← Book details In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 128

Sashe 8

In Between The Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Around 8:40Am Hajar tabude dakin nasu ta shigo tana kallon Raudan dake kwance kan gadonta idanunta sunyi suntum suntum tace "kije Mama na kiranki adakinta, Khamis kuma yazo yana falo" ko alamun tashi batayi ba hakan yasa Hajar tamata ihu. "wai bazaki tashi kije kiran da mama ke mikiba mara kunya" tashi tayi ahankali tana turo baki tafita daga dakin, dakin Maman su ta shiga, Mama na zaune kan katafaren gadonta ta mimmike kafafun tana shan farfesun kaza, watsa mata harara tayi tace "sai yanzu kikaga daman zuwa rasakunyar beran tanka" ahankali tace "ina kwana Mama" hararanta Mama tasake yi tace "daban kwana ba zaki ganni anan ne?" matsar da farfesun tayi gefe ta sauko daga gadon, gaban wardrobe dinta tayi tabude taciro wani sabon dinkakken atampa na mustard da brown anyi dinkin riga da skirt sai mustard veil da mustard flat shoe mai kyau, mika mata Mama tayi cikin daure fuska tace "ai tun asuba kikai wanka, gasunan shirya anan yanzu nan Hajar zatazo tamiki kwalliya kitafi yana falo" karban kayan tayi ahankali ranta abace ta cire rigan ta ta shiga sakawa ahankali, rigan ta tsaya tana kallo yanda net ne daga ta kirjin ana hango boobs dinta, hannu tasa a wurin ta dago kai ta kalli Mama da itama ita take kallo cikeda masifa tace "miye to?" cikin dan shakakkiyar muryanta tace "ana hango kirjina Mama is net" harara Mama ta watsa mata tace "naga dai Khamis zaki aura har ubanki yasan da zancen, banda haka Khamis dandan Yayata ne na yarda da tarbiyan shi, yaro mai natsuwa da hankali ga kunya, me kike nufi mai zaimiki? Besides wanan dinkin mai net din wuyan ai shinaga yan mata ke yayi yanzu saisa na bada amiki irin shi dan haka karki kara cemin komi" daidai lokacin Hajar tabude kofar dakin ta shigo dauke da kayan kwalliya murmushi sosai Mama tayi tace "kaga yar albarka maijin maganan uwarta, bazaki taba ganin mara dadi ba arayuwanki Hajar saidai kiga daidai, yimata kwalliyan sutafi sai dare yau" murmushi Hajar tayi jin ddin maganan maman su, taja kujera ta zaunar da Raudan data dawo kaman gunki ta shiga mata makeup din, cikin 5min tagama mata sosai tai kyau, tadau gyalen ta yafa mata a kafada tace "tashi kuje" kallon gyalen tayi kaman zatai kuka tace "ahaka Anty, jibi kirjina fa" mugun kallo Mama ta watsa mata tace "barganin kinyi gayu bazai hana na lallasaki da safen nan ba, dan ubanki inya gani aike zai aura ballema Khamis baida kallon nan, wuce muje" ta tasata agaba sukai falo kanta akasa, wani kyakyawan farin guy ne zaune akan daya daga kujerun dake jere a hadadden falon yana sanye da farin shadda dake kyalli taji guga da bugu, ganin Mama yasa ya saukar da kanshi kasa cikeda kunya yana murmushi, dan dariya Mama tayi tace "kagamun dan banzan yaro ni ake kunya kuma yanzu Khimis, lallai duniya ashedai da gaske ne yaro akace za'amai aure natsuwa yake" tai murmushi tace "kaga ga kanwar taka nan tashi kutafi, dan Allah Khamis sai dare kaji zaku dawo ka kaita yawon bude ido, nariga nafadama Babanta zaka kaita wujen Yaya ne, so ba matsala, sai darefa karka manta banso taje wajen shegen Aliyun nan ne, neman hanyar rabata dashi nake ido rufe, tashi kuje adawo lpy, akwai kudi hanunka enough kona kara maka?" tashi yayi yace "akwai Small Mum" gyadakai tayi tace "yauwa saikun dawo to" ta tura kan Raudan dake tsaye gefenta tace "kutafi sai anjiman ku" bude kofa yayi ya fita tabishi ahankali, rakasu Mama tayi har bakin kofa tana murmushi harda sauke ajiyan, tasamu inda ta tura mai taurin kan, taga ta inda Aliyun zai ganta yau, maida kofa tayi tarufe takoma daki. Tafiya suke a tsakar gidansu da babu kowa sai ma'aikata dake watering plant, Khamis na gaba ita tana baya tana waige ganin Mama takoma daki yasa tajuyo tace "Ya Khamis kaje mota bari nazo" kallon so yamata zaiyi magana tace "please kaji wlh yanzun nan zanzo" gyada mata kai yayi yace "okay" yay gaba, sake kallon dakinsu tayi ganin kofar a kulle yasa ta kwasa da gudu tai shashin Ya Aliyu kafin akamata, bude kofan tayi ta shiga da gudu ta mayar tarufe ganin baya palor yasa tai hanyar bedroom dinshi, knocking kofar tayi ahankali cikin tattausan muryanshi yace "come in" bude kofan tayi ta shiga yana zaune kan gadonshi sanye da white bathrobe yasaka white bathroom slippers rikeda wayarshi yana daddannawa ga cream dinshi agefenshi daya ajiye, murmushi tayi takarasa kusadashi da sauri ta zauna tace "good morning Ya Aliyu" ajiye wayan hanunshi yayi a gefe yadago kai ya kalleta zai amsa sai yay shiru yana kallon fuskarta, dauke kai tayi da sauri dan tasan yanzun nan zai gane tai kuka, hanun yasa yadago fuskarta, Kallonta yayi ahankali yace "wat made u cry?" juyar da kanta tayi da sauri ta mike tsaye tace "dazu ne dazanyi alwalan safe wani kwaro ya shigan min ido, nazo nafadama zan fita ne Yayan mu" kallo yabita dashi ko kadan bai yarda da maganan ta ba yasan dukanta akayi dan tazo wajenshi jiya amma saiya share, ahankali yace "where are you going?" shiru tayi tana dan zaro ido bataso tamishi karya kuma kunya takeji tacemai itada dandan yayar Mama zasu fita. "where are you going?" yasake jefomata tambayan akaro nabiyu kanta tadan sosa tace "uhmm Mama ta aikeni gidan yarta Anty Hauwa ne" dan yatsine fuska yayi yanuna kayan datasaka da yatsa yace "like this?" gyadamai kai tayi tace "Mama tace dole saina sasu" tashi yayi daga kan gadon yamike tsaye, gyalen dake kan kafadarta yaja ya warware gyalen ahankali ya yafamata ya lullube tundaga wuyanta har zuwa cikinta yace "leave the veil like this, cover yourself, your clothes are too expose, be safe okay" gyadamai kai tayi ahankali, sai alokacin yadan sakin mata murmushi yace "saikin dawo nima am going out yanzun nan, take care Angel" murmushi tayi yaja hancinta yace "now go" juyawa tayi da gudu tafita shikuma yacigaba da shiryawa so yake yaje gidan kanwar Dad Momman Suleja. Tunda tafito ya tsareta da ido harta karaso wajen motan tabude ta zauna tada motar yayi yay horn sojan yabude musu gate suka fita sukadau hanya saida yay dan nisa yana tuki sanan ya kalleta yace "mesa kika chanza yanayin gyalenki?" kallonshi tayi cikeda murmushi tace "yayan mu yace nasa ahaka yafi" tabe baki yayi ya maida hankalin shi kan tukinshi yace "ayanda yake da yafi kyau, kin wani lullube ko ina saikace matar aure, nidai gaskiya kicire baby" kin cirewa tayi ta kalli hanya tace "wai ina zamuje?" lashe lips dinshi yayi yace "Mama tace nakaiki yawon bude ido so zamuje yawone muci soyayyan mu ko yar kanwa ta" dan murmushi tayi batare datai magana ba, suna shiri sosai da Khamis wanda yake cousin dinta bata taba sanin su Mama na shirin hada auren subane sai ranan baban Khamis da yan uwa shi sukazo, tasaba dashi but har yanzu zance soyayyan su namata wani iri but koba komi yana sonta sosai kuma yanaji da ita, hanyar Suleja dataga sun dauka yasa tace "Suleja zamu? Naganmu ahanyan" gyada matakai yayi yace "yes babyna, Suleja zamu" gudu yacigaba da shararawa har suka karasa cikin Sulejan suna hira jefi jefi agaban wani dan gida madaidaici yay parking yabude motan yafita tabishi da kallo, key yaciro daga aljihun shi yabude gidan ya shiga yabude gate din sanan yadawo ya shigar da motar cikin compound din sanan yafito ya rufe gate din yadawo ta side dinta yabude mata marfin motan fitowa tayi tana kara gyara gyalenta tana kallon ko'ina, hanunta yakama yace "nakawo ki gidan dazamu zauna bayan auren mu, inkin gama gani zan kaiki company danake aiki dashi kiga office dina, do you like the house Baby? Koda yake muje kiga cikin gidan" yaja hanunta da take kokarin karba sukai ciki, dan madaidaicin falone dake dauke da manyan kujeru zaunar da ita yayi akan daya daga cikin kujerun yace "sit bari nakawo miki water" yay hanyar kitchen bin gidan tayi da kallo ganin kaman ana zama ciki saikuma ta kawar da tunanin dan anan Suleja yake aiki hala yana yawan zuwa gidan, fitowa yayi dauke da tray da two bottle water kekai sai farm fresh yogurt ya ajiye agabanta yace "baby wanan ne kawai agidan, bari namana order abinci online" girgiza mai kai tayi tace "no banajin yunwa nai breakfast fa" ruwan ya nuna mata yace "to ruwan fa" murmushi tayi tace "shima sai anjima zansha Ya Khamis" dauke tray yayi ya ijiye akasa ya matso kusada ita. Yanda ya matso kusa kusada ita yasa gabanta yafadi sosai da sauri ta matsa gefe, sake matsowa shima yayi zata sake matsawa ya fizgota yace "me haka? Common baby ninefa, me kike wani guduna kaman dodo" girgiza mai kai tayi gabanta nadan faduwa tace "a'a ka matsa, ka matso kusadani da yawa babu kyau, Allah yahana" dan rungumota yayi yace "comeee onnn babyna, am your husband to be fa, meto dan natabaki kokuma na matso kusadake? Mama tasanni, Dady ya sanni kowa ya san da maganan mu, Mama ta bamu go ahead muyi yawon Bude ido, yausai dare zamu dawo tacefa, is opportunity baby muji dadin mu mu more, now give me a kiss" yay maganan yana pulling dinta da karfi da yaji zuwa jikinshi, fizge kanta tayi arude tace "me haka Ya Khamis, kadena, wlh zan hadaka da Maman mu, ni katashi ka maidani gida nafasa fitan" tai maganan tana kokarin tashi daga kan kujera tana gyara gyalenta da kyau, sosai maganganun ta suka bakanta mai rai sosai tashi shima yayi yace "okay mutafin" da sauri tai gaba saida yabari takai wajen bakin kofa sanan yawani dauketa yay sama da ita yace "wlh sainai yanda naga dama dake after all u are my wife to be" yay hanyar bedroom da ita, ihu ta kurma tana wuntsila kafa. "Ya Khamis me haka na shiga uku, mezakamin?" jefata yay kan gado kafin ta tashi yafada kanta ya fizge gyalen da karfi da yaji ya cillar akasa da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta tafashe da kuka sosai, cikin jin haushin kauyancin ta ya dafata yace "wai me haka baby? Bakisanni bane?" kabar da hanunshi tayi cikin ihu tace "stop touching me
Chapter 8 · 0% Book details