← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 128

Sashe 20

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ba karamin faduwa gabanta yayiba jin kalaman dasuka fito daga bakinshi, rawa lips dinta yafara tanadan zaro idanu zatai magana yamika hanunshi ya karbi wayanta dake kan hanunta ya bude ganin ba key, danne danne ya shiga yi kafin ahankali yamika mata wayan yace "take" hanunta tamiko ta karbi wayan da sauri tajuya tai cikin gida tarufo kofa, hakanan yaji ko kadan baiji dadi data tafiba kaman yabita, komawa cikin mota yayi yabude ya shiga, kifa kanshi yayi akan starring mota ya fuzar da iska he seriously don't know what's wrong with him, tun daga fitowan Aneesa daga gidan bikin tareda Nihal idanunshi suka sauka akanta lokacin yana tareda Abdul a cikin mota, Abdul yacemai sutafi yace yaje shizai shigo anjima, haka ya dinga kallonta ta mota har lokacin databi motan su Lado da gudu da lokacin data shige lungun mota da lokacin data fara kuka tana waya, shidai baisan mesa ba he just love natsuwar yarinyar, yanda take tafiya a natse, da yanda take magana a natse, da yanda muryanta ke fita so gently and innocently bala'in burgeshi yake, boldness din yarinyar use to melt his heart, bai taba ganin yarinya dat match his taste like her ba, hakanan yaji he just wanna be her friend, a girl like her is worth associating himself with, wayarshi dayay kara yasa ya kalli wayan ganin Dad ne yasa ya ijiye wayan yasan fada Dady zai fara baifito da bodyguard dinshiba, tada motar yayi yaja yana lumlunshe ido he's so tired dan driving dinan dayayi, and he's so sleepy Allah dai yakaishi gida lpy kawai.
Dakinsu ta shiga da sauri Ammi tace "meya daddar dake haka?" rasa abinda zatace ma Ammi tayi hakan yasa ta shiga kame kame kafin tace "uhmm Maman Muhammad ne ta shiga wanka saida najirata tafito fa Ammi" tai maganan tana hawa kan kujera dayake tanada tsawo tana hawa takai ta makala kwan lantarkin aiko wuta yakawo sanan ta sauko, dakinta tayi tacire kaya tadauro zani tafito, tsakar gida tawuce tadau bucket tajuye ruwan zafin da Ammi tadaura ta shiga bayi tayo wanka tareda dauro alwala fitowa tayi tawuce ta shige dakinta wani dogon rigan atampa tasaka sanan tadau hijabi tafito Ammi dake binta da kallo tace "bakiyi salla ba?" gyadamata kai tayi tana hawa kan dadduma tace "banyiba" magrib da isha tayi bayan ta idar tai shafa'i da wuturi, sanan ta cire hijabin tana sauke ajiyan zuciya ta kwanta akasa tana mikama Ammi kafafunta a shagwabe tace "wash Ammi kafana ciwo" murmushi Ammi tayi ta karbi kafafun ta daura kan cinyanta tace "raguwa kawai" matse kafafun nata ta shiga yi hakan yasa ta lumshe idanu wani mugun bacci na neman dibanta, kafeta da idanu Ammi tayi tana kara godema Allah daya bata yarinya mai natsuwa ga hankali, Aneesa is just a gift to her life duk rashin jinta inhar tace tak to ta natsu, she just pray Allah yabata miji nagari dazai kula da ita yabata all that she deserves, karasa matse kafafun tayi sanan tadan bubbugata ganin tai bacci. "Aneesa, Aneesa, tashi kije ki kwanta" bude idanu tayi dake cikeda bacci ta kalli Ammi, Ammi tace "tashi kije ki kwanta sannu yau mata sun aikatu" murmushi tayi ta mike tsaye tana tafiya ahankali tawuce, wayarta tadauka dake kan kujera ta wuce dakinta kwanciya tayi kan gado bayan tai bismillah sanan tai addu'an bacci wani bacci mai dadi yau awon gaba da ita.

_"why, why Aneesa? I trusted you, mena miki da zaki kasheni eh? I trusted you Aneesa, you are my friend, we are friends remember? I love you Aneesa, why, why, why, why, dama kin tsaneni, dama so kike ki kasheni, why Aneesa?!" yadaka mata wani irin tsawa da duka karfinshi daya rage kumfa na fita daga bakinshi, idanunshi sunyi jajir yana kakarin mutuwa hawaye na bulbulowa ta gefen idanun._ afirgice ta farka daga baccin daya kwsheta tana wani irin zufa komi na mafarkin datayi na dawo mata fresh, mutumin dazu tagani kumfa na fitowa daga bakinshi yana kakarin mutuwa yana mata all this maganganun itakuma tana gefenshi idanunta sunyi jajir sai kuka take ga ankwa a hanunta, batasan mesaba fashewa tayi da kuka sosai tana girgizakai, karan wayarta daya cika dakin yasa ta mugun firgita, da sauri tasa hannu ta goge hawayen daya bata mata fuska tamika hannu tadau wayarta dake gefen filon ta kalli screen din. "Aliyu" taga yana kira, faduwa gabanta yasake tazaro ido ta kalli time a jikin wayan 12:25Am.

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

1️⃣6️⃣
Chapter 20 · 0% Book details