duk ita kadai, duk in yatuna abinda yama Aneesah dudda sun riga sun nunamai komi yawuce sai yaji kunya yakamashi, hakama saida Ammi tasa baki sanan Daddy ya yafema Hajar dan taso ta rokesu gafara, a lokacin da Ammi tanunama Dady tanaso tadawo da Hajar flat dinta nuna mata yayi ina, a barta a flat din uwarta tacigaba da zama anan amma bazai taba bari tadawo flat dinta ba sai tazo ta kashe su wata rana inaaa.
Chapter 119 · 0% Book details