Sashe 54
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace "Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace "Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi murmushi yace "Anty Hajiyan ma hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa, ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace "Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta xubo min wani" Ummi tace "Mu ma fa tuwo muka yi" A fusace Inna tace "To ni ina ruwana da tuwon ku? Ku tuwon ku har wani dadi garesa miya kamar an wanke kai, ki min abinda nace kada ran kowa ya baci a gidan nan" Ummi ta mike a fusace ta kwashe tuwon ta mayar cikin warmer din, Imaan tace "Dama kice yaya ne ya xubar na ni ba" Inna tace "Haba dai, dama ina xa ki iya xubar da wannan abincin ai sai dai shi" Tsallake miyar Mujaheed yyi ya shiga parlon ya xauna, Ummi ta tafi da abincin da ta kwashe part din su Imaan, gyaran wajen inna ta dinga yi duk suna xaune, bata gama ba Ummi ta dawo da wani abincin ta ajiye ma inna tace "Imaan Ammin ki tace xa ki dawo ki sameta" Inna tace "Sai me xai faruwa idan ta sameta, bakin cikin kara min abinci take komai, ina laifin ma tace xata gamu da Mujaheed din, Imaan ce ta wani san xubar da abincin mutane, bata ta6a ba tunda take, lafiya take kawo min abinci ta koma to yau da yake ta hadu da wnn mutumi a hanya" tana kai wa nan ta shiga parlon tana kallon Ummi tace "Don Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki karasa goge wajen baki ji bayana ba kamar xae cire" Ummi tace "Toh su da suka xubar...." Kallon da Mujaheed ke mata yasa tayi shiru ta mike rai ba dadi ta fita ta ci gaba da gyaran wajen. Inna ta shiga daki sai ga ta ta fito da bowl na dambun nama, tace "Tun ranan litinin nake ta ajiya amma ban gan ku ba na nace to ko lafiya, na ba kowa nasa...." Mujaheed ya amsa yace "Na waye wannan din?" Tace "Na kai da takwara ta" Ya saci kallon Imaan, da sauri Imaan tace "Inna ni dai ki raba mana da kanki" Mujaheed yace "Toh samo leda sai ki raba mana" komawa daki Inna ta yi, Mujaheed ya mike kafin Imaan ta ankara har ya fice parlon, kwalo ma inna kira ta yi, ya saka takalminsa ya kara gaba, inna ta leko parlon tace "Lafiya!" Imaan ta fara kuka tace "Ya tafi da naman gaba daya" inna tace "Maxa tashi ki bisa in ya kama ki je parlon Ahmadu ki tafi" Imaan ta mike ta fita parlon, bata son gudu saboda laluranta, hakan yasa kafin ta iske sa har ya shige part din su, ta goge hawayen da ya cika idonta a ranta tace "Allah ya isa" daga haka ta wuce apartment dinsu kawai, Sai da ta tsaya Ammi ta gama fadanta na xubar da abinci da tayi sannan ta shiga bedroom dinta. Bayan isha tana saka kayan baccinta wayar ta ya fara ring, duk tunaninta Sadeeq ne don kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, Daddy ta ga ke kiranta, ta daga a hankali tace "Ina yini daddy" yace "Lafiya lau Mamana, ya gida?" Tace "Alhmdlh ya aiki?" Yace "Da godiya, kina karatu sosai dai koh?" Tace "Ehh ina yi" yace "Maa sha Allah, daxu kafin magrib inna ta kirani wai sati daya kenan baki je gaisheta ba, why is that?" Imaan tace "Daddy na fa je yau" Daddy yace "All those days me ya hanaki xuwa?" Tace "Cewa tayi kar mu sake xuwa ni da yaya fa" yace "That's because kuna mata rashin kunya ke da shi, wato warning da na maki kafin in tafi went in vain koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Toh kar ki sake skipping one day baki je gaisheta ba, idan Ammin ki ce don ta maki fada xa ki k'i xuwa gaisheta, she is my mother Imaan you have to respect her much, shi ma Mujaheed na kirasa ban samesa ba ki kai masa waya yanxu" Kamar xata yi kuka tace "Toh" daga haka ya katse wayarsa, Hijab ta sa har kasa ta fita, Ammi dake parlor tana kallo ta bi ta da ido, Imaan tace "Daddy yace in kai ma yaya waya" Ammi tace "Shi me ya samu wayarsa?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, Ammi ta ci gaba da kallonta, hakan yasa ta nufi kofa ta fita. Babu kowa babban parlon nasu don hatta kayan kallo ma a kashe suke, ta haura sama ta na kallon direction din dakinsa don har ta manta rabon da ta je wajen, takawa tayi har bakin kofar sannan ta bude tana lekan cikin bedroom din, wani sanyayyen kamshi me hade da sanyi ya doki hancinta da fuskarta, shiga dakin tayi ta kulle kofar, ko ina fes har kan gadon dake dauke da farin bedsheet, Ko ba a fada mata ba tasan wanka yake jin saukan ruwa da kamshin sabulu da ya hadu da kamshin dakin, xaro ido tayi tana kallon sketches dinta dake bangon dakin kusan gudu hudu, tun tana Jss3 tayi drawing din mai kyau coz she is more than perfect a zane, turo baki tayi ta dau kujeran dake gaban mirror ta kai jikin bangon ta hau ta dinga cire hard carbon paper din a hankali kar ya yage. Bude kofar bathroom Mujaheed yyi ya fito da short yana goge gashin kansa da karamin towel, xaro ido yyi yana kallonta da mamaki, ta juya jin an bude kofa suna hada ido ta turo baki tace "Yaya daddyna yace in kawo maka waya" Tana magana wayarta da ta ajiye kan gado ya fara ring, sakkowa tayi da sauri ta dau wayar tace "Ga shi nan ya kara kira" daga haka ta nufesa ta daga kiran ta kai kunne tace "Daddy ga shi nan" mika masa wayar tayi ya amsa ya kai kunne hade da sallama, Kamar ance ta juya taga bowl din dambun naman da ya dauke ajiye a gaban mirror dinsa, yana magana da daddy amma duk hankalinsa na kanta kuma yana lura da ita, ganin ta nufi gun mirror din ya fixgota, xaro ido tayi xata yi magana ya rufe bakin, sai ce ma daddy yake toh don ya kagu ya katse wayar, kamar kuwa daddy ya shiga ransa yace "Shikenan we will talk tomorrow sae da safe" da sauri yace "Allah ya tashe mu lafiya Abba, mun gode, sae da safe" daga haka ya katse wayar ya juyota yana mata wani irin kallo yace "Drawings din da kika cire nake so ki hau kujeran ki maida su yanxu kafin ki fada min sanda na fara wasa da ke da xaki shigo min daki kai tsaye" ta 6ata fuska tace "Toh ba waya na kawo maka