← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 128

Sashe 11

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ganin yanda Aliyu ya mareshi da farko ya shiga yarfe hannu zaka gane baida karfi kona sisi, kallon yanda Rauda ke kuka sosai abayanshi take alamun batada hope zai musu dukan tsiya sanan yama yayan nata dukan tsiya shima hakan yasa taji wani karfi yazo mata da bata taba jin irin that kind boldness ba in her life, cikin wani irin izza ta shiga gaban Aliyu tana taku dai dai tana clapping hands dinta cikin isa da takama tana clapping din tana kallon fuskan Khamis din dake kallonta kaman yanzu yafara ganinta, tsayar da tafin tayi tace "kasan mesa nake tafa maka?" tai wani murmushi ganin baice komiba kawai kallonta yake kaman wani wawa tace "wani zubin idan kare na haushi idan kai tafi saikaga yadan natsu" cikin fada yace "nikike cema kare?" cikin dakewa ta nunamai yatsa tace "quit, am still talking" samun kanshi yayi dayin gum ganin yar yarinya namai magana kaman uwarshi, tace "what differentiate human being da animals is ability to think and reason which bakada duka biyun you are just a dog malam which yayan mu bazai taba iya biyema yadawo kaman kaiba ko?" tadan juyo for the first time ta kalleshi idanunshi da nata suka sarke faduwa sosai gabanta yayi tadan kyafkyafta ido sau biyu pink lips dinta sukadanyi rawa ahankali tace "ko?" gyadamata kai Aliyu yayi batare dayasan yamayi ba, juyar da kanta tayi tace "kai mailafine bagaremu ba kadai har agun Allah, sanan kanada bakin zage zage kana turashi kanaso yabiye maka kuyi fada, wai intambayeka man do you know who is a Man?" wani matsiyacin kallo tamai ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace "A Man baya tsayawa yay physical fight da kowa dan physical fight dangrades one's level, banda haka a Man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin tsananin fushi which is abinda yayi yanzu, kazaci kana ihu kana cika kana batsewa kana tunanin by d time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?" tamai tambayan tana hura hanci daya kaman wata boss tana kallonshi, dan murmushi Aliyu yasaki for the first time ya rungume hannayenshi a kirji, ganin har lokacin Khamis din baice komiba ya tsaya yana mamakin tane yasa tace "and yanzun nan zan nunamaka idan yatashi yace zai ci uban naka u can never match his level of power, kwabaka zaiyi kaman yanda ake kwaba dibila tsaya kagani" tai maganan tana tsugunna wa a wurin duk suka bita da kallo kasan dake bakin Gate din ta kwasa da hannunta dayawa batare da duksun luraba dan hijabinta yarufe mata hannu sundaiga ta tsugunna mikewa tsaye tayi Khamis din nabinta da kallo hannunta tadaga un expectedly ta watsamai kasan a fuska aiko suka shiga idanunshi biyu, ihu yayi. "wayyo Allah na, wash Allah idanuna, sainaci durun uwarki yarinyar nan" yayo kanta yana sosa idanunshi dayakasa budesu tsabagen kasan data sakamai a ciki matsawa gefe tayi da gudu ta kalli Ya Aliyu dake binta da kallo tace "Yayan mu yimai shegen duka ramama kanwarka abinda yamata bazai iya ramawa ba idanunshi cike suke da kasa" ware manyan idanunshi Aliyu yayi yana kallon this wired girl, gyadamai kai tayi da sauri tace "ka zaneshi, daddaki azzalumin" jin daga ta inda take magana yasa Khamis yay wurin yana murza ido yace "dan uwarki ubanwa yace miki koni makahone zai iya tabani ne wanan ragon" dawowa tayi kusada Aliyun ta kallai tace "yimai lilis u can do it, zo zan nuna maka inda zaka dinga duka ajikinshi zokaga" tai gaban Khamis din dake bubbude kafa yana sosa idanu kaman mahaukaci tsabagen azaban kasan dake cikin idon, ta nunama Aliyu cikin shi daya fara dan tara teba dama babu riga ajikinshi tace "zoka naushi nan" turashi Rauda tayi tace "muci ubanshi Ya Aliyu ka rama mana" ahankali Aliyu yadaga kafa yana kallon Aneesa dake nunamai cikin Khamis kaman wawa yakaraso kusada inda take yana kallonta still, zare ido tayi tsabagen jin dadi zasuci ubanshi tarage murya kaman mai shirin gulma tace "yauwa naushi nan". Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace "it's hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt" sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace "gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan" tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace "zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80" da sauri ya kalleta yace "80?" kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. "Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na..." zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace "ina zuwa bari kuga" da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace "Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga" kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace "yauwa rikemin hanunshi tabaya" tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace "wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc...." bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace "dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya" takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace "am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude" ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace "baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to" juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace "sunana Nana Fateema" "can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?" Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace "bye Friend" daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin
Chapter 11 · 0% Book details