Sashe 69
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
fiddo, Sadeeq ta ga ke kiranta, ta daga ta kai kunne, Cikin cool voice dinsa yace "How r you Imaan?" A hankali tace "am fine ina yini?" Yace "Lafiya lau, kina hanya ne?" Tace "Ehh" yace "Ina xa ki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Xanje supermarket" yace "Wanda muka hadu ranan?" Tace "Ehh" yace "Tell me what you want to get sai in siyo in kawo maki yanxu" da sauri tace "A'a bana so" a hankali yace "Why?" Tace "Ni dai bana so, yanxu ma xan hau adai daita ai" yace "Toh shikenan, we will talk later, Allah ya tsare" tace "Ameen thanks" daga haka ya katse wayar ta samu adai daita ya kai ta har mall din, wani babban boutique dake opposite mall din ta shiga, gun eyeglasses ta tsaya tana duba glasses masu kyau shigen irin wanda yake sa wa, ta wara ido ganin the prices are waoww, wani da ya mata kyau sosai ta dauka tana dubawa kafin ta tafi gun da ake biyan kudin kayan ta basu atm suka cire kudinsu suka mata packaging din eye glass din ta fita ta tsallaka ta shiga cikin mall din, gun body creams ta tafi ta dau cream da take shafawa duk da akwai mai yawa a gida, kawai dai ta juye a wani container ta boye ne sanin Ammi na iya shiga daki ta duba bayan ta taho, bayan ta dau cream din xata juya ta kusa cin karo da mutum, komawa baya tayi da sauri da nufin basa hakuri, sai kuma ta xaro ido da mugun mamaki tana kallonsa, murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace "Sorry" ta sunkuyar da kanta yace "Har kin gama shopping din ko yanxu kika fara" ta dauke kai tace "Na gama" yace "Toh mu je ki rakani I want to get somethings" Daga haka ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar munafuka, gun kayan ciye ciye su chocolates, biscuits sweets da dai sauransu ya tafi, yana kallonta yace "Kanwata xata yi birthday gobe, so nasan dai ku mata babu abinda ku ke so da ya wuce wannan, am asking for a favor duk abinda kika san kina so ki daukar mata nasan ita ma xata so" Murmushi tayi tace "Ohk then" nan ta dinga jidan duk abinda ya kwanta mata take mugun so kuma, ya dinga tura trolley din yana biye da ita, xaro ido yyi yace "Anya imaan wannan banda mugunta kuwa, yanxu duk wannan abubuwan da kike dauka kina nufin kina son su?" Ta juya ta wara masa manyan idonta tace "Ai duk abinda kaga na dauka a nan I love it with all my heart, baka san yanda nake son chocolates da sweets ba koh" murmushi yyi yace "Toh mu bar mata su a haka" tace "A'a jira ga wani chocolate can..." Da sauri ta tafi ta debo har biyar ta xuba a trolley, ta kwaso wasu biscuits ma ta xuba, ta dau wani sweet ta xuba shi ma, ta juya tana kallonsa tana murmushi tace "Toh ni dai ina mugun son teddy in daukar mata" ya langwabar da kai yace "Kawai so kike account dina yayi kuka yau koh??" Ta hade rai tace "Just guda biyu ko uku fa, Is she not ur sister? And is it not her birthday" daga haka ta tafi gun teddies ta debo uku masu tsada da kyau ta jefa cikin trolley din tace "Tunda kana complaining account dinka, mu bar mata su a haka kawai" Yar dariya yyi yace "Noo ci gaba har sai kin gaji" tace "A'a I have conscience" dariya yyi ya bi bayanta ganin ta nufi gun counter, cream dinta ta ajiye xata bada ATM card ya riga ta mika nasa, juyawa tayi tana kallonsa sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, nan aka cire kudin aka bata receipt dinta, ta taya sa ciro abubuwan cikin trolley din shima ya bada atm card aka cire aka masu packaging, barinsa tayi da kayan gaba daya ta dau teddies din suka fita. Bayan ya xuba ledojin a bayan mota ya rufe motar yana kallonta kafin yace komai tace "Yau ne birthday din?" Gyada mata kai yyi smiling, ta boye fuskarta a hankali tace "Toh ni dai ina son kaza ko xaka siya mata" Wara ido yyi yana kallonta, sai kuma yyi dariya yace "Ina kika ga kaxa imaan?" Ta turo baki ta nuna masa inda ake gashin kaji, yana murmushi ya tafi, ya siyo kajin gasassu biyu ya dawo ya sa a mota, ya juya yana kallonta pleadingly yace "Let me drop you plss" da sauri tace "Nooo thank you" tana fadin haka ta bude karamar jakarta ta fiddo glass din dake leda tana kallonsa ta mika masa, a hankali ya sa hannu ya amsa yana kallon kwayar idonta, hakan yasa tayi saurin sauke nata idon, bude ledan yyi ganin glass din underneath his breathe yace "Waow..." Murmushi tayi xata juya masa baya ya riko hannunta cikin sanyin murya yace "Thanks Imaan, I love it..." Bata ankara ba sai gani tayi yyi pecking hannunta, ta kwace hannun da sauri tana xaro ido a tsorace, shi ma daburcewa yyi yace "I... Sorry I.. I am just happy imaan, I love the glasses" ta kirkiri murmushi har sannan tana jin warm lips dinsa a hannunta, xata juya yace "Wait Imaan" tsayawa tayi gabanta na faduwa, ya bude front seat yace "Plss let me drop you home" kasa ci gaba da kallonsa tayi ta kuma kasa cewa A'a, a hankali ta shiga motar yyi murmushi ya rufe, ya xaga ya shiga driver seat suka bar mall din, bata yrda yaje dai dai gate din su ba tasa ya ajiye ta few houses away from theirs, ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka ya xaga ya bude back seat, ya fiddo gaba daya ledojin siyayyar da suka yi da teddies da kajin duk ya ajiye kusa da ita ya wara ido yana mata murmushi yace "Dama duk naki ne" bai jira cewarta ba ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar ya bar ta da zare ido ya bar layin, kallon ledojin ta dinga yi kamar xata yi kuka, yanxu ya xata yi da kayan nan.... Kwasa tayi ta boyesu cikin flowers ta dinga dauka da daddaya da daddaya tana kai su part din inna, duk a mugun tsorace take, Inna ta saki baki tana kallon kayan, imaan ta tafi dauko last ledan, Yusuf dake ta kallonta tun shigowarta na farko ya mike ya isa kusa da ita da mamaki yace "Daga ina kike wannan saurin hakan Imaan, what's all this u are taking in" kin tsayawa tayi tana kirkiran murmushi ta wuce sa da sauri, tsoronta daya kar ta gamu da Mujaheed, har dai ta isa parlon inna, Inna dake tsaye bakin kofa har lkcn ta sake baki tana kallon uban ledojin ta bi ta da kallo har ta ajiye na hannunta, Inna tayi kasa da murya tace "Imaan ina kika samo wannan kuma?" Imaan ta kwashesu gaba daya ta kai dakinta da sauri duk ta ajiyesu sanin Yusuf xai iya biyota, Tana fitowa dakin tace "Ni dai kawai kiyi shiru inna kar ya Mujaheed ya sani wllh duka xai min" Inna ta hade rai tace "Duka?? da kuwa ya dokar ma kansa fitina da bala'i, kuma da karshen xamansa ya kama a gidan nan" Imaan ta xauna saman kujera har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Yusuf ne ya shigo parlon, inna ta wani tsuke fuska, yana kallon Imaan yace "Daga inna kike Imaan?" Inna tace "Yau naga jaraba, to ina ruwanka isuhu ko ka aiketa ne? Ku dai 'ya yan Ahmadu ku daina sa ido wllh, meye kuma wani daga ina take kamar xamanka take a gidan, ni dai ba ruwana, ku dinga tsoron Allah kuyi mai fishshe ku a gidan nan" juyawa Yusuf yyi ya fita parlon, inna ta kulle kofarta ta sa makulli, ta kalli imaan tana murmushi tace "Kar dai sabon saurayin ne yyi maki uban siyayyar nan takwara" Imaan tace "Wllh kar ki gaya ma kowa idan ba haka ba kazar ma baxan tsam maki ba" Inna tace "Ke ma dai da wata magana wllh, sai kace wata yarinya?? Wa xan gaya ma ni patuu, wannan ai sirri ne tsakaninmu" Imaan ta shiga ta fiddo ledan kajin guda biyu tace "Toh idan yaya ya shigo fa?" Inna tace "Oh oh Allah, waye kuma wani yaya, ina ruwana da shi, ko me xai xo ya min? Ko ya xo ma ni baxan bude kofata ba bbu ruwana, idan ma ya xo damuna yake ba abinda yake tsinana min"