← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 207

Sashe 176

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Sorry for the short chapter... don't forget i am still not home but I am managing to type, in sha Allah xuwa karfe tara da wani abu ltr xa ku ji ni.
Thank you.

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788Mujaheed yyi wani murmushi yana shafa kansa a hankali yace "Saboda bai dau wayarki ba shine kika fara leg and backache kenan??" Banxa tayi masa ta koma ta kwanta ta juya masa baya, ya dinga kallonta ko kiftawa babu kafin ya mike ya nufi kofa yana murmushi ta bi sa da harara har ya fita ya rufe mata kofa. Tun daga wannan rana Sadeeq ya daina kiran Imaan gaba daya sai dai in ita ta kirasa, sosai ta shiga damuwa ta rasa me ke mata dadi, ko abincin kirki bata iya ci, bata taba tunanin akwai abinda xai daga mata hankali haka ba, ko da yaushe a sanyaye xaka ganta, tana wanke wanke a kitchen ranan Thursday da yamma Ammi ma na kitchen din tana kwashe shinkafar da ta dafa a warmer, tarwatsewan glass cup da ta ji yasa ta juya da sauri tana kallon Imaan da ta koma baya tana xaro ido, don na biyu kenan ta fasa tsayuwarta a sink din, Ammi ta daure fuska cikin tsawa tace "Are you stupid imaan, tunanin uban me kike kika sake fasa min wani cup din?" Hawaye imaan ta fara yi tana kallonta, Cikin tsawa Ammi tace "Get out kar in gaura maki mari my friend" juyawa Imaan tayi da sauri ta fita, Ammi ta gama kwashe abincin ta tafi ta ci gaba da wanke wanken, tana gamawa ta fita xuwa dakin Imaan, Kwance ta ganta ta rufe fuskarta da pillow, har ta karasa kusa da ita ta xauna gefen gado bata sani ba, Ammi tace "Imaan..." Da sauri ta dago a tsorace don bata ji shigowar ta ba, sai kuma ta fara goge idonta tana sunkuyar da kanta, Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Tell me what's wrong with you plss Imaan, kina da wata da xaki fada ma damuwarki ban da ni, am asking you this for the third time, kar ki yarda in kira daddy yanxu kin san dawowa xai yi" Imaan ta fashe da kuka sosai ta rungume ta, lkci daya jikin Ammi yyi sanyi, ta dago kanta cike da damuwa tace "Ki gaya min damuwarki daughter" cikin rawar murya tace "Ammi mai sunan Daddy ne...." Da mamaki Ammi ke kallonta lkci daya kuma gabanta ya fadi don right from time ta gudar ma only child din tata heartbreak, cike da karfin hali tace "What about him???" Cikin kuka Imaan tace "He is calling me no more, ko na kirasa baxai dauka ba sai washegari" Ammi dake kallonta duk da tashi da hankalinta yyi ta dake tace "Me ya hada ku?" Shiru Imaan tayi hawaye na sakko mata, bata ma san me xata ce ma Ammi ba, tasan ko hauka take baxata ce don ya ganta da Mujaheed a eatry bane Mujaheed na bata nama a baki, ta hadiye abu da kyar tace "Kila saboda yana ganina tare da Yaya ne always" Ammi tace "Toh dole sai kin tsaya tare da Yaya, Ina ruwanki da shi da yyi aurensa, wato yana ganinku kuna shashancin da ku ka saba kina xaunawa kusa da shi ko???" Imaan ta fashe da kuka a hankali tace "Wllh Ammi na daina haka ai" Ammi bata iya tace komai ba, imaan ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "Ammi ko xa ki kirasa ki masa magana don Allah" wani kallo Ammi ta mata tace "Ba mu gaji haka ba ai, ni ba gantalalliya bace, kuma bari in gaya maki ba a ma namiji son hauka, kawai don bai kula ki ba ki wani damu ki daga hankalinki kisa ma kanki wani cutar ki cuce ni?" Ta rufe fuskarta a kafar Ammi tana shessheka tace "Ammi wllh da gaske Ina son sa" Ammi ta dinga kallonta, can ta dago kanta cikin sanyin murya tace "Ki kwantar da hankalin ki Imaan, amma bana son kina damuwa, kin basa hakuri kuma?" Imaan ta girgixa mata kai, Ammi tace "Toh ki kirasa ko ki masa text ki basa hakuri, sai ke kuma ki kama kanki ba ruwan ki da wani Yaya from now on kin ji abinda nace?" Imaan ta gyada mata kai a hankali, Ammi tace "Kuma ban ce ki gaya ma Inna ba" a hankali Imaan tace "Toh Ammi" Ammi tace "Ta shi mu je ki xuba abinci yanxu" ba musu Imaan ta mike ta bi bayan Ammi suka fita dakin. Karfe shidda Imaan ta tafi kai ma Inna abinci don bata ma son ta je da Magrib ta hadu da Mujaheed, turo baki tayi ganin takalma bakin kofar, ta shiga da sallama ba tare da ta yarda ta kalli wanda ke xaune a parlon ba ta ajiye abincin, Inna na washe baki tace "Toh kin kawo a dai dai kuwa, kawo plate in dibar masa nasan baxai wuce shinkafa ba dai" Imaan ta saci kallonsa lkci daya gabanta yyi mugun faduwa ganin Sadeeq xaune parlon cikin kananun kaya idanuwansa sanye da glasses, suna hada ido ya dauke nasa idon, ta kasa fita parlon, Inna tace "Baxa ki kawo kwanon bane in tashi da kai na" Yana murmushi yace "Kaka da gaske fa na koshi, yanxu muka gama cin abinci da abokaina a gidan cin abinci" Inna ta rike ha6a tace "Toh abincin gidan naku ba dadi ne Bukar har sai ka fita gidan masu abinci?" Sosai Sadeeq yyi dariya yana kallonta yace "Kaka saboda abokaina ne muka je can" Inna ta tabe baki tace "Atoh, na ji ance fa naman aladu suke siyar ma mutane, ni dai da xaka yi hakuri ka daina xuwa idan ma girkin gidan naku ne baka so sai ka dinga xuwa nan xan saka maka a kwano in ajiye, kazamai da masu wari sun yi yawa a duniya yanxu kaje ka ci abinda xai hallaka ka wataran mu shiga uku gaba daya" Shi dai dariya kawai yake Imaan ta juya ta fita parlon.... Dai dai inda suke yawan tsayuwa da Mujaheed ta tsaya, ba a wani dau lkci ba taji foot steps dinsa yana tahowa, yana kusa isowa wajen suka yi ido hudu, yyi slowing pace dinsa amma kuma ba shi da alamar tsayawa, cikin sanyin murya tace "Plss ka tsaya Abbana" Tsayawa yyi ya dawo gefenta ya rungume hannunsa a hankali yace "Toh na tsaya daughter" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta sunkuyar da kai cikin rawar murya tace "Don Allah kayi hakuri ka yafe min" Yace "Inyi hakuri a kan me" da kyar tace "Abinda yasa kake fushi da ni" yayi murmushin karfin hali yace "Aa ban yi fushi ba Imaan" tace "Wlh ka yi, don Allah kayi hakuri wllh hakan baxai kara faruwa ba" Yace "Imaan don Mujaheed yayan ki ne kamar yanda kike yawan fadi ba yana nufin same parent suka haife ku ba so I have all right to get angry, Shi din ba Muharramin ki bane, da nine nace mu fita eatry ni da kudin gaisuwana ke kanki ba yarda xa ki yi ba, not to talk of giving ur meat..." ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Plss kayi hakuri, baxan sake ba, abinda ma yasa ya kai ni wajen ranan ya siya min kaza shine saboda I promise xan taya sa fada ma wata yarinya da yake so cewar yana sonta wai ya kasa fada mata.... Wllh saboda nace ni xan yi ma yarinyar magana ya sa ya siya min kaza don in maya" murmushi Sadeeq yyi yana shafa kansa yace "Ya wuce Imaan... Xan wuce masallaci it's almost time" a hankali tace "Ka hakura?" Yace "Tuni na hakura ai" mu je ki raka ni gate, har suka isa gate babu wanda yace komai cikinsu, yana kallonta yace "Good night" ta gyada masa kai ya wuce ta juya ta koma ciki. Tun daga sannan imaan tayi kokarin dinga avoiding Mujaheed, ko parlonsu ya shigo dama tashi take ta wuce daki ko ta wuce kitchen, part din Inna kuwa kafin yaje xata kai mata abinci ta maxa ta dawo, ana haka har ya rage two weeks su fara exams kuma hakan yyi dai dai da saura sati biyu a kawo lefenta tare da sadaki daga gidansu sadeeq, sosai ta dage da azkar kamar yanda Ammi ta ce mata saboda yawan faduwan gaba da take, Ammi ma ta bata addu'o'in da xata dinga yi tana kuma kokarin tashin ta duk dare tayi sllh. Yau Saturday Imaan ta fito parlor sanye da hijab dinta har kasa hannunta rike da karamin jaka, duk da babu komai fuskarta sai eye pencil da Chappete ba karamin kyau sanyanye tayi ba, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da kallo har ta durkusa kusa da ita tace "Ammi xa mu wuce" Ammi ta d'an yi shiru kafin tace "Kar ki dade Imaan, ko minti goma plss kar ki yi ba mutuncin ki bane, kina yin abinda ya kai ki ki juyo" Imaan ta d'an yi murmushi tace "Toh Ammi in sha Allah" Ammi tace "Ko xa ku dawo napep xa ku hau kin ji abinda nace koh?" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka ta fita parlon, ta nufi part din su Maimoon, a hankali ta bude kofar ta shiga da sallama murya can kasa, Umma ce xaune parlon, sai Mujaheed dake xaune shi ma ya jinginar da kansa da kujera idonsa lumshe, Safeenah ma na xaune parlon tana taunar cingam, Umma tace "Toh ni na ta6a jin rashin lafiya haka, bari Abbansa ya shigo kila idan yyi masa magana xai yarda a dubasa, su dama likitocin nan haka suke da shegen taurin kai sai dai su duba wasu ba dai a duba su ba" Safeenah ta tabe baki tace "Wllh kuwa Hajiya, har ce min yake ba ruwana in daina sa masa ido, Toh ya baxan sa ido ba mijina ba lafiya, ko abinci bai ci fa Umma sai dai coffee da tea mun fi sati a haka" Umma ta rike ha6a tace "Ba lafiya kuwa, bari Abba ya shigo wannan ai ba yi bane" Imaan da ta sunkuyar da kanta ta nufi stairs tace "Ina yinin ku" babu wanda ya tanka ta a parlon har ta wuce sama, Umma ta kalli Safeenah, Safeenah tayi wani murmushi tana kas kas da cingam, Mujaheed tunda ya ji muryarta ya bude ido, ba a dau lkci ba Imaan ta sakko tare da Maimoon dake sanye da hijab ita ma har kasa, suna shigowa parlor Umma ta bi su da kallo, Maimoon tace "Sai mun dawo Umma" Umma tace "Yauwa" Imaan dai bata juyo ba har ta fita, Maimoon ma ta fita, Mikewa Mujaheed yyi yana kallon Umma yace "Bari in je in gaida Inna in dawo yanxu" Safeenah ta mike tace "Ehh bari mu je Umma yanxu xan dawo sai mu fita kasuwan" wani kallo Mujaheed ya dinga mata fuska daure yace "Da can baki san xa ki part din Inna ba sai da nace xan je??" Safeenah ta tabe baki ta nufi kofa tana gyara mayafin jikinta ya bi ta da kallo, imaan da Maimoon na isa bakin titi suka tsayar da adaidaita, Imaan na kallon Maimoon tace "Wllh ban san me yasa gabana ke faduwa ba tun daxu Maimoon" Maimoon tace "Haba dai, to ki dinga addu'a" Imaan tace "Ehh Ina yi" daga haka ta kalli mai adaidaitan da suka tsayar....
Chapter 176 · 0% Book details