Sashe 107
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
It's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then you show ur evidence of payment through my WhatsApp digit 07087865788 to be included in d payment group. Mujaheed ya kalleta yace "Ina son xan je gidansu Farida ne" Ammi tace "Wace faridar? Wace ku ka yaudara ko wata daban?" Shiru yyi bai ce komai ba, Ammi ta tabe baki ta maida dubanta kan TV, yace "Ni ban yaudare ta ba Ammi, kila hakan Allah ya tsara we are not destined to be together" Ammi tace "Toh yayi kyau, haka Allah ya tsara" Bai ce komai ba, can ta kallesa tace "Toh me xaka je ka mata?" Yace "Ina son xuwa in bata hakuri ne, idan ta gan ni da Imaan she might listen to me, bana son tayi tunanin yaudararta nayi" Ammi tace "Toh Allah ya kyauta, amma yanxu dare yyi sai ka bari gobe" yace "Gobe da safe xata wuce kano" Ammi ta girgixa kai, tace "Toh ba sai ku tafi har da Maimoon ba" yace "Eh xa mu je tare" Ammi tace "To ka turo Maimoon din xa su fito tare" yace "Toh nagode" daga haka ya mike ya mata sallama ya fita parlon, Ammi ta mike ta shiga dakin Imaan xaune ta sameta tana karatu, Ammi tace "Ki shirya ke da Maimoon xa ku raka Mujaheed wajen Farida" Imaan ta xaro ido tace "Yaya kuma? A'a ni Ammi baxan je ba" Ammi ta dinga kallonta sannan tace "Me yasa?" Girgixa kai tayi tace "A'a ni bacci nake ji" Ammi tace "Me ya hada ku da Mujaheed din?" Da sauri ta kalli Ammi sai kuma ta dauke Kai tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Toh tashi ki rakasu ku dawo" daga haka Ammi ta fita dakin, da kyar Imaan ta mike har ranta bata son bin Mujaheed, can dai ta sa Hijab dinta har kasa ta fito, dai dai nan Maimoon ma ta shigo parlon, Ammi na kallon Imaan tace "You pray before leaving, and ku kula" A hankali Imaan tace "Toh" daga haka suka fita tare da Maimoon bayan ta gaida Ammi, a waje suka samesa yana jiransu cikin mota, Maimoon ta shiga back seat, Imaan ta hade rai ta shiga ita ma, Maimoon tace "Ki tafi gaba mana" Imaan tayi mata banxa ta rufe motar, Mujaheed yace "Wata ta dawo gaba, I am a driver to none of you" Maimoon ta turo baki ta bude motarta ta fita ta koma gaba, tada motar yyi suka dau hanyar titi, lkci lkci yake kallon Imaan dake kallon waje, gidan yayar Farida dake unguwar sanusi suka tafi, Mujaheed yyi parking kofar gidan ya kashe motar, yace "You two should go in, ku ce mata I am outside, she isn't picking her cals" Imaan ta bude motar ta fita, Maimoon ma ta fita suka shiga gidan a tare, A parlor suka tadda yayarta da yaranta uku, tana kallonsu ta amsa sallamarsu, Imaan ta xauna ta gaisheta Maimoon ma ta gaisheta duk ta amsa amma da alamar bata gane su ba ma, Maimoon tace "Aunty Farida fa?" Yayar tace "Tana daki" karamin yaronta ta aika ya kirata a daki, sai ga ta ta fito, tsaye tayi tana kallonsu, can tayi murmushi tace "Sannu ku da xuwa" Imaan tace "Ina yini Aunty farida" Farida ta xauna tace "Lafiya lau Imaan ya Ammi fa" Maimoon ma ta gaisheta ta amsa tace "Daga Ina ku ke haka da daren nan?" Imaan tace "Daga gida mana" Murmushin fuskarta yayi fading tace "Toh a xubo maku abinci" Imaan tace "A'a mun ci abinci, Aunty farida Ammi ce ta aiko ni" Farida tace "Ayya, toh ina jin ki" Imaan tayi murmushi tace "Ko xa mu je waje?" Farida ta mayar mata da murmushin sannan ta kalli yayarta tace "Anty kanin Mujaheed ne" lkci daya yayar ta hade rai ta ci gaba da kallonta, Imaan ta mike tayi ma yayar sallama Maimoon ma haka sannan suka fita, Farida ta mike ta bi bayansu, mamaki ya kamata ganin sun fita wajen gate don ta xaton cikin compound din Imaan xata bata sakon Ammi, ta dai bi bayansu har waje, sosai gabanta ya fadi ta tsaya tana kallon Mujaheed dake tsaye jikin mota ya rungume hannunsa, ta sunkuyar da kai ya karasa har inda take, Juyawa tayi xata koma ciki ya kamo hannunta a sanyaye yace "Pls listen to me Farida" kasa kallonsa tayi hawaye ya kawo idonta, sosai jikin Imaan yyi sanyi, Maimoon ta bude mota ta shiga don ita ma ta bata tausayi, cike da karfin hali Mujaheed yace "I neva meant to break ur heart Farida, even for once, but you know Allah plans best, may be we were neva destined to be together, ki yafe min pls, Umma ta bata son aurenmu and I can't disobey her" Hawaye na xuba idonta tace "Allah yasa hakan yafi alkhairi, and I am wishing a happy married life in advance" a sanyaye yace "Forgive me plss Farida" ta gyada masa kai da kyar tace "I have done that in sha Allah" Yace "Tun daga farkon relationship dinmu 4 years ago har xuwa yanxu idan na 6ata maki kiyi hakuri ki yafe min" tace "Baka min komai ba kuma na yafe maka ni ma ka yafe min, Allah kuma ya saka maka da alkhairi abubuwan da ka min from the beginning har xuwa yanxu, thank much Muhd, Allah kuma ya baka Ikon ci gaba da yi ma mahaifiyar ka biyayya, ku rabu lafiya" Ya sauke idonsa kasa yace "in sha Allah xa mu dinga xumunci..." xame hannunta tayi ta juya ta nufi gate dinsu, a hankali yace "Idan Allah ya kaddara you will still be my wife some days, I will be very glad in hada ki da kanwarki...." Farida bata juya ba har ta shiga ta rufe gate din, Juyawa Mujaheed yyi kamar mai tausayin kasa ya xaga ya bude driver seat ya shiga,Tada motar yyi yana kallon Imaan da ta turo baki bayan ta goge hawayen idonta, Bai ce komai ba ya bar layin da motar, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin motar, the journey was very silent, yyi parking a kofar gida Maimoon ta bude motar ta fita, Imaan ma ta fita ta shiga gate da sauri, Parlor ta tadda Ammi, ganin mood dinta Ammi tace "Ya aka yi" xaunawa tayi hawaye ya kawo idonta tace "Ammi ta ban tausayi, me yasa Yaya xai mata haka, he betrayed her" Ammi ta tabe baki bata ce komai ba, tace "Har kuka fa sai da tayi" Ammi tace "Toh Allah ya bata wanda ya fi sa, wani hanin ga Allah bai wa ne, bata san ma wani gata Allah ya mata da ya rabasu ba, don Ina tausaya mata idan Mujaheed ya aureta barin yanda uwarsa bata sonta" Imaan tace "Toh Saboda me?" Wani murmushi Ammi tayi tace "Ko makiyina baxan ba shawara ya ba ma Mujaheed 'yar sa ba, Kinga Hajiya Rukayya ta wuce tunanin kowa, ni ba miji daya muke aure ba amma irin xaman da muka yi ba shi da banbanci da muna auren miji daya, na sha wahalar ta ne, sam bata san da annabi ya kafu ba" Imaan dai tayi shiru, Ammi tace "Don haka gwara dai ta aura ma d'an nata yar kawarta, sun fi kusa kuma sun san kansu" Washegari Juma'ah Imaan na dawowa schl ko uniform bata cire ba sai ga inna ta sha atamfarta mai tsada an yafa mayafi, Ammi tace "Sannu da xuwa Inna" Inna tace "Yauwa takwara ta dawo makaranta kuwa?" Ammi tace "Ehh yanxu ta shigo" inna tace "Toh da kyau, dama so nake ta rakani gidan ta rasulu kwana biyu shiru ban ganta ba" Ammi ta kwalo ma Imaan kira, Imaan ta fito, Ammi tace "Xa ki raka Inna anguwa" Imaan ta hade rai tace "Ban ma yi wanka ba kuma ban ci abinci ba, gashi kai na ma ciwo yake min" Inna tace "Kanki na ciwo kuma? Toh yi xaman ki bari in je in samu Maimoon ko Ummi su rakani, ya xan yi dake idan kin fadi a titi, wa gareni titin?" Daga haka ta juya ta fita, Imaan ta koma dakinta. Imaan na wanke wanke kitchen da yamma Ammi ta kwalo mata kira fito da sauri, Ammi tace "Kiran ki ake a waya" daukar wayar tayi ganin Sadeeq ne ta daga ta bar parlon, gaisawa suka yi yace "Pls dear ki d'an fito ki amshi sakon Inna am outside" Imaan tace "Sako kuma?" Yace "Ehh ko kina wani abu ne?" Tace "A'a ka dai shigo ka kai mata ai ni bn san da sakon ba" yayi murmushi yace "Ai anjima da daddare xan xo sai muje part din nata tare, yanxu sauri nake Mum dita ta aikeni xan kai mata sako" Imaan tace "Toh sakon meye?" Yace "Ke dai fito ki gani" a hankali tace "Toh" Daga haka ya katse wayar, Ammi dake jin wayar da take tace "Sakon meye?" Imaan tace "Ko ba Inna bace tace ya siya mata iron" tagumi Ammi tayi tana salati, can tace "Yanxu Inna mutunci take nema mana gun yaron nan ko tsiya, sam ban ji dadin sanin yaron nan da tayi ba, me kuma xata yi da iron idan ba fitina ba anjima ta hada kayan ta bada a goge mata gun masu laundry, wannan wani irin kaskanci ne fisabilillah, to ita Ina nata iron din?" Imaan tace "Daga ranan Ummi ta ce ya mata shocking shikenan Inna ta saka a bola" Ammi tayi salati tace "Wannan tsohuwa dai Allah ya raba mu da ita lafiya, ynxu abinda nake so da ke idan ta dawo anjima ki dau wayarta kiyi blocking number sa sannan kiyi deleting don ba mutunci take siya maki a gun sa ba, snn ki nuna masa baki son ma yana xuwa bangarenta kwata kwata" a hankali Imaan tace "Toh" Hijab kawai ta sa ta fita kofar gida, waya na kare kunnensa ya kafeta da ido har ta iso inda yake, katse wayar yyi yace "How are you doing dear" tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace "Fine Alhmdllh" Bude motar yyi ya fiddo wani leda ya mika mata yace "Gashi ki ba Grandma" Shiru tayi bata ce komai ba, can ta amsa tace "Toh angode" wani ledan ya fiddo ya