Sashe 57
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.Ranan Friday Imaan suka gama exams din first term ss2, suna tsaye tare da Mariya a bakin gate din makarantar tasu ko wannensu na jiran driver, Ummi da Rahma ko fitowa cikin schl din ma basu yi ba, Maimoon dai na tare da wata Kawarta a waje ita ma, Mariya na ganin motar Sadeeq tace "Lahh ya Sadeeq ne ma ashe shi sa ya bata mana lokaci" Imaan dai bata ce komai ba, tunda yayi parking idonsa ke kan Imaan, suna had a ido gabanta ya fadi, siblings din sa duk suka shiga motar, Mariya bata taba sanin Yayan nata na interacting da Imaan ba don Imaan din bata gaya mata ba, Mariya tace "Mu je ku gaisa da shi, shine ya ta6a ajiye ki gida ko baki gane sa ba" Imaan ta d'an yi murmushi kawai, Mariya ta kama hannunta suka nufi gun motar, Mariya tace "Ya Sadeeq frnd dita da ka taba ajiyewa a gida..." Ya cire glass din idonsa Yace "Yea na gane ta" Imaan ta sauke idonta kasa tace "Ina yini?" yace lafiya lau, fatan an gama exams lafiya" tace "Alhmdllh" yace "Toh Allah bada result mai kyau" ta daga kai tana kallonsa tace "Ameen" lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana" ta girgixa kai tace "Aa yanxu driver din mu xai xo" Yace "Ohk then" ta saci kallonsa ya kashe mata ido daya, ta daga ma Mariya hannu ta juya da sauri ta tafi gun Maimoon, Sadeeq ya tada motar ya bar wajen, Ya Yusuf ne ya xo daukansu bayan tafiyar su Sadeeq da kusan minti bakwai, Maimoon na turo baki tace "Ya Yusuf driver din fa?" Yusuf yace "Ya kai su Umma kasuwa, M.A aka ce ya dauko ku tun daxu ya ki, ni kuma ynxu na dawo aiki" Maimoon ta kyabe baki tace "Da dai Anty Farida aka ce yaje ya dauko, jiya fa da yamma har Hayin d'an bushiya muka je daukota taje gidan aunt dinta, baka ga uwar wahalan da muka sha ba ga hold up sai kusan shidda da rabi muka dawo gida" Yusuf yace "Au suna tare har yanxu kenan?" Maimoon tace "Tab, sosai ma, gobe xata koma schl sai kaga tulin shopping da yayi mata" Yusuf ya sake baki yana kallonta, Maimoon ta kyalkyale da dariya tace "Amma fa wllh ya Yusuf kar ka ce masa komai, dama yace kar in fadawa kowa" Yusuf yace "Ae ko kin fada ma kowa tunda kika fada gaban Imaan da Ummi" Imaan ta hade rai tana kallonsa ta madubi tace "Ya Yousuf kamar ya?" Ya wara ido yace "Ke sai ki kwasa ki kai ma inna, Ummi kuma ta gaya ma Umma, saukin abun dai idan magana ya fita an san it's either Imaan or Ummi sae M.A ya ji dadin jibgarku da kyau" Imaan ta xumburo baki tace "Naji dai" Ummi kuwa yi tayi kamar bata ji sa ba dama, suna isa gida Maimoon tace "Dama ya Yusuf ka ja masu kunne ba ruwana idan suka fada ma kowa" wani kallo Imaan ta watsa mata ta fice daga cikin motar tana turo baki ta kara gaba. Satin da aka shiga banda shirye shiryen bikin Seeyamah babu abinda ake a gidan, tun ranan lahadi yan uwa suka fara xuwa daga nesa gida ya fara cika da jama'a, kowa ya xama busy a gidan barin Umma da Anty, Ammi kam baya baya ta dinga yi, tun a ranan lahadin dama ta kai nata gudunmawarta na tsadaddun manyan bedsheets biyu, da set din food warmer shi ma biyu masu kyau sosai, a walakance Umma ta dubi kayan aka bar su a nan parlorn. Ranan laraba Abba ya ba su Maimoon kudin gyaran gashi da lalli a kai su Saloon, Har xa su fita ya dakatar da su ya ciro wani dubu biyar din yace "Na mance ban bada na mamana ba, gashi nan ta shirya ita ma ta je" Fita suka yi su hudu Ummi na cewa su yi wucewansu kawai don Imaan ba xuwa xata yi ba, Maimoon tace "Ba ruwana Abba cewa yyi mu je mu kira ta" A balcony suka tadda Anty tana magana da wa enda xa su yi girkin biki a biya su, Mujaheed ma na xaune balcony din sai Yusuf dake tsaye, Anty tace "Saloon din xa ku yanxu" Maimoon tace "Anty Abba yace mu je da imaan" Anty tayi wani dariya tace "Wace Imaan din tab, amma ku je dai ku ji abinda xata ce" Imaan na dakinta Maimoon ta shigo parlor, nan ta sanar ma Ammi abinda Abba yace Ammi ta kira Imaan, tana fitowa Ammi tace "sai ki dau Hijab ku wuce saloon" sosai gabanta ya fadi ta marairaice tace "Saloon kuma Ammi, aa ni dai xan wanke gashina da kai na" Ammi tace "Kee! dau Hijab ki fice min parlona, dama idan baki gyara gashin nan ba yau kar ki dawo min gidan nan" Imaan fa fashe da matsanancin kuka tana kallon uwar tata, ganin Ammi ta mike ta shiga daki da sauri ta dau Hijab dinta ta fita, Maimoon ta bi bayan ta tana dariya kasa kasa, Anty na ganinta tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" cikin kuka tace "Anty ni fa gashina bashi da wani datti kawai combing dinsa ne bana yi" Anty tace "Toh mu ga gashin" tana shesshekar kuka ta cire Hijab din ta cire hulan kanta, Yusuf ya dauke kai bai son dariya ta fara wani sabon kukan, ga dai gashi har gashi amma duk an cukuikuye shi waje daya, Anty tace "When last kika wanke gashin" a hankali tace "Ranan nan" Anty tayi murmushi kafin ta ce komai Mujaheed ya mike fuska daure yace "Mu je in kai ku saloon din" Ta fashe da sabon kuka xata koma bayan Anty ya ja ta sai gun motarsa, Yusuf yayi murmushi yace "Da yake Umma bata nan ba" Su Maimoon duk suka shiga motar bayan ya tura Imaan ciki, Suna isa saloon din Imaan ta hadiye kukan da take barin da taga yan mata kala kala cikin saloon din, Ita Mujaheed yasa a fara gyara ma gashin, da ruwa mai dumi sosai yace a wanke mata gashin nata bayan an sa mai, banda turo baki bbu abinda take tana runtse ido don ba daman kuka ga yan mata kar su mata dariya, lkci daya gashinta ya dawo sak na Indians sai sheki yake, ganin an kusa gama mata ya kalli kannin nasa yace "Sai ku samu napep da xai maida ku gida, coz I am a driver to none of you" daga haka ya fice saloon din, duk suka bi sa da kallo. Sai bayan magrib suka shigo gidan don har da lalle suka yi, dama Imaan direct part din inna ta nufa tun daga bakin kofa ta cire Hijab din jikinta ta shiga tana murmushi tace "Inna..." Inna tayi mitsi mitsi da ido tana kallon gashin nata tace "Ikon Allah kin ganki kin fito sak mace ko?" Imaan ta xaro ido tace "Toh da ni na miji ne?" Inna tace "Idan ba kallon isuhu nake maki wani lkcn ba shegiya nake" Imaan ta fashe da dariya har da kwanciya kan kujera, Inna ta kalli Mujaheed dake cin abinci tace "Ko kai baka gani ba Mujaheed?" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta mike xata shiga daki Inna tace "Dawo nan ana ma yar uwar ki gyaran jiki tunda can bangarensu ya dawo kamar wajen cin kasuwar laraba" Imaan tace "Anty Seeyama" Inna tace "Ehh kema da dai Allah ya fiddo maki da mijin nan kiyi aurenki da wuri ki haifi kanninki da uwarki taki haifo maki" Imaan ta hade rai tace "Yar karama da ni xaki ce min aure?" Inna ta kalli Mujaheed tace "Don Allah Mujaheed Imaan bata isa aure ba yarinyar da ke al'ada? Ga kirjinta cike da dukiyar fulani" Murmushi Mujaheed yyi kansa a kasa yana cin abincinsa, Imaan ta harari Inna ta juya ta nufi kofa inna tace "Ke kika sani, ni ba ruwana wllh, Allah na tuba lalurorin ki na duniya ma ai tsaye yake da kafafuwansa gun d'a na, ba gwara kiyi auren ko Bukar xai huta da kashe kashen kudi kije can kuma mijin shi ma ya d'an dana ukubar" Washegari alhamis Imaan ta tashi da ciwon ciki ga bak'i a part dinsu balle tayi raki yanda ranta ke so, duk magungunan da ta sha ba wanda taji ya mata, ta lallaba da kyar ta tafi bangaren inna, ita din ma dai parlon nata duk tsofaffin kawayenta ne a xaune, imaan ta gaishesu da kyar ta shige bedroom dinta ta kwanta, lkcn Azahar nayi dama inna ta lallabo ta shigo dakin ta sa ma bandakinta makulli don ba wanda xai shiga balle ya mata kazanta duk me son yin alwala ga pampo can ta bude, idan kuwa xai kama ruwa ne to yaje sashin masu biki, ganin juye juyen da Imaan take duk ta hada xufa duk da iskan fankan dake dakin ta wani xaro ido tace "Ke lafiya meye hakan, ni fa ba ruwana idan baki da lafiya ne ki tafi bangarenku kada a gigitani a nan, meye wani juye juye kamar macijiya a kan gado na" Imaan ta fashe mata da kuka tace "Wayyo cikina ke min ciwo" Inna tace "Auzubillahi, to rufa min asiri ki sakko ki tafi gun uwarki ba ruwana" Cikin kuka tace "Akwai mutane a can" a fusace Inna tace "Mutanen banxa ina ruwanki da su, idan wani abu ya sameki maganin me mutanen xa su yi banda su cika mu da surutu, dama ba komai ya kawo su ba sai kwadayin d'an shinkafar da xa a raba a kwano da kaji banda haka wani ma anyi shekara goma ba a gansa ba, ki tashi ki tafi tasan yanda xata yi dake idan ma asibiti ne ta kai ki, idan ko ba haka ba idan ban sa an dage bikin ba ace bani ba, biki ya fi rai ne" da kyar Imaan tace "Ni fa marana ke min ciwo" Inna tace "Wai jini?" Imaan ta gyada mata kai, Inna tace "Toh shi kuma wanda kika yi