← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 207

Sashe 171

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

don haka yanxu kawai so nake kada auren ya faru, ni dai ba shige shige nake ba balle ace, ba ruwana da boka ko malam, kawai dai da yan dubaru xa a raba su, kema kuma dole sai kin bada contribution" Safeenah tace "Toh ta yaya?" Umma tace "Ba kince tana xuwa gidan nan ba, dama nima naji labarin suna xuwa da kakar, shi yasa nace bari in xo in same ki" Safeenah tace "Ba dai ko da yaushe su ke xuwa ba sai jefi jefi" Umma tace "When last suka xo??" Safeenah tace "xai yi kusan wata daya, Umma tayi tagumi tana naxari, can ta kalli Safeenah da ita ma tayi shiru xuciyarta fal takaicin wanda Imaan xata aura, wai yaron Bulasawa, Umma tace "Kinsan me xai faru yanxu Safeenah" Safeenah ta kalleta tace "A'a" Umma tace "Ki jira sai Mujaheed din ya dawo sai ki ce masa kwana biyu baki ga Inna ba, yaushe xata xo?? Ko kuma kyalesa kawai bari in baki lambar Innar ki kirata sai bayan kun gaisa sai ki tambayeta kwana biyu shiru shiru baki ganta ba yaushe xata xo??" Safeenah tayi murmushi tace "Koh?" Umma tace "Ahaf jikinta na rawa xata xo, ai ita tana son a dinga nuna ana ji da ita, kuma in xata xo da wuya ta xo ita kadai, Dole da Imaan din take fita kinga shikenan Allah ya kawo mana ita har gida amma kar ki yarda ki gaya ma Mujaheed kamar yanda nace da farko don akwai sa da kwakwalwa, nan da nan xai gano ki" Safeenah tace "I thought as much, ga wayar ki sa min lambarta" Umma ta amsa wayarta ta saka mata lambar Inna daga nata wayar sannan ta mika mata, Safeenah ta amsa ta kai kunne, Inna na dagawa ta rafka sallama, Safeenah ta amsa tace "Ina yini Inna?" Inna tace "Lafiya lau, waye don Allah, ni dai aiki nake ta yi na bude ma mutane akwatuna tun safe suna shigowa gani, kinsan duniya ba gaskiya yanxu sai a samu rikakken barawo da xai boye abu ya wuce da shi shi sa nake sa ido" Safeenah tace "Safeenah ce Inna" Inna tace "Waye Safeenah kuma?" Safeenah ta tabe baki tace "Matar Mujaheed" Inna tace "Ayyo, Safara'u ce, Toh sannu kin ji labarin an kawo kaya kenan?" Safeenah tace "A'a ban ji ba" Inna tace "Atoh wa xai gaya maki dama d'a bakin ciki uwa bakin ciki, wllh har yanxu ban ga keyar Rukayya ba, Mujaheed kuwa tunda ya shigo ya gaggasa min magana ban kara ganinsa ba sai jiya da aka kawo kaya, bakina a leko na shiga daki da gudu na dau katon bargona na rufe ma yarinya kaya da shi tun bai kai ga gama kirga guda nawa bane, akwatuna takwas ne da kyar ake xuge xif din, Toh me xance banda in gode Allah, har da gwal na dankunne guda biyu da xobuna biyu fa a ciki, ni dai ba ruwana duk me ma jikata bakin ciki Allah shi yasan yanda xai yi da shi, ko ke wllh baki samu haka ba shi sa Mujaheed ya fito kiri kiri ya nuna bakin cikinsa a fili, kwana nayi Ina al-ajabin abinda ya gaya min ranan wllh, isuhu kuwa har nan ya xo ya min Allah sanya alkhairi...." Safeenah da Umma sai sauraronta suke don a hands free Safeenah ta sa wayar, Umma ta wani kankance ido tana kallon wayar, Safeenah ta tabe baki tace "Toh Allah ya kyauta, yaushe xa ki billo Inna kwana biyu shiru" Inna tace "In billo a yashe ma yarinya kaya in shiga uku Safara'u, ai ba xancen billowa sai na kai Imaan dakinta, sa ido yayi yawa gwara in mike tsaye kyamm, toh ke baxa ki xo ganin kayan bane kike jira in billo?" Safeenah ta kalli Umma, Umma ta gyada mata kai da sauri alamar tace xata xo, Safeenah ta tabe baki tace "Toh xan shigo in sha Allah" Inna tace "Atoh, sai kin xo, sai kiyi sauri don xuwa anjima xa a kai ma kakarta ta wajen uwa ta ga kayan ita ma, sannan a maido min inyi gadin kayana" Safeenah tace "Toh sai anjima sai na xo" Bata jira cewar Inna ba ta katse wayar tana kallon Umma da tayi tagumi, Safeenah ta ja tsaki tace "Ai nima sai inda karfina ya kare wajen ganin auren nan ya fasu wllh, wato shi sa yarinyar ke ganin kowa banxa, ita a dole xata auri yaron Bulasawa to taga samu ta ga rashi tunda har labari ya xo kunne na kuwa" Umma tace "Wllh da kin gama min komai a duniya idan har muka hadu muka tarwatsa lamarin nan, Kinga wahalar da na sha gun uwar yarinyar nan wllh kwakwalwarki baxai dauka ba, ta dalilin uwarta aka min kishiya, aka kuma sakeni...." Nan umma ta fara giggila ma Safeenah karya da gaskiyar abinda ya hadata da Ammi, tana kai wa aya, Safeenah ta gyada kai tace "Ki kwantar da hankalin ki Umma, ai tunda har labari ya xo kunnena an gama komai, dama kwata kwata na tsani yarinyar tun daga ranan da na fara daura ido kanta, ki manta da ko wani shiri da kike a da ki sa min ido" Umma tace "Atoh, shkkn.. Amma fa baxan mance shirin da nake ba, don kunya ba kadan ba nake son Uwar yarinyar ta kwasa a hannu, yanxu dai ki shirya anjima kije ganin kayan kada a dago komai a rai" Safeenah tace "A'a rashin xuwan kawai ya fi, ban gani ba balle raina ya kara 6aci" sai kusan yamma umma ta bar gidan ko digon ruwa bata sha ba, amma ko a jikinta. Yau tun safe Mujaheed ke xaune garden din gidansa har wajen sha biyu na safe, Safeenah ce ta shigo garden din cikin shiga ta alfarma tana taunar cingam tana kallonsa tace "Doctor d'an baccin weekend din ma gaba daya baka yi ba yau, ni dai yanxu fita xan yi, xan je can gida daga nan kuma in tafi gidan ku in gaida su umma" Daga kai yyi ya kalleta calmly yace "Baxa ki ba" Safeenah ta gwalo ido tace "Baxan je ba kuma, mahaifiyata da taka xan je gaidawa fa" ya mike a d'an tsawace yace "Nace baxa ki fita gidan nan ba Safeenah..." Daga haka ya wuce ya bar ta wajen tsaye, ta ja tsaki tace "Don kana fama da miskilancin ka kwana biyu sai ka sauke kai na, Toh wllh sai na fita" Kiran Umma tayi da wayarta ba a dau lkci ba Umma ta daga, ko gaisuwa babu Safeenah tace "Toh gashi dai ya ki bari na in fita wllh kuma yau ya kamata mu yi abinda ya kamata, kusan sati daya kenan Mujaheed magana da kyar yake min a gidan nan, ni ban damu ba don dama haka yake wani lkcn amma na wannan karan yyi yawa, tun asuba yake xaune garden yau wllh kamar maraya, during weekdays kuwa dama sai nayi bacci yake shigowa ya fice kuma da sassafe washegari, kwata kwata na rasa gane kansa ban san me ke damun sa ba, ni duk wannan ba wani damuna yyi ba don a sauki na, amma yanxu gaskiya ki kirasa ki masa magana don idan har ban fito ba yau shirye shiryen mu ya ruguje ne kawai" Umma tace "Kyaleni da shi kawai, mu ma nan ai ya fi satin bai xo ba, Ina ga halinsa na da ne ke kokarin dawowa" daga haka umma ta katse wayar, Safeenah ta tabe baki ta wuce cikin gidan, tana ta xaune parlor har bayan minti talatin ganin bai sakko ba ta mike ta wuce sama, ya fito wanka kenan ta shiga dakin, yana mata wani kallo yace "Kin xata kiran da kika sa mahaifiyata tayi min xai sa ko fita gidan nan ne yau??" Ta nufesa tace "Wai me ke damun ka two days ne Mujaheed, dubi fa you look so pale, and ni dai nasan lafiyar ka qlau" Ko kallonta bai yi ba ya bude press dinsa ta rungume sa ta baya tana shafa chest dinsa cike da shagwaba tace "Ni dai wllh ka gaya min meye damuwarka mijina" Bata jira cewarsa ba ta juyo da shi ta rungume sa gam tana shige masa and she really turn him on....
Chapter 171 · 0% Book details