← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 128

Sashe 93

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Satin Aliyu uku da kwana biyar a asibiti sanan yadanji dama dama dan yaga gane mutane yawani irin yin haske bau aka sallamoshi, bata wani magana sosai Dady da Abdul saisuyita mai maganan duniyan nan da kyar zai basu amsan guda daya, sai karfin hali baida karfi ko kadan amma kome zasumai sai yace su barshi shizai iya dakansu dan fushi yake dasu sosai ahaka dai harsuka kai gida, wanka yayi da ruwan dumi a bathroom sanan yafito ya shirya cikin sport wears yasaka sport shoe na Nike yafito compound yahau kan exercise machine dinshi, baida lafiya fa amma saiyayi koya dena tunanin Aneesah, daga window falonshi Dady yahago Aliyun yafara yahau kan extention machine yanayin da sauri Dady yabude kofa yafito yana tafiya da sauri yazo wajen ya tsaya akanshi yace "lafiyan ka Gadanga, off this thing and come down, kadaisan wanan exercise dinan kan affect ur heart ko dan zai dinga racing and pumping more and more, wai mesa kakeson exercise haka?" batare daya dena abinda yakeyin ba yace "because Aneesah naso" shiru Dady yayi kafin ahankali ya matso kusada Aliyun sosai hannunshi yamika ya danna power button din machine din yakashe machine kafin ahankali yakai hannunshi yadaura kan kafadar Aliyun dake kallonshi, anatse yace "Gadanga na, zan fadama what am about to tell you now bawaidan ka shiga tashin hankali bane dan banson inga iska na wahalar dame kwasan kara ne, Aliyu na listen" Dady yay maganan muryanshi na karaya dan yasan he will hurt Aliyun more, ahankali yace "son Baffan Aneesah yacemini ansama Aneesah rana wata daya da sati biyu, as of now am talking to you bikinta baifi nan da sati biyu da yan kwanaki ba, no need to be suffering yourself doing all this kaji Aliyu na" wani irin sanyi kafafun Aliyu yayi baimasan lokacin daya zube a kasan wajen ba yazauna dabas yana wani irin numfashi kirjinshi na sama da kasa, da sauri Dady yazauna kusada shi tareda daura hannunshi kan kirjinshi yace "kai Aliyu menene haka, calm down, calm down" girgiza ma Dady kai yayi cikin wani irin rudewa yace "Dady but I love her" gyadamai kai Dady yayi yace "yes Son, I know you love her" wasu irin hawaye masu zafinne suka gangaro mai akumatu kafin da sauri ya shige jikin Dady yana numfashi sama sama, rungume shi Dady yayi shima so tight kaman zaiyi kuka yace "am so sorry Son, is all my fault, laifinane Aliyu, dukni najama my actions and deed crippled your love life, am sorry Son kayafe min kaji, I regret my actions wlh Aliyu, nai nadama nai nadama sosai, am so sorry my son" gyadama Dady kai yayi ahankali inka gansu gwanin ban tausayi kaman ba Dady senate president na mai shegen kudi da dan gaban goshinshi, ahankali Aliyu yasaki Dad yamike tsaye hannu yasa ya goge hawayen shi tareda juyawa yay flat dinshi, binshi da kallo Dady yayi yanda yake tafiya ahankali yaji kuka yazomai yadade zaune awurin kafin yatashi yawuce flat dinshi dan yasan koya shiga na Ammi koroshi zatayi dan cikin nan yasamata masifan dahar tsoron ta yakeji wani zubin, saisa ma yama kasa tunkaranta da maganan yana bukatanta dudda sha'awanta kaman zata kasheshi amma ya shanye lallabata yake yanzu.

6️⃣6️⃣

Sallama yayi tareda turo kofar falon Ammi ahankali, kallo daya Ammi tamai saida gabanta yafadi sabida yanda idanunshi sukai ja sosai tadauke kai tacigaba da karatun littafin azkar din datake karantawa, maida kofan ahankali Aliyu yayi ya shigo dakin ahankali yana tafiya har jiri jiri yake gani dan rabon shi da abinci 3days kenan, yanajin yunwan fa amma baya iyacine ko kadan, ko Dady yakawo mai abinci saidai ya zubar yacemai yaci Dady yay ta jin dadi, ahankali ya shigo falon yazo har gaban Ammi yazauna tareda lankwashe kafa kaman dalibin dayazo bayar da karatu, cikin wani irin muryan na wanda baida karfi ko kadan dinan yace "Mum yau kwanana uku da aka sallamoni a asibiti bakizo kin dubani ba, Mummy mena miki dayasa dakika tsaneni haka? Mesa bakisona? Mesa ko kallona bakison yi, Mummy tunda mahaifiyata tarasu u were the first person dana bata position din mahaifiyata, because u are everthing I want as a mother and even more, Mum Dady yacemin ansama Aneesah rana k....k....ko?" yakara she maganan muryan shi narawa sosai kaman zai fashe da kuka, dan murmushi yayi irin mai ciwon nan yace "Mummy I know you are doing duk abinda kikeyi sabida abinda Dady yama Aneesah, Mum Dady is very very sorry, yay nadaman abinda yayi, he regretted his actions, Mum nima nai fushi da Dady sosai but nahakura yanzu dan nasan yay nadama" yasake yin shiru kafin ahankali yace "rana tafarko da son Aneesah yafara shiga zuciyata shine ranan data fara taimakon Rauda a Suleja da Nazif yaso yamata fiyade, aranan nafara jin ina sonta sabida Aneesah prove to me cewa she is a helper and a woman's keeper, the day dat I fell in love with her more shine ranan da she was crying because tayi dare a inda taje lalle, I understand daga yanayin ta cewa yarinya ce that was well trained and brought up at home batasaba yin dare a gida ba, one of the major elements dayasa naso Aneesah was she is always on hijab harda safan kafa, gatada natsuwa, akan Aneesah nasan cewa hijabiya sister's are also outspoken, they know their right, and they can fight for their right, Mum inason Aneesah dayawa" dan shiru yayi yace "Mum kin tsaneni kin tsani Dad, bazaki bani auran Aneesah bako?" yasake maimaita kalman nan akaro nabiyu da saida yataba Ammi dan magana yake kaman maraya, sake gyara zaman littafin data rike a hannu tayi kaman karatun ta take danbataso yagane komi, ahankali ya sauke ajiyan zuciyan daya sauka akan kafafun ta tajishi zafi sosai, murya chan kasa yace "shikenan, nahakura Mum, kowani hukunci kika yanke na dauka, Ke mahaifiyata ce inkin tsaneni is okay, inkin bani abu is okay, hakama inkin hanani is okay, Allah yabasu zaman lafiya dama abinda nazo nafada miki kenan" yasa hannu yadafa hannun kujeran sabida jirin dayake gani yamike tsaye, sanan yaja kafa ahankali yajuya yacigaba da tafiya yana expecting Ammi ta kirashi, ahankali Ammi ta janye littafin daga fuskarta tasa hannu.

Ahankali ta sharo hawayen daya taru a idanunta ya mugun bata tausayi bana wasaba har kasan zuciyanta tanason Aliyu but she can not do anything bikin da duka duka saura sati kadan ne mezatayi.

_Agurguje_
Chapter 93 · 0% Book details