← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 128

Sashe 19

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gudu yake sosai basu wani jimaba ya kai Sulejan sanan yarage gudu yadan kalleta cikin calm voice dinshi yace "show me the road to your house" gyadakai kai tayi tasa hannu tana nunamai hanyar yanata bi har sukakai anguwan su, a kofar gidansu ta hango Ammin su tsaye sanye da dogon hijabin ta hanunta rikeda waya, da hannu tamai pointing Ammi tace "ga Ammi na nan" rage gudu yayi tareda rage karfin wutan gaban motan sabida karya haska Ammin sosai tun kafin yay parking tawani irin bude motar da gudu tai wajen Ammi data tsare motar da kallo. "Ammi, Ammi, Ammi" kafin Ammi tace ma wani abu taje da gudun gaske tai tsalle ta rungume Ammin kaman wacce tai shekara bataga Ammin nataba, rungumeta tight Ammi tayi tanama Allah godiya. "Alhamdulillah" kafin ta dagota daga jikinta takama habarta da hannu daya tasa dayan hanunta tana share mata fuska tace "Alhamdulillah Allah nagode maka, you are ok ko Aneesa na?" hannun Ammi ta rike tareda gyada matakai tana murmushi hakan yasa Ammi tasake sata ajikinta ta rungumeta, shiru yayi ya tsaya a mota yana kallonsu, looking at affection din Ammi towards Aneesa yasa yaji he just wish Mummy shi was alife to hug him like this, he miss his mum so so sooo much, lumshe ido yayi ahankali zuciyanshi namai wani irin zafi.

Ahankali yajinginar da kanshi da kujera kirjinshi namai wani irin zafi, knocking glass din motar da akayi yasa yabude ido ahankali, Ammi yagani tsaye rungume da Aneesa a gefenta, ahankali ya bude kofar shibai masan mezaiyi ba yadai sami kanshi da kasa daga fuskarshi ya kalleta zaiyi magana Ammi tarigashi. "nagode, nagode bawan Allah, yanda ka taimaki Aneesa Allah ya taimaka maka adukkan al'amuranka, Allah ya haskaka rayuwan ka, kakawo mini ita har gida safe and sound, thank you so much, may Allah reward you abundantly" kasa ma magana yayi sai gyadamata kai da yayi ahankali, ganin haka yasa Ammi tadan bugi kafadar Aneesa da kanta ke kasa tace "bakimai godiya ba Aneesa" ahankali tajuyar da kanta ta kallai har lokacin kanshi akasa dauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan yatsunta data shiga wasa dasu ahankali tace "nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi" murmushi Ammi tayi tace "mun gode malam saida safe, wuce mutafi Aneesa" jan hanun Aneesan tayi tasa key tabude kofar gidansu dahar ta kulle ta shiga, dan waigawa Aneesa tayi tasake kallon motar dudda bata iya ganinshi daga wurin amma saida gabanta yafadi da sauri ta shige ta maida kofar tarufe, sukai cikin gida, falo suka shiga ta ijiye souvenir da akabata akasa ta zauna kusada Ammi tana bude jakanta tace "Ammi barina saka chaji tunda akwai wuta, yautun safe bansama wayata chaji ba" ciro wayar tayi daga jaka tana kokarin kunna wayar kwan lantarkin falon yawani irin yin kara ya tarwatse da gudu tarike Ammi sabida tsoron dataji, salati Ammi tayi. "innalillahi tome kuma yasami kwan lantarkin ko karfin wutan yay yawane?" tai maganan tana kunna wutar toculan wayanta ta haska wajen wutan taga yanda yafashe, tsaki Aneesa tayi tace "Ammi dama wanan na dan dari uku baida kyau energy bulb yafi wanan yan darin dakike siyowa kyau, anmafa ce baya jan wutafa, bari naje nasiyo" tai maganan tana zage handbag dinta ta kwaso duka kudin da aka bata ta mikama Ammi tareda zare dubu daya ta mike tsaye tareda daukan hijabinta, Ammi dakebin kudin da kallo tace "wayabaki kudi dayawa haka Aneesa?" dan dariya tayi tace "amaryan tabani wai kudin lallena bari nadawo nabaki labarin abinda ya faru yau" dubu biyu Ammi tazaro cikin kudin tamika mata tace "gashi ki shiga gidan Maman su Muhammadu kice nace gashi injini" karba tayi tace "to" tawuce tafita daga dakin tana haskawa da wayanta dan tsakar gidansu dama babu fitila, bude kofar gidansu tayi tafita tana haska kudin hanunta da waya tacire dubu biyun tarike su separate sanan ta shiga gidan dat is next to them inda Ammi ta aiketa ta mika kudin tafito tana kalle kalle, idanunta ne suka sauka akan motan daya kawota ganin har yanzu motan na wurin baitafi ba, faduwa da gabanta yayi yasa tasauke kai da sauri ta dena kallon motar, tsallakawa tayi dayan side din tai wajen wani shago dayake chan gaba kadan, ta shiga tasayo kwan lantarkin mai kyau nadan dari biyar sanan tajuyo tanadan satan kallon motan tana tafiya towards there house, sosai mamaki yakamata ganin har lokacin motan na wurin tai hanyar kofar gidansu tana kallon motar, hannu tasa zata bude kofar gidansu saikuma ta janye hannun tasake juyowa ta kalli motan to kodai baida lafiya ne? Mutumin da tun dazu yakawo ta aiya kamata ace yatafi by now, in fact yamayi nisa ahanya, kasa hakura tayi ji kaman wani abu na fizganta tafara tafiya so take kawai taduba shi taga ko lafiya, ahankali take tafiya tana kallon motar kafin takarasa gaban motan taga yabude kofan motar hakan yasa ta tsaya chak takasa karasawa tadan kwantar da kanta tana lekawa, ahankali yasa kafarshi yafito daga motar yamaida kofar motar yarufe tareda jingina da motar ya rungume hannayenshi a kirji yana kallonta, faduwa gabanta yayi sosai sabida yanda idanunsu suka hadu da sauri tajuya zata koma ya kira sunanta for the first time. "Aneesah!" tsayawa tayi chak jin yanda yakira sunanta har ranta taji kiran sunan saida duka organs din jikinta suka amsa, murya chan kasa ta yanda ita kadai ne zata ijiyajin meyace calmly yace "come" sosai takejin maganan shi nazuwanma zuciyanta kaman command, kasa jurewa tayi tajuyo ahankali taa kallai, gyada mata kai yayi tareda dan lumshe ido sanan yabude su yadaura akanta, daga kafa tayi ahankali tataho wajen kanta akasa ta tsaya agefen shi kafafun ta nadan rawa sabida wani sanyi dasuke mata da batasan nameba, juyowa yayi yay facing dinta yana kallon yanda take wasa da kwalin kwan fitilan hanunta, murya chan kasa yace "ina kikaje?" batare data kalleshi ba kanta akasa tace "kwan lantarki naje nasayo" shiru yadan yi kafin ahankali yace "maisa baki aiki brother kiba yaje kika fito da dadaddare?" kanta akasa tace "uhm banda brother" "ke kadaine?" yatambaye ta immediately bayan tai maganan, gyadamai kai tayi batare datai magana ba, ahankali yace "what about your Dad?" dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta maida kanta kasa, ahankali cikin wani irin siriruwar murya tace "yarasu" sosai kalman yarasun yadaki zuciyan shi hakan yasa yay shiru yana kallonta sai chan yace "sorry! Allah ya jikanshi" gyadamai kai tayi kaman zatai kuka dan sosai tuna mata da Baba, ahankali tace "Ameen" sukadanyi shiru batare dawani daga cikinsu yakara cewa wani abuba, dan dago kanta tayi ta kallai ganin ita yake kallo har lokacin yasa tace "in tafi?" girgixa mata kai yayi yace "No" tsayawa tayi duk tanajin wani iri yanda ta tsaya dashi danko kadan bata saba tsayawa da samari ba ita bamata dawani saurayin kirki dan batabasu lokaci. "me kikaje yi agidan bikin nan?" hanunta ta shiga wasa dashi kanta akasa tace "lalle naje yi musu" "lalle? You mean henna? Are you a henna designer?" gyadamai kai tayi tace "eh, na iya" dan murmushi yayi yarinyar nan bala'in burgeshi take bana wasaba, shidai in his life this is the first girl daya taba gani dayaji ta burgeshi, dago kai tayi ahankali kaman wacce take tsoron ta kalleshi tadan kalleshi tace "ya kanwar ka?" dan shiru yayi kafin yadan juyar da idanunshi cikin jin dadi yace "oh Rauda? Dama kin ganeni?" gyadamai kai tayi da sauri tace "eh tundazu ai naganeka, kunyi kama ai da ita saida kafita uhmm...uhmm" muryan ta ya sarke sotake tace yafita kyau amma takasa fadi hakanan taji tanajin kunyan tace mai haka, murmushi yayi sosai ganin takasa fadin abinda takeso tace mai, murya chan kasa cikeda zolaya yace "ashe kin iya kuka haka I tot mara tsoro bata kuka eh Fearless lady?" rufe fuskarta tayi da hijabi da sauri tareda yin murmushi akunyace tai gaba zata wuce dan maganan ta ya mugun bata kunya da sauri yace "wait" tsayawa tayi chak batare data juyowa ba sai murmushi take ya mugun bata kunya, cikeda murmushi tace "wat? kaga Ammi na zata zo tanemeni yanzu nan" tafiya daidai yake hanunshi zube cikin aljihu harya tako ya tsaya abayanta chak, yanda tajishi abayanta yasa taji numfashinta na neman daukewa da sauri tajuyo sukai facing juna yanda taga yana kallonta yasa taji takasa magana sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri heart dinta is beating way too fast kuma batasan mesaba sai kyafkyafta ido take, one step yakara ya matso gab da ita ahankali yace "can we be friends Aneesah?"
Chapter 19 · 0% Book details