Sashe 99
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.Imaan na kwance bedroom dinta dab da Magrib taji an danna bell, tashi xaune tayi don ita kadai ce gidan Ammi na can Unguwar rimi, daddy kuma bai dawo ba, can ta mike ta sa Hijab dinta ta nufi kofar a hankali tace "Waye?" Muryar Ummi ta ji tace "Aunty na kiran ki" Imaan ta bude kofar tana kallonta, a tare suka tafi part din da Ummi, Imaan ta wuce sama ta bude kofar dakin Aunty, Aunty ta fito bayi bayan tayi alwala tana kallonta tace "Ya jikin?" Imaan tace "Na ji sauki Aunty" Aunty tace "Ammi can xata kwana fa, sai ki dawo nan ki kwana ko ki tafi gun inna" Imaan tace "Xan je gun Inna" Aunty tace "Toh ga abinci ki dauka" ba musu ta durkusa ta dau warmer din da Aunty ta nuna mata, Aunty tace "Ki tabbatar kin sha magungunanki bayan kin ci abincin" Imaan tace "Toh sai da safe" daga haka ta bude kofa ta fita, a stairs suka hadu da Yusuf, suna hada ido ya dauke kai, tace "Lah ya Yusuf kayi tafiya ne, ban ganka 2 days ba" Yusuf na ci gaba da haurowa stairs din yace "Not at all" daga haka ya wuceta ta bi sa da kallo, can dai ta sauka ta bar parlon. Part din inna ta wuce ta sameta tana sllh, ta ajiye abincin hannunta a parlor ta fito bakin tap ta daura alwala ta koma ciki, tana idarwa ta koma kan kujera ta kwanta, inna ta gama addu'o'in da take tace "Toh wai me yasa kika baro gidan bikin kika dawo?" Imaan tace "Dama ba kwana naje yi ba" Inna ta tabe baki tace "Toh ita Rukayya taje gidan kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a bata je ba" inna tace "Ikon Allah, Kice Amina ce kawai ta je?" Imaan ta gyada mata kai, inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni, tun da uwata ta haifeni ban taba ganin haka ba wlh, Rukayya bata da xuciya mai kyau sam, ko da yake abun na da tushe, kinsan lkcn da Bukar ya auro Uwarki bata da aminiya da ta wuce Amina, lkcn Amina tana nan wata yar duma duma da ita kamar ki latsa ta jini ya feso, toh a lkcn gida daya Rukayya da uwarki suka xauna sai dai kowa da sashensa kamar dai Wannan gidan amma ko rabin gidan nan bai kai ba, lkcn Ahmadu da Bukar na yaku bayi basu da komai sai wahala, tun ba yau fa suke son junansu in gaya maki, dama a haka kuma suka taso, toh kullum Rukayya bata da aiki sai neman fitinar uwarki a tsakar gida, kaii Gaskiya Rukayya ta dade tana hauka, ga uwarki mai hakuri bata biye ta, ga uwa uba kawaici, amma akwai ranan da xuciya ya debi Aisha ta nakada ma Rukayya shegen duka har sai da ta targada mata hannu, da kyar aka kwace ta hannun Aisha, ni dai ce ma Bukar da Ahmadu nayi duk su kora su gidan iyayensu ba ruwana, to sun fa mayar min da gidan 'yaya wajen dambe, a lkcn kuma kullum Amina sai ta xo gun uwarki, tun fa Rukayya bata san Amina xata aure mata miji ba ta tsaneta har xage xage sun ta6a yi da jefe jefen dutse, to ana_nan ana_nan Ahmadu ya kyallara ido ya ga yar duma duma Amina, to karewa ma gun Aisha ya amshi lambarta idan ba mantawa dai nayi ba, Rukayya na ji tana gani Ahmadu ya aure kawar makiyiyarta wato Aisha, in gaya maki Aisha ce a kan gaba na komai da bikin, kuma ni nasan da gayya tayi haka, to da Aisha ma aka raka Amina dakinta gashi gida daya ya hade su da Rukayya, to kinji musabbabin komai... Ba irin xugar da Rukayya bata min ba kan in sa ubanki ya kara aure tunda uwarki bata haihuwa ni dai naki, kinsan da Rukayya yar dakina ce kafin ta xama bala'i, duk da dai nayi masa magana na yi masa magana har na gaji na kyalesa wato Bukar, to Aisha ta shanye min shi, daga karshe dai Bukar ya raba fada ya dauke uwarki suka koma Abuja da xama gaba daya, ai sun fi shekara biyar a Abuja, kuma fa lkcn... Katse ta Imaan tayi tace "Toh ni dai ban tambayeki ba, wllh har na gaji da jin labarin nan, a wata sai kin bada labarin nan ya fi sau biyar" Inna tace "Ai ba sai kin tambayeni ba duk sanda na ga dama dole in bada labari ko da kuwa ni daya ce a daki, to ina ruwan wani da ni??" Imaan ta tabe baki ta mike ta jona ruwa a heater don yin wanka, dawowa tayi ta xauna tana jiran ruwan yayi, inna tace "Ke wai bulasawan na maki waya ma kuwa?" Imaan tace "Ehh" inna ta d'an yi murmushi tace "Toh madallah, gama wanka ki xo in baki wani labari mai ban al-ajabi" imaan tace "Ai ruwan bai yi ba ki bani" Inna tace "Ki dai yi wankan tukun" Juye ruwan Imaan tayi haka ta wuce bayi inna na cewa "Don Allah idan kin gama ki dauraye bayin da omo, kazanta dai ba kyau" Imaan dai ba ta tanka ta ba ta cire kayanta ta shige bathroom. Imaan na gama wanka ta fiddo daya daga sleeping wears dinta dake press din inna ta saka ta feshe jikinta da turarrukan Inna ta fito ta xauna tana kallon inna da ke xuba gyangyadi a xaune, murmushi imaan tayi ta dau remote xata canxa tasha aka bude kofar parlor da sauri ta mike xata gudu xuwa daki Mujaheed ya shigo, tuni ta shige daki ta sa makulli ta wani hade rai, Inna da ta bude ido a gigice tace "Subhanallahi, lafiya??" Mujaheed dai na tsaye sai kallon kofar dakin yake, inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga jin tsoron Allah, ya xa a maida min gida kamar filin daga, baka ji yanda xuciya ta ta tsinke ba wllh, ni dai ana shiga hakkina... Wnn 'ya ta Bukar dai ba ta da imani an wani laka6a mata Imaan din karya" Shi dai Mujaheed bai ce komai ba bai kuma fasa kallon kofar dakin ba, wayar inna ya fara ring, kamar xata yi kuka tace "Kaga wani bala'in koh, toh meye wnn fisabilillahi tsakar dare kuma" daukar wayar tayi ta danna inda ake picking ta kai kunne hade da sallama tace "Waye??" Sadeeq yace "Ina yini kaka?" Tace "Ce maka nayi waye??" Yace "Sadeeq ne" Inna ta bude ido sosai tace "Bulasawa?" Yayi murmushi yace "Ehh kaka" Inna tace "Lahh ina yini??" Mujaheed couldn't stop looking at her da mamaki, Sadeeq yace "Ya gidan kaka?" Tace "A'a lafiya lau wllh Bukar, ya iyayen ka?" Yace "Suna lafiya lau" inna tace "Toh madallah, shiru shiru ban ganka ba kwana biyu, Hala imaan ce ta baka lambar wayata?" Yace "Ehh ita ta ban" Inna tace "Toh ai ta kyauta wllh, shkkn sai in ba Mujaheed da ya tsaya kaina sandandan ya min saving, yaushe xaka billo?" Sadeeq yace "Gobe in sha Allah" Inna tace "Toh Alhmdllh, da kaina kuwa xan maka tuwo da miyar taushe in sha Allah" Sadeeq yayi yar dariya yace "Toh nagode kaka, imaan din na kusa?" da sauri inna ta mike tace "A'ahh toh bari in bata har ta kwanta ina jin, Kasan bata dade da dawowa daga gidan bikin su kakarta ta wajen uwa ba" Sadeeq yace "Toh ki barta gobe xan kira in sha Allah, dama ke na kira mu gaisa" inna tace "Ae ko naji ddi Allah maka albarka, maxa kashe kudin ka na ta konewa" yyi murmushi ya katse wayar. Inna na kallon Mujaheed ta mika masa wayar tana washe baki tace "Kai yi min saving, lambar bulasawa ne" Mujaheed ya amshi wayar yana kallon number, Inna ta xauna tace "Kai amma yaron ya kyauta, wllh na ji dadi, kaga alamar xai rike min jika da kyau kenan wllh, gashi gobe yace zai shigo, sai in baka dari biyar dita ka shiga kasuwa ka siyo min kayan miya da nama lafiyayye in masa miya mai kyau" Mujaheed ya xauna kan kujera har sannan bai daina kallonta ba, tace "Ka min saving mana Mujaheed kar lambar ya bace" Mujaheed ya gama danne dannensa ya mika mata wayar ta, ta amsa ta ajiye tace "Dole in tashi da sassafe kenan gobe, bari ma in dauko maka kudin kar ka manta ka tafi baka amsa ba in rasa d'an aike" Mujaheed dake kokarin controlling temper dinsa yace "Ki dai ba Yusuf" inna ta gwalo ido tace "Waye kuma Yusuf?" Mujaheed bai tanka ta ba tace "Toh bari kaji, Rabonsa da ya tako nan ya gaida ni tun ran da yyi abun kunyar nan, to dama idan ya xo da wani idon xai kalleni, A'a ba ruwana ni bana bukatansa dama, ga dai ka" Mujaheed na gyada kai yace "Ita kuma yarinyar nan kice mata wllh idan ta sake ganina ta kwasa a guje sai na sa ta kuka a gidan nan" inna tace "Oh oh Allah, yau naga jaraba, baxata gudu ba kana cutar ta Mujaheed? nine fa na koya mata ta dinga gudu idan ta ganka, toh me xata tsaya ta maka idan ta ganka, ni dai ba ruwana, ka dinga tsoron Ubangijin ka, ai ta ma kusan aure ta huta da fitinar ka sai in ga ko gidan mijin xaka bi ta kana cuta kuma, karshenta sai ka kare a kurkuku don Bulasawa daure ka xai yi a fita da kai kasashen turai ai maka hukunci, ka ga sai ka bar Ahmadu da Bukar da kashe makudan kudaden da suka fi karfinsu, idan ba haka ba kuma ka ru6e a kurkuku in shiga uku" mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa fuska daure, inna tace "Toh kudin cefanen pa, baka amsa ba fa? Ko xaka siyo min da kudin ka" Washegari da safe Imaan na shan shayin da inna ta hada mata, inna tace "Wai me yasa kike gudun katon can ne, halan laifi kika masa" Imaan taki cewa komai da farko, can kuma tace "Ba komai, ni bana son yana kulani a gidan nan nima