← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 207

Sashe 126

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788Mujaheed na dinning a xaune Maryam ta sakko downstairs tare da Maimoon, yana kallonta yace "Maryam" ta kalli direction din sannan ta tafi tace "Sai yanxu kake breakfast?" Yace "Ehh... xauna" ba musu ta ja kujera ta xauna, ya ajiye cup din coffee dake hannunsa yace "When did she tell you is the birthday?" Maryam ta langwabar da kai tace "She told me nothing about it again, tun ranan bata gaya min komai ba" Yana kallonta da kyau yace "Karya kike Maryam" ta xaro ido tace "Karya kuma ya M.A, bana ma tunanin Birthday din na nan don bata ce min komai ba, kuma kaga gashi ana ta hidiman biki, kila ma ta manta idan ma Birthday din na nan" yace "Make me a promise Maryam" tace "What promise" yace "You will watch her movement keenly" dariya tayi tace "Ohk then, amma kuma abun mamaki ina ma xata je ana biki" Yace "Just do what I say" tace "Toh na ji" yace "Good tashi ki tafi" Mikewa tayi ta bar dinning din, ya dau coffee dinsa ya ci gaba da sha a hankali. A bedroom Maryam ta tadda Imaan dake ta shiryawa slowly wai don a tafi a mance da ita, Maryam tace "Naga alamar baki son xuwa saloon din nan imaan" kamar xata yi kuka tace "That's just it, ni scalp dina ma ciwo yake min, aje ayi ta ja min gashi kaina ya fara min ciwo, ni dai kawai ku tafi kice masu baki gan ni ba" Maryam tayi dariya tace "Kai Imaan, da ni ke da irin gashin ki ai duk sati sai naje saloon" ita dai Imaan bata ce komai ba, Sadeeq ne ya fado mata ta tuna wata rana da daddare suna waya yake ce mata shi dai yana son dogon gashi, haka kawai taji tana ma son xuwa saloon din, Maryam ta gama yafa karamin veil din abayar jikinta tace "Ohk then xan ce masu ni ban gan ki ba" Imaan tace "Ko kuma ma dai kawai bari mu je, idan ya so ana gama mana sai mu tafi mu siya abinda xa mu siya a shopping mall, koh?" Maryam ta wara ido kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ehh haka ne kuma" Imaan tace "Kinsan fa gobe ne birthday din kuma I have to give him the gift this night" Maryam tace "Au haba, same day da bikin Ya Mujaheed kenan?" Imaan tace "Sure" Maryam tace "Tabdi, Toh yanxu ya xa ki yi? Ga biki ga birthday" Imaan tayi yar dariya tace "Ni ina ruwana da biki, Ai na riga na ce ma Daddy xan je gidan Gwaggwon Ammina gobe da safe" Maryam ta marairaice tace "Tafiya xa kiyi ki bar ni yanxu?" Imaan tace "Of course no, tare xa mu ai" Maryam ta langwabar da kai tace "Yanxu haka xa mu yi missing bikin ya MA, gashi ma anjima da daddare xa ayi dinner fa" Imaan tace "Aa idan kinga xaki tsaya ki tsaya ni dai ba ruwana" Maryam tayi murmushi tace "Aa mu je gidan grandma din dai..." Imaan tace "Better" a tare suka fita dakin, Ammi dake parlor ta nuna ma Imaan kan kujera tace "Ga kayan ku nan ki shiga da shi ciki yanxu aka kawo" Imaan ta dauko ta kai daki sannan ta fito, sosai gaban Imaan ya fadi ganin Mujaheed parking space a tsaye, tun da ya kalleta sau daya ya ci gaba da danna wayarsa, ta dauke kai ta isa gun motar da ake kai su makaranta tana kallon Maimoon, Maryam kuma ta tafi gun Mujaheed tana murmushi tace "Our handsome groom..." Imaan ta tabe baki tana kallon Maimoon tace "Ina Drivern da xai kai mu Saloon din?" Maimoon tace "Ya Mujaheed yace xai ajiye mu shima fita xai yi yanxu" Xaro ido imaan tayi tana kallonta, ta hade rai bata dai ce komai ba, Ummi ta fito bangarensu tana kallon Mujaheed tace "Rahma xata taho daga baya, wai xa su fita tare da Umma yanxu" bude driver seat Mujaheed yyi ya shiga yana kallon Maryam yace "Har da ke xa aje gyaran gashin?" Ta xaro ido tace "Eh mana" murmushi yayi yace "Toh shiga..." imaan ta bi bayan Maimoon tana cika tana batsewa ta shiga back seat, Ummi ma ta shiga. Suna isa saloon din yyi parking yana kallon Maimoon ta madubi yace "Since babu mutane sosai a saloon din xan jira ku gama" Maimoon ta washe baki tace "Tohh mun gode Ya Mujaheed" a fusace imaan ta fice a motar ta bar door din a bude cikin tsawa yace "Keee" juyowa tayi da sauri, fuska daure yace "Xo ki rufe min mota kada in sauka in xane ki yanxu" Ganin babu wasa tattare da shi ta dawo kamar xata yi kuka ta rufe motar ta juya ta shiga saloon din, Maryam tayi murmushi tace "Ya M.A kai dai kawai kayi tafiyarka ko motorcycle din nan mai kafa uku sai mu hau ya dawo da mu gida" Mujaheed yace "Sauka kije kiyi abinda ya kawo ki nan" Yar dariyar yake tayi ta bude motar ta fita, ita kanta bata ji dadin jiransu da yace xai yi ba, shikenan ya ruguje masu plan. gyara ma Imaan gashi ake amma gaba daya hankalinta na gun lekan waje don ganin ko Mujaheed ya canxa mind dinsa ya tafi, amma duk ta leka sai taga yana nan, ta ji kamar ta kurma ihu, a haka har aka gama masu gyaran gashin aka fara masu lalle a hannu, Maimoon ce ta fara fita bayan an gama masu, Ummi ma ta fita, Maryam na kallon Imaan a hankali tace "Kinga yayi spoiling plan dinmu ko, yanxu how are we going to get the gift?" Imaan ta rasa abinda xata ce mata, can Maryam tace "You know what, kawai mu koma gida, dama akwai few abubuwan da nace ma mum xan siya a Nigeria, muna isa gida yanxu xan amshi card dinta mu fita daga can ma sai in siya abubuwan da nace" Sosai hankalin imaan ya kwanta, ta d'an yi murmushi tace "Toh shikenan, har naji dadi" tashi Imaan tayi suka fita saloon din din Maimoon ta bada kudin kafin su fita, tun da suka fito Mujaheed ke kallonsu ta madubi har suka iso gun motar, ganin Ummi xaune a gaba Maryam ta shiga back seat tare da Imaan, tada motar yayi ya dau hanyar gida. Suna isa gida Mujaheed yayi parking ya kashe motar, Imaan ta fita ta dau hanyar apartment dinsu, ya gyada kai yana bin ta da ido ta madubi... Maryam tace "Mun gode ya M.A" bai amsa ta ba tayi wucewarta tana murmushi. Maryam na gaya ma mama Hadiza xata fita shopping ta hanata wai bayan biki sai su je, ba ynda Maryam ta iya ta koma dakin Imaan a sanyaye ta sanar mata abinda mamarta tace, imaan ta rasa yanda xata yi, Maryam tace "Toh ko mu bari kawai gobe da safe idan mun fita xa mu gidan grandma dinki sai mu shiga mu siya" a hankali Imaan tace "Noo yau ya kamata in basa, yau nake son in basa" Shiru Maryam tayi, can tace "Ba xa mu je dinner ba anjima, kawai mu jira sai mutane sun cika wajen sai in sulale da makullin motar Yaya Yusuf mu je mu dawo" Imaan ta xaro ido Tace "Ni fa ban yi niyyar xuwa dinner din ba wllh" Maryam tace "Ae ko gwara ki daura niyyar xuwa yanxu, don that's the only way out" Imaan tace "Toh shikenan" Ana idar da Magrib duk aka gama shirin tafiya wajen dinner, duk wannan abun Mujaheed na lura da su keenly, kuma yaki tafiya duk da yanda abokansa suka dinga takurasa su wuce saboda amarya har ta iso wajen, Maryam dai ta dinga bin Yusuf wai ya bata makullinsa tayi driving din, daga karshe dai babu yanda ya iya ya bata, da kyar imaan ta saka gyale a kan ankon su na Dinner da Daddy yayi masu gaba daya gidan, tayi kyau har ta gaji amma sai wani nonnokewa take abunka da ba sabon ba, Maryam ce tayi driving din nasu xuwa hall din da xa ayi dinner din.... Waje ya cika makil da masu kudi sai ruwan naira ake tun kan a fara komai, Fara'a gun umma ba a cewa komai, Inna na xaune tare da ta rasulu a table guda duk sun sha atamfar England an yafa gyale sun tsuke fuska suna kallon ikon Allah, Imaan na shigowa hall din tare da su Maryam ganin Inna da ta rasulu ta rufe fuskarta gyalen jikinta ta dinga ba66aka dariya, suka nemi waje suka xauna, kallon inda amarya da ango ke xaune tayi, taga Safeenah da tayi wani kyau irin na aljanu sai sheki gwalgwalan jikinta suke, kayan jikinta kam dama ba acewa komai, ta kalli Mujaheed da ya sa lafiyayyen farin gezna sai walkiya yake, hada ido suka yi da shi tayi saurin kauda kai, Imaan ta kalli Maryam tace "Ni dai xan koma gun su Inna kafin mu fita" bata jira cewar Maryam ba ta mike ta tafi gun su Inna Mujaheed ya bi ta da ido.

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter 126 · 0% Book details