← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 128

Sashe 78

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Number Baffa Ammi ta nemo ta kira, ringing daya ya dauka, ahankali Ammi tace "barka da warhaka Baffa" "barkan mu dai Maman Aneesa" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali tace "Baffa ansaki Aneesa yau tana hanyar zuwa kaduna, zan turama number mutumin daya dauketa, Baffa ka kulamin da Aneesah, Baffa Aneesa need strick care gidan yari Alhaji yaturata, zadaika ganta dakanka, Baffa rayuwata nacikin kunc....." takasa magana sabida yanda kuka yaci karfinta, haushin ta sosai Baffa yakeji amma ayanda Ammi ke kuka sai jikinshi yamai sanyi yasan koshi baikai Ammi jin bakinciki faruwan komiba, murya chan kasa cikeda lallashi yace "kinga, kinga Maman Aneesa, calm down komi yay tsanani maganin shi Allah, wanan jarabawa ce da yardan ubangiji kuma zamuci, dan haka kiyihakuri, kuma karkiji komi akan Aneesa Allah yakawo ta lafiya koma me tadawo yarmuce ahaka zamu rungume ta da hannu bibbiyu sanan we will shape her to our like, addu'a kawai zakiyi tamata kinajina, kul karna karaji kinyi kuka kan zancen nan tunda ansakota Alhamdulillah, duk wata matsala da sauki ce da yardan Lillahi, share hawayenki" ahankali Ammi tasa hannu ta share hawayen tass ta sauke ajiyan zuciya, murya chan kasa tace "Baffa sai magana ta biyu" da sauri Baffa yace "oho ina jinki" ajiyan zuciya tasake saukewa tace "Baffa alfarma nakeso, inaso ka saidamin da shanayen Aneesa guda biyu so nake kabani dubu dari sauran kudin inaso kayi amfani dasu ka shigarmin da kara kotun musulunci anan kaduna, inaso araba aurena da Alhaji, dubu darin zan biyashi kudin sadakinshi dasu" shiru Baffa yayi tunda tafara maganan harta gama saida tace "kanajina Baffa" da sauri yace "inajinki" anatse yakira sunanta. "Rukayya" yanda yakira sunanta kai tsaye yasa Ammi tagane he's so serious dan he hardly call her name direct. Anatse Baffa yafara magana. "Rukayya na isa dake, sanan inada iko dake, kinada wani irin matsayi na yar uwata najini dabazan iya tsayawa ina ganin zakiyi shireba na barki, nasan kin tsani Alhaji sabida abinda yama Aneesa, bari kiji wata magana aduk lamarin nan laifin Alhaji guda nake gani, shine dabai tsaya yasaurare muba, kisaka kanki atakalmin shi, daga ke har Alhaji kunyi boko, yan boko kuma mutanene dasun yarda da technology, babu yanda za'ayi mutum kaman Alhaji yaga camera yakama abu haka bayan ya kalla kuma yace bahaka bane, tunda har yagani da idanunshi ga Aneesa nasaka poison bazai taba yarda ba itabace dole kuma ya hukunta ta, kar abin nan yasa kice zaki nemi saki, babu kyau saki, kin riga kinsa Aneesa tadawo wajena hakan dakikayi kin kyauta tabarmai gidanshi, Ke kiyi zamanki kicigaba da rayuwan aurenki, ki rubuta ki ijiye nina fadamiki wata rana Alhaji saiyazo yasa guiwanshi akasa yabaki hakuri, gaskiya bata boyuwa fa da dadewa, komujima komu dada gaskiya zata bayyana, Allah zai warwaremuku komi, zai wanke Aneesa dake, bama ke kadaiba, Alhaji harnan kaduna saiyazo ya roki Aneesa gafara, nidake bamusan gaskiyaba Allah zai bayyana mana gaskiya, kiyi hakuri bazan taba baki goyan bayan ki kashe auren nan kifito ba, amma kiyakuri dan ke wacce aka cutace, Allah zai bimiki hakkin ki kowaye awanan lamarin sai Allah yatona musu asiri dai dai, daya bayan daya namiki alkawari, Aneesa kiyita mata addu'a, kimata fatan samin miji nagari na aurar da ita muhuta kinji Rukayya kiyahakuri" hawaye Ammi ta share bataso tama Baffa gardama hakan yasa tace "shikenan Baffa nagode" "yauwa, Allah yamiki albarka, kituramin number kinji" to.
:*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

5️⃣4️⃣

_07012181461 chat me up in kinason wanan book din_

.........
Dady yakai almost 20min awurin a tsaye yana mamakin what just happen yanzunan tsakanin shida Aliyu, inda yabari Aliyu ya kona kanshi da yaya zaiyi? Da ina zaisa ranshi, dagokai yayi ahankali ya kalli ma'aikatan wajen cikeda sanyi jiki yace "agyara wajen nan dan petir nada hatsari sosai" sanan yawuce yana tafiya ahankali ahankali duk jikinshi yay sanyi sosai yana kallon yanda matayenshi ke tashi daga window dasuke leke suna komawa ciki yadauke kai yawuce shashin shi yafada kan kujera.

Agurguje Aliyu yay wanka kusan sabi uku sabida yadena warin petir din sanan yafito, agurguje yake shirya wa dan baiso yabata lokaci, 3quater na gucci yasaka da wata dark brown paco robbani logo print shirt daya haska fatar shi yafito da kyanshi, fesa turare yayi yasa takalmin shi na prada sanan yadau car key dinshi yana dingishi yafito yay flat din Dady babu alamun wasa akan fuskanshi, ahankali yatura kofan dakin da sauri Dady dake kishingide kan kujera yatashi yazauna da kyau yana kallon Aliyun kaman yau yafara ganinshi, har gabanshi Aliyu yakaraso ba yabo ba fallasa yace "Wani prison ka kaita Dad?" yadanyi shiru yana kallon Dady kafin ahankali yace "zanje nadauko tane" sosai Dady ke mamakin shi dansai yanzu yakara ganin son Aneesan akwance kan fuskar Aliyun, ahankali Dady yanisa yana kallon fuskanshi dasaiyau ya yarda da maganan manya cewa abinda kafiso shiyafi baka matsala banda haka ace duk wanan abin dayake ma Aliyu bayagani, yazaci in Aliyu ya warke yaji meyayi he will be proud of him yarungumeshi yace I love you Dad, you are the best saidai yaga akasin hakan, sabida shine fa ya kulle Aneesa amma duk bayagani, yarinyar dataso aikashi lahira saima haushin shi dayake ji, ahankali yace "Zilanious prison take" dago idanu Aliyu yayi ya kallai irin kallon nan na Dady zaka iya aikata haka kafin ahankali yajuya kawai yafita daga flat din Dady na binshi da kallo yawuce yafita abinshi batare daya waigoba koya juyoba.

Yayi tafiyan almost 30min sanan yakai prison din shima da taimakon Google map, parking yayi yafito yana zare bakin glases din idanunshi kafin ya shiga ciki hargaban kanta inda wata guard take ga katon book din rubuta name of visitors a gabanta, tun kafin Aliyu yakaraso inda take take wani irin jarababben kallonshi wani irin dan gayune yau haka yazo prison dinsu, turaren shi daya fara mata sallama yasa tadawo daga yar gajeran tunanin datake, tace "Well done Sir, barka da zuwa yallabai, wakazo gani?" girgiza mata hannu yayi alamun he's not here to visit anyone, cikin kwantacciyar muryanshi yace "am here to pick up someone da akai releasing" da sauri tace "what's her name sir?" "Aneesah is her name" zaro ido tayi ta kallai tace "Aneesah barkono? Ai indai itane ansallame ta tun dazu about 30-38min ago ma kam" dukan wajen yayi cikeda cinrai zaijuya yawuce tace "Sir excuse?" dan juyowa yayi ya kalleta, murmushi tayi tace "don't be offended zan dan yimaka personal tambaya ne" gira daya yadaga mata batare dayay magana ba alamun go on am all ear, murmushi tayi tace "Sir you are so cute wlh, please wats your relationship da Aneesah" dan tabe baki yayi ganin tambayan gulma ce yace "am her husband to be, and Aneesah is Cutie than I" da sauri tace "no way wlh, kai kaga kyan ka kuwa gaka fari kaman jinin bature, kafita kyau" ahankali yace "I will take that as a compliment, as 4 me tunda nake I've never set an eye on a lady that is as beauty as Aneesah ba in my life, she is the definition of Queen of heart, excuse me" yajuya yafice daga wurin da saurinshi ya shige mota yana duba agogon wayanshi maybe hala to takai gidama, dawani irin sauri yaja motar baida burin daya wuce yadaura idanunshi akanta and apologise to her on his father's behalf.

Ahankali sallan la'asar takama shi ya tsaya yayi sanan yakoma mota gabanshi na faduwa yakosa yaga Aneesan, parking yayi a compound dinsu ysauko daga motan yana dingisawa yay flat din Ammi, sallama yayi tareda bude kofan falon, Ammi ce kadai zaune kan kujera sai bowl dake dauke da sliced fruit masu sanyi da fork ta tasa agaba tana kallo takasa ci tadago kai tana kallon Aliyun, da sauri Aliyu yamaida kofan yarufe yakaraso gabanta tareda tsugunnawa yadafa hannun kujeran yace "Mum am just coming back from the prison ance tuntuni aka sallamota inkika fitarmin da novel waje Allah ya isa ban yafemikiba
Chapter 78 · 0% Book details