← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 128

Sashe 70

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tundaga yanda Ammi taga fuskarshi gabanta ya shiga faduwa ta shiga ambaton Allah, dawani irin zuciya Dady ke dumfaro su harya karaso inda suke tsaye hannu yasa yawani irin fizgo Aneesa dake tsaye kusada Ammi jikinta na rawa Dady baiyi wata wataba ya daga hannu ya watsa mata lafiyayyen mari "tass!" runste ido Ammi tayi dan har kashinta taji marin da Dady ya dauke Aneesa dashi, fashewa da kuka sosai Aneesa tayi tsabagen tsoro tamika hannunta tana kokarin kamo Ammi tace "wayyo Allah na Ammi, Ammi, Ammi, Ammi n...." zuba mata wani marin Dady yayi akaro na biyu da saita yasa tai shiru tai gum tama kasa magana sai dubu datake gani a idanunta cikin ihu da daga murya Dady ya jijjigata yace "me Aliyu yamiki? Meya miki kikeso kiashi lahira? Ubanwa yasaki kikashe min d'a??" yakara daga hannu zaikai mata mari na uku Ammi ta kirashi. "Alhaji" dago kai yayi ya kalli Ammi idanunta sunyi jajir suna shirin tsiyayar da hawaye, cikin raunin zuciya Ammi tace "kayakuri Alhaji ka kwantar da zuciyan ka abi komi ahankali, Aneesa bazata iya kisa ba, nasan abinda na haifa" cikin wani irin fushi Dady yace "nine makaryaci ko, kina zaton shiri nama yarki? Okay naji shairi namata a CCTV baya shairi ko to muje kigani" ya finciki Aneesa dahar lokacin bata gani sosai yay flat din Mama Ammi tabisu da sauri su Rauda dake kuka sosai da sauran matan Dady ma suka bisu har dakin cameran, shiga dakin Dady yayi rikeda Aneesa kaman wacce tai sata sauran matan ma da Ammi ma ta shigo cikin tsananin fushi Dady yace "play d footage back officer" dan bude idanu Aneesa tayi ta kafe computer da ido, wani irin faduwa gaban Ammi keyi lokacin da sukaga Aneesa ta jefa kwayar a mug da lokacin data dagargaza daya ta zuba akan pancake dakin yadau salati Mama tace "ga irinta nan ai, aure aure yau munga ranan aure aure, ka aurosu karufa mata asiri ka kawota gidanan da ita da agolan yarta, kahada yarta da namu gashinan suke son kashemaka d'a muda muke gidan nan shekara da shekaru ko kurjewa bamu tabasa Aliyu yayi ba amma gasunan dududu satinsu nawa a gidan just sati biyu da kwana daya" tajuya ta kalli Ammi tana mata tafi a fuska tace "to Allah yatona asirin ku, Allah yatona asirin ku kinyi amfani da yarki ta kashe Aliyu an kamaku, Allah saiya sakama Aliyu, butulu kawai murders, Aliyu daya dauke ku a matsayin uwa, andaiji kunya anji kunya, wlh hukuma ce zata rabamu daku, mutumin daya miki komi yafi fitaki kanmu harda siyamiki mota ne zaki kashema da" Dady jiyayi kirjinshi na tafarfasa kan maganganun Mama dan kaman tana sosamai inda kemai ciwone, cikin fushi Dady yajijjiga Aneesa dake kuka sosai yace "me dana yamiki Aneesa zaki kasheahi tell me the truth" fashewa da kuka sosai tayi tace "Abba wlh wlh, na rantse maka da girman Allah bani bane wlh, wlh kuw......" wani irin mari Dady ya kifa mata abaki saijini cikin ihu yace "stop lying! Stop lying kifadamin gaskiya, Maman ki tasa ki kashemin Aliyu kowane?" da sauri ta girgixa kai muryanta harbaya fita da kyau tsabagen kuka tace "wlh Abba banine ba, banine ba na rantse maka da girman Allah" cikin wani irin fushi ganin yanda take karya bayan ankamata dumu dumu yasa Dady yarufe ta da duka baji bagani tun Aneesa na ihu tana kiran Ammi hartazo takasa ihu ganin yana neman sumar da ita yasa officer da yaranshi suka rikeshi, yaciro ankwa daga aljihu yakama hannun Aneesa yasamata yace "with all the evidence damuka samu a kanki malama Aneesa, you are under arrest for attempt murder of Aliyu Muhammad Ibrahim you have the right to remain silent anything you say will be used against you" yajuya ya kalli Ammi dake kallon Aneesan dako numfashi bata iyayi yace "ki gayama yarki tafadi gaskiyan duk inda tasamo wanan poison din inba hakaba gidan yari ne makomarta" yaja Aneesan kaman yanajan kare sukai hanyar fita daga dakin Ammi ta tsaya still tana ma Dady wani irin kallo, duk fita akayi daga dakin akabi su officer dan aga inda zasuyi da Aneesa yarage daga Ammi sai Dady adakin, ko kallonta Dady baiyiba azuciye yazo zaibi tagefenta yawuce takama hannunshi tarike lumshe ido Dady yayi Allah kadai yasan iyason dayake ma Ammi dan tabashin nan datayi har brain dinshi yaji, kasa juyowa yayi hakan yasa ahankali Ammi ta zagayo ta gabanshi tasan Dady nacikin tashin hankali, ya acikin matsala saisa dudda uban dukan dayama Aneesa still tamai uzuri batason ko kadan taga bakinshi, ahankali tana kallon fuskan shi tai kneeling akasa ta hade hannayenta ta danne zuciyata sosai dan bata so ta karaya she needs to be strong and fight this battle for her daughter a yanzu Aneesa batada kowa sai ita she's all alone, Murya chan kasa tace "Alhaji nasan kana cikin tsananin fushi da bacin rai amma dan girman Allah ka sauraren" tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya tadaga fuskanta ta kallai har yanzu idanunshi a lumshe kaman bayamason ganinta ne, Murya chan kasa tace "Alhaji bantabajin daidai da atom of hatred towards Aliyu ba, na rantse maka da Allah ubangijin mu, ubangijin Al arshi wanda ya busamana numfashi, ubangijin sammai bakwai, wanda ya halicce ni ya hallice ka ya hallici duwatsu da dabboni Alhaji bazan taba tunanin bama Aliyu wani abu danna halaka shi ko kokuma wani abu mai kama da hakan, haka zalika zan iya rantsemaka Aneesa ma bazata iya hakanba, am not justifying abinda Aneesa tayi bakuma kokarin kareta nakeba, but dan Allah ka yakuri, ka sauko da zuciyan ka, dan girman Allah kasaka asaki Aneesa she is too small tazata san rayuwan gidan yari kokuma rayuwan police station the trauma bazai taba barinta ba, Allah kayakuri ka janye case dinan kasa asaki Aneesa tadawo gida let's solve matsalan nan maturely, matsalan gidane let's solve it at home dan girman Allah kaji".

4️⃣8️⃣

Bude idanu Dady yayi yadaura su kan Ammi saida taji tsoron yanda idanunshi yayi ja, ahankali yace "nafada kaman bakijini da kyau ba yanzu zan kara maimaita miki kiji da kyau, duk wanda yace zai tabamin yaro to wlh sai inda karfina yakare aduniyan nan, sanan kikace bincike? Binciken uban me za'ayi bayan ke dakanki kinga lokacin da shaidaniyar yarki ta barbadama yarona poison a abinci binciken uban me zanyi eh? Listen to me and listen very well Aneesa will pay for wahalan dayarona yakeyi mercilessly, dukan danamata anan kadan ne azaban dazansa amata saita gwammace dama mutuwa tayi da wanan azaban, kema kidage da addu'a Allah tashi kafadun Aliyu idan yarona yamutu banga abinda zai hanani karna saka arataya Aneesa harta mutuba, sanan banga abinda zaisa na withdrawing case dinan ba your daughter must be charged for attempt murder of my son" yana fadin haka ya kabar da hannun Ammi dake kan guiwanshi yay gaba zai wuce da sauri Ammi tabishi tasake rike guiwanshi tasa hannu daya ta share kwallan daya zubomata zatai magana saikuma tafashe da kuka sosai at this point takasa rike kukan kawad dakai Dady yayi dan baiso taga fuskarta ahankali cikin kuka sosai Ammi tace "Alhaji kayakuri, kayafema Aneesa, banda karfin ja dakai, banda karfin jadakai wurin hukuma, Alhaji Aneesa marainiya ce, kasan kannin mahaifinta ko kudin belinta kokuma kudin tara basuda shi kayakuri, kabi abinan ahankali, Alhaji koda Aneesa ce tayi hakan naji tunda dai Aliyu da ranshi yana numfashi bazaka iya yafemata ba?" da yatsa Dady yanuna ta yace "inhar akan Aliyu ne bansan yafiya ba, koda duka duniyan nan zasu taru bazan yafema yarki ba dan ta taba abinda yafi soyuwa agareni" ya tura Ammi yawuce yafita daga dakin, fashewa da kuka sosai Ammi tayi tama kasa tashi daga wurin takai kusan minti ashirin sanan tasauko kasa Mama da kishiyoyinta duk suna zaune suna ganinta suka kece da dariya hawaye ta share tawuce tafita daga dakin hanyar Gate tayi sojoji suka tareta sukace Alhaji yabada umarni kar abari tafita daga gidan haka ta lallaba takoma daki kuka taci bana wasaba ganin kanta yafara ciwo yasa tawuce ta watso ruwa tai alwala tazo tai sallan azahar tai addu'o'i tai addu'a Allah ya kare mata Aneesa saikuma kuka takasa hakura, ganin har dare ba labarin Aneesa gashi takasa bacci bataga Dady ba danbai dawoba yasa duniya tamata zafi tadau waya takira Baffa nan ta sanar dashi abinda ke faruwa tsaf tana kuka da kyar Baffa ya lallasheta ya sanar da ita gobe suna hanya, ranan saidai bacci barawo ya saceta bata iya bacci ba.

Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa
Wuraren karfe uku su Baffa suka iso Amma anhanasu shigowa Ammi itama anhanata fita, da waya tamasu kwatancen asibitin da Dady yake, nan sukaje suka sami Dady, faram faram Dady ya karbesu yakaisu sukaga Aliyun sun firgita da condition dinshi kaman wanda ke coma nan suka bijiromai da maganan Aneesa Dady kekaxewa yayi yahau xubomjsu ruwan bala'i kan saiyaga bayan Aneesa sun tsorata dan sunga new side of Dady sukai sukai dashi to yafada musu wani police station Aneesan take yaki yace "sai danshi ya warke tukunna suji yanda yakeji" ganin kaman ba Dady yasa suka juya suka tafi nan suka kira Ammi suka sanar da ita komi Ammi kuka harta godema Allah.

Hausawa sunce abu kaman wasa wai karaman magana tazama babba, yau kimanin sati biyu kenan Ammi batasa Dady a ido ba! Batasa Aneesa a ido ba! Gashi yahana abarta tafita daga bayama sojoji uku taga sunzo gaban flat dinta sun tsaya ko nan dachan ba'a bari ta tafito tana flat dinta, sosai wani irin zazzabi da ciwo yarufe ta bata iya bacci, kullum kaima Allah kukanta take, tana addu'a yabama Aliyu lafiya sanan ya tsare mata Aneesa aduk inda take yanzu ne tasan cewa manyan kasa masu kudi masu kudine, imagine Dady yasa ankulle Aneesa bamasusan a inda aka kulleta ba, duk police station dasu Baffa zasuje dazaran sunkira sunan Dady saidai ma akore su a karshe ma komawa kaduna sukayi dan duka kudaden su yakare akan zirga zirgan dasuka dingayi a Abuja.
Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa.
Chapter 70 · 0% Book details