← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 207

Sashe 122

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yace "Ina yini?" Mama Hadiza tace "Lafiya lau, Sannu da xuwa" Inna tace "Saurayin Imaan ne, jira kawai yake ta kare sakandari ayi magana, d'an gidan Ahmad Bulasawa ne mai gidajen man fetur a arewa, sunan yayanki garesa.... Baki ga kirkinsa ba, ni dai tunda nake ban taba cin karo da mutum mai kirki da mutunta babba irinsa ba" Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai, Sadeeq dai ya sunkuyar da kansa sai murmushi yake, Inna ta kwalo ma Imaan kira tace "Ji walakanci, to meye na gudu daga jin sallaman bawan Allah, baxa ki fito ku gaisa ba, ba don ke ba a ina xa mu sansa" Imaan da ta xauna saman gadonta ta turo baki ta ki cewa komai, Sadeeq na shafa kansa yace "Dama baki na xo gaidawa kaka" Inna tace "Ahh toh madallah, Ka ganta nan xaune...." Ta fadi haka tana nuna masa Mama Hadiza tace "Uban Imaan ne ya sha nono ya bar mata, ita ce autata, yaranta hudu a duniya Allah yayi ma daya rasuwa, dayar tayi aure tana can gidan mijinta a kasashen turawa, sai kaninta da ke karatu sannan wannan yarinya Maryam da suka xo tare, sa'ar Imaan ce yarinyar kawai dai Imaan ta fita tsayi, ita kuma Maryam din ta fi Imaan xama mace" Tagumi Mama Hadiza tayi tana kallon uwartata, Sadeeq kam murmushi kawai yake kansa a kasa, Inna tace "Toh duk ba wannan ba, kana da labarin bikin Mujaheed wannan Juma'ah me xuwa ne kuwa Bukar?" Sadeeq ya kalleta yace "Ai kam bata gaya min ba kaka..." Inna ta saki salati ta rike ha6a tace "Kaga fitina koh? Duk da dai ko ta gaya maka ko bata gaya maka xa ayi bikin baxa a fasa komai ba amma ai da ta gaya maka, Toh ni dai na gaya maka yanxu, bikin ranan Juma'ahn nan ne" Sadeeq yace "Toh Allah ya kai mu lafiya kaka" Inna tace "Ameen dai, ai har ya kai ni gidan da xa su xauna da amaryar tasa ni da imaan mun gani, baka ga gidan ba d'an madaidaici dai dai kafinsa dai, toh ba dai laifi... ni dai nace Allah ya sanya albarka ai dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Sadeeq ya kasa daina murmushi nan ko dariya ne kawai ke cin sa, Takaici yasa Mama Hadiza ta mike tana kallonsa tace "Toh Sadeeq nagode da gaisuwa Allah yayi albarka bari in shiga can cikin gida" Yace "Toh Ameen mama, nagode" fita tayi daga parlon, Inna tace "Toh ki ce ma Aisha don Allah tayi miyar shuwaka yau, naji raina na so" Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Inna tace "Don Allah Imaan ki rufa min asiri ku fito ku gaisa, wannan ai kauyanci ne daga ganin saurayi ki shige daki, ni ko lokacinmu ba a haka" Sadeeq yace "Ki kyaleta kaka" Inna tace "In kyaleta d'an nan?" bata jira cewarsa ba ta mike xata shiga dakin, Imaan na ganin haka ta maxa ta sa hijab dinta ta fito, Inna tace "Ki daina haka don Allah sai ayi tunanin goyon kauye ce ke, nan ko a Habuja aka haife ki" Dariya Sadeeq ya fara yi imaan ta daure fuska ta xauna saman kujera a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Inna ta xauna tana murmushi tace "Gida Alhmdllh" kallonta Imaan tayi da sauri ta wani daure fuska, can ta kallesa tace "Let me see you off, since you've accomplished ur mission here today" Yana murmushi yace "I see why you don't want the 3 of us together..." Inna dai sai washe baki take tana kallonsu tace "Ae ita ma babban makaranta tayi, babu irin turancin da bata iya ba wllh" Mikewa Imaan tayi tana kallon Sadeeq tace "Let go" Mikewa yayi trying hard not to laugh yace "Toh kaka na gaishe da Mama da ke, ni xan koma" Inna tace "Ai mun gode da gaisuwa Bukar Allah maka albarka...." Dubu goma ya ajiye mata tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku Bukar baka gajiya??" kofa ya nufa yace "Ai ba yawa kaka, ayi hakuri" daga haka ya fita don tuni Imaan ta fice daga parlon, sai da suka bar part din Inna Sadeeq ya tsaya ya dinga dariyar da bai samu damar yi a parlor ba non stop, Imaan ta dinga kallonsa kamar xata yi kuka, ganin yanda yake dariya seriously ta jingina da flower tana ci gaba da kallonsa don bata taba ganin dariyarsa haka ba sai this very moment, he looks more cute laughing, bata san lkcn da tayi murmushi ba her eyes still on him, don kansa ya gaji ya dakatar da dariyar haka, a hankali tace "You look cute while laughing" da sauri ta rufe fuskarta bayan ta fadi haka, ya kafeta da manyan idanuwansa, kamar ta sani kuwa ta juya masa baya tana xaro ido, and he felt like hugging her tightly to himself, ya dai yi murmushi ya sauke kansa kasa praying in his mind Allah yasa xuwa wajensu Abba da xai yi tare da uncles dinsa in few days time won't be a futile effort... Takun da suka ji a bayansu yasa duk suka juya a tare, Mujaheed ne ke tahowa tare da Maryam, Sosai gaban Imaan ya fadi tayi still inda take, tunda ya kallesu sau daya ya dauke kai, Murya can kasa Sadeeq yace "Is she the Maryam?" Imaan ta gyada kai a hankali tace "Sure" Suna isowa inda suke Sadeeq ya mika ma Mujaheed hannu, Mujaheed na kallonsa ya mika masa nasa, Sadeeq yace "Ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh" daga haka ya wuce, Maryam ta gaida Sadeeq, Yana murmushi yace "It's nice meeting you Maryam, hope babu gajiyan hanya yanxu" Tace "Ba gajiya kam, kun fa dace da sis dita, Allah ya bar ku tare" ya wara ido yace "Ameen, I love those last words of urs... Kuma dole sai na biya words din, you say what ever you want ko menene idan kuma kin bar min xabi shikenan" ita dai Maryam dariya kawai take tace "Toh nagode Sadeeq" daga haka ta bi bayan Mujaheed da sauri, tana iskesa murya can kasa tace "Wllh he is just too cute Ya M.A, Imaan is very lucky..." Mujaheed bai tanka ta ba ya bude kofar parlon Inna ya shiga ta bi bayansa, tana cewa "Nama san me xan ce Imaan ta basa for his birthday...." Kallonta yayi yace "Me xaki ce mata.." ta kashe masa ido tace "That's our secret big Bro" Xaunawa yyi saman kujera yana kallon Inna, Inna tace "Yanxu wannan yaron dake neman Imaan ya fita, baka ga yanda ya dinga fada imaan bata gaya masa bikin ka ranan Juma'ah bane, gaba daya bai ji dadi ba, Allah kadai yasan me Bulasawan da kansa xai baka, mutum miloniya meye kuma baxai bada ba" a fusace Mujaheed yace "Sai dai ya baki ke da kike bukata, amma ni bana bukata, kuma don Allah kiyi hakuri ki daina maganata a gaban mutane bana so, ni abinda nake da shi ya isheni xaman duniya ba sai na hangi na wani ba" Yana fadin haka ya fice daga parlon, Inna ta tabe baki tace "Uwarka Rukayya ka gaggatsa ma magana ka fita ba ni ba wllh, ba abinda ya hada ni da kai dama, kawai Ahmadu ne ya haifeka ni kuma na haifesa, Ni ban yi mamaki ba tunda goyon Rukayya ce kai din ai, xaka yi fiye da haka" Maryam na dariya ta mike ta fita a parlon ita ma, da daddare Imaan na fitowa daga wanka daure da towel tace "Wai ina kuka je daxu da yaya tun safe" Maryam dake operating laptop tace "Wato kina wanka hankalin ki na wajen ki fito kiyi tambaya" Dariya Imaan tayi tace "Eh mana" Maryam ta ajiye laptop din a gefe tace "Ae babu inda ba mu je ba..." Imaan tace "Kamar Ina da Ina?" Maryam tace "Ya fa ce kada in gaya ma kowa har ke" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Don Allah ki gaya min, ai ba gaya masa xan yi ba" Maryam tayi dariya tace "Anya xan iya gaya maki kuwa, ce min fa yayi amana, kuma sbda ke muka je wajen...." Imaan kamar xata yi kuka tace "Don Allah ki gaya min, wllh baxai sani ba, abinda ma ba shiri muke da shi ba yanxu"
Chapter 122 · 0% Book details