← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 207

Sashe 202

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na kira in ji dalilin Change of attitude dinsa?" Imaan da har hawaye ya kawo idonta ta girgixa mata kai a hankali, Maryam tace "Ce min yyi ince maki idan kin isa ki fada ma su Abba kin fasa auren a dawo masa da sadakinsa" Sosai gaban Imaan ya fadi ta dinga kallon Maryam xuciyarta na bugawa, Maryam ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "I am not in support of you marrying Sadeeq any longer Imaan, ba shi da mutunci ko kadan, hallaka ki kawai xai yi Imaan, kiyi hakuri ko min son da kike masa ki samu Inna ki gaya mata abinda ke faruwa a san abun yi tun da sauran lkci..." Imaan ta fara kuka a hankali, cikin sanyin murya tace "But I love him Maryam, shi ma yana sona, I just don't know what came over him..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da dinning cikin rawar murya tace "May be stress yasa yake jin haushi haka, ni dai nayi masa uxuri, this is not the Sadeeq I use know, nasan idan munyi aure xa mu koma yanda muke da in sha Allah...." Da mugun mamaki Maryam ke kallonta tace "Are you on ur right senses Imaan, Ina gaya maki ga abinda mutumi yace kice idan kunyi aure xa ku dawo yanda ku ke da???" Imaan ta dago tana kallonta hawaye na sakkowa idonta tace "Ina sonsa a haka Maryam, kawai ki taya ni da addua Allah ya maida sa yanda yake da, beside bayan duk bak'in da suka taho from different places sai ace an fasa aure, idan shi bai fito ya fada masu ya fasa ba I see no reason why I should do so Maryam" Mikewa Maryam tayi tana mata wani irin kallo tace "Baki da hankali wllh" Imaan ta tashi da sauri tace "Plss this should be between us, ban ga dalili me karfi da xai sa ince na fasa auren nan ba, don Allah forget you even called him, ai ni xan xauna da shi ba ke ba, I know he loves me, nima kuma Ina sonsa, so plss mu bar maganan nan a nan" daga haka Imaan ta bar dinning din Maryam ta bi ta da kallo baki bude. Daren ranan Imaan bata yi bacci ba, gaba daya she is just disturbed nd restless, ta mike xaune daga karshe ta kalli Inna dake sllh kamar dai yanda ta saba duk dare, kallon agogo tayi taga biyu da minti biyar, wayarta ta dauka tana kallo, sai kuma ta shiga text message, cikin minti goma ta gama rubuta ma Sadeeq text, da farko tambayarsa tayi ko tayi masa wani laifi ne ya gaya mata, daga karshe kuma ta basa hakuri cikin tausasan lafazi ta tura masa, tagumi tayi tana kallon wayar duk da bata expecting reply don tasan bacci yake at that time, text taga ya shigo wayar nata gabanta ya fadi sosai, ta dinga kallon wayar kafin ta dauka ta bude text din tana kallon content dinsa, "if you think you notice any change of behavior da bai maki ba a tattare da ni, ki yanke hukunci da kika ga is the best, wanda xai yi suiting din ki" ta karanta text din ya fi a kirga amma ta kasa apprehending, can ta yi dialing numbersa har ya gama ring bai dauka ba, ta kuma kira bai dauka ba, ta tura masa text na cewar ya dau call dinta don Allah, ba a dau lkci ba reply ya shigo yace "Good night" Ta dinga kallon reply din sannan ta ajiye wayar ta mike ta shige bathroom ta rufe kofa, kuka ta fara yi a hankali tana jin xuciyarta na mata xafi, tayi kukan da ta dade bata yi ba amma maimakon taji d'an sanyi a ranta sai k'una da radadi, bubbuga kofa Inna tayi tace "Me kike yi a bandaki tun daxu Imaan, lafiyan ki??" Imaan ta fara wanke fuskarta da sauri, Inna bata fasa bubbuga kofar ba hakan yasa imaan ta bude kofar kanta a kasa, Inna ta gwalo ido tace "Kukan uban me kike? Ni fa bana son a gigitani gaskiya, ni ba karamin aiki na bane ince ki bi dare ki koma gidan ku, lafiya kike kuka a bandaki" Imaan bata tanka ta ba ta fara alwala, Inna tace "Naga jaraba, don xa a maki aure kuma sai ki shige bandaki kiyi ta kuka salon cuta ta kama ki" inna na tsaye tana kallonta har ta gama akwala ta fito ta sa hijab dinta ta hau saman darduma, Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" daga haka ta tafi ta xauna ta ci gaba da addu'o'in da take. Washegari tun sassafe Umma ta bar gida ana girke girke, ko danginta daya babu a cikin mutanen da suka cika gida, Ummi da Rahma ma duk ta sa sun shirya sun bar gidan, Aunty mamaki ta dinga yi na irin xuciyar umma, tunda take bata taba ganin mata mai nuna bakin ciki kiri kiri a fili irin Umma ba don cikin anko hudu da suka yi da Ammi ko daya ta ki yi, su Ummi ma ta ki barin su dinka nasu da aka masu. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Aunty misalin tara na safiyar ranan Thursday din, Inna na kallonsu tace "Toh dama so nake ku rufa min asiri ku tattara 'yarku ku maidata can bangaren ku, tun daren jiya take kuka ga idanuwa can sun kumbure, toh ina dalili wani abun ya sameta a bangarena, dama aure hauka ne, wannan mata mai gyaran jiki ba irin lallashin da bata mata ba amma kamar ana tunxurata, to tunda uwarta ta sallama maku ita shi sa na kira ku, ku tafi da ita can nayi kokari haka kuma Allah ya gani" Aunty ta mike ta tafi dakin inna tana kallon Imaan dake kwance, murmushi tayi ta xauna kusa da ita ta dagota tace "Haba daughter, kuka kuma haka?? Ko kina da damuwa ne?" Imaan bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, Aunty tace "Kiyi hakuri kar ki sake kuka kinji, it's always like this for every lady Imaan" Imaan ta fara wani sabon hawayen, Aunty ta rungume ta tana lallashinta, Mama Hadiza ta shigo dakin ita ma ta dinga kwantar mata da hankali, sai da suka tabbatar tayi shiru gaba daya sannan suka fita dakin, Aunty ta hado mata shayi mai kauri ta kai mata.
Chapter 202 · 0% Book details