← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 207

Sashe 191

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaya ma Hajiyar Marafa ba, kin santa da xuciya ki bar ni da shi kawai, kema kinsan haka nan baxai mare ki ba, wllh sai yayi da ya sanin abinda ya aikata, muna nan da ke" Safeenah ta yi tsaki bata ce mata komai ba, Umma tace "Tunda shawarar da kika bada aka yi amfani da shi kwanaki bai yiwu ba yanxu baki da wata shawarar da xa ki kara ba mu?" Safeenah tace "Don an kai lefe da kudin aure ba yana nufin anyi aure bane...." Shiru tayi ta bude jaka jin wayarta na ring, ta fiddo wayar tana kallon screen din, Kallon Umma tayi tace "Shi yake kirana" Umma ta xaro ido tace "Haba?? To dauka ki ji uban me xai ce maki" Safeenah ta wani daure fuska ta daga kiran ta sa handsfree tayi shiru, sallama yyi cikin sanyayyen muryarsa, cike da masifa tace "What did u want from me Mujaheed?" Ya d'an yi shiru sannan yace "I want to say I am sorry, kiyi hakuri tsautsayi ne" ta fashe da kuka tace "Tsautsayi ka daga hannu ka mareni a dakina a kan wata can, kuma a gabanta??" Yace "Nace kiyi hakuri, and take note Imaan ba wata bace kanwata ce, I see no reason xaki daga hannu ki mareta in kyale ki..." Safeenah ta bude baki ta xaro ido tana kallonsu Umma, tace "Wato kirana kayi ka sake min rashin mutunci kenan Mujaheed?" Murya can kasa yace "Not at all Safeenah, Kinsan Imaan ba lafiya sosai gareta ba, kuma ga grandma dinmu a gidan, da ban yi haka ba anything can happen... ni nasan halinta ke baki sani ba, so don't ever, I mean ever.... try giving her a bad look talkless of you laying ur hand on her face, xan iya maki fiye da abinda kika yi...." Sai kuma ya kwantar da murya yace "Yanxu dai I didn't call to talk long plss kiyi hakuri da abinda ya faru idan ma kince xa ki rama shkkn sai ki rama a kai na, but If you try touching my lil sis I will not take it likely with u" Bude baki Safeenah tayi da mugun mamaki tana kallon Umma da ta gwalo ido tana sauraransa ita ma, a hankali Safeenah tace "You called to warn me Mujaheed?" Yace "Not at all, na kira ne in baki hakuri, and tell me where you are now??" Umma tayi kasa da murya sosai tace "Kice kina gida wajena" Safeenah ta tabe baki fuska daure ta ki cewa komai, yace "Am asking kina Ina" alama umma ta dinga mata ta gaya masa tana can gida, ta harareta ta dauke kai tana wani cika tace "Ina gidan ku" Mujaheed yace "Good I am happy baki tafi gida ba, later da yamma xan shigo in sha Allah, I need rest now..." Daga haka ya katse wayarsa. Safeenah ta ja wani tsaki tana kallon Umma a fusace tace "Ni dai Hajiya kin bari kawai na tafi gidanmu Hajiyarmu ta san abinda ake ciki, aure ko wata uku ba ayi ba an fara mari na sbda wata shegiya, dubi fa hakuri ya kira ya bani amma dubi irin maganganun da ya dinga min da warning?? Infact wai ma me yasa baya ji da kanninsa haka yanda yake ji da ita?" Umma ta tabe baki tace "Uwar ce ta asirce min shi, tun yarinyar na yar karama tana yar yaye yake bauta da ita ke kya ce don shi aka haifota, nayi nayi in rabasa da ita amma inaaa, da yake kinsan lkcn a wajen kakar tasu yake, ita kuma yarinyar kullum sai an kai ta can sai ya maida ta gida da yamma, idan ba karyar kakarsu ba ma cewa tayi da sunansa ta fara magana, amma duk karya ce wllh, a haka dai ta taso ta makalkale ma d'a na sai kice shine Abubakar ubanta, idan kuwa xai dawo hutu gida daga Uk uban tsaraban da yake yo mata hankali baya dauka, kanninsa ko quarter dinsa basa samu wllh, wai ma don abun ya ragu sosai yanxu, ae ba karamin tashi tsaye nayi ba gaskiya, ban yi da wasa ba kam, kwanaki da dadewa fa mijin da Seeyama ke aure yanxu ya so hada imaan din da, kinsan abokinsa ne kuma yaron ga kudi ga hankali amma sbda shi shashasha ne wai da Imaan xai hada sa, ni ko na ruguje xancen gaba daya, shine yaron ya dawo ma Seeyama, yanxu wnn auren ma da ake son a mata shine gaba a kan komai ina jin, kuma bbu mamaki ya ma san yaron Bulasawan..." Safeenah da ke ta kallon Umma tace "Toh ni dai gaskiya tayi aurenta ta tafi gidan mijinta ta kyale min miji haka" Umma ta bude baki tace "Tayi aure kuma? To ai tunanin xata auri yaron Bulasawa ne yasa take raina mutane take ganin ita wata ce, wllh shi yasa take maki kallon hadarin kaji, kallon kowa take kasa da ita sbda tana tunanin yaron Bulasawa ne xai aureta, amma bata san she is mistaking ba, wllh wllh ba mijinta bane yaron in dai ina numfashi, ke kinsan ko gaisheni yarinyar nan da kike gani bata yi kuwa?? Uwarta kuwa jin ta take ita wata ce yanxu a dole ga ta surkar Bulasawa, to xa su kwashi kunyar su kuwa a hannu wllh ba cika baki ba" Safeenah ta tabe baki tace "To ae don an kai sadaki da lefe an sa rana ba shine yake nufin an daura auren ba, in dai ni take ma wani gani gani wllh ta tari aradu ba gamo... Sai na kunyatata in ga ta tsiya in ga karshen auren nata da shi Sadeeq Bulasawa din" Umma tace "Atohh, ni dai dama nace idan aka yi auren nan to fa ban haifu cikin uwata ba, daga ita har uwarta da kakarta sai sun kwashi kunyarsu a hannu ina kallo" Hajiya Saude tace "Kuna ta surutu ni ko har na gama yanke shawarar what next... Kuma in Allah ya yrda naji kamshin nasara...." Umma ta kalleta da sauri tace "Toh ba mu mu sha" Hajiya Saude tace "Amma duk da haka sai mun koma wajen mutumin nan ko xuwa gobe" Bayan Magrib Mujaheed yayi parking kofar gidansu ya fito ya kulle motar gaisawa suka yi da mai gadi dake bakin gate, Mai gadin na kallonsa yace "Likita ba lafiya ne" Mujaheed na kallonsa yyi murmushi yace "Alhmdllh, na ji sauki" daga haka ya shiga compound din, direct part din Inna ya nufa walking slowly, a hankali ya murda kofar parlon ya shiga, ido hudu suka yi da Imaan dake xaune parlon tare da Inna da ke ta fiddo kayan cikin akwatunan lefen da aka kawo bakinta har kunne, Ta Rasulu ma sai aikin fiddo ubansun kayan take tana cewa "Toh ga dai kaya ba laifi an xuba karyar naira, ko da yake suna da shi ne, Ni fa nasan har uwar Bulasawan nan a da wllh, don akwai wata makociyata kawar kanwarta da suke uwa daya tana ma uwar Bulasawan aikatau, lkcn ma kudin bai bunkasa haka ba, toh sai makociyar tawa ta ja ni wataran muka je gidan kawar kanwarta wai xata kai mu gidan kakar shi mijin Imaan wato uwar Bulasawa, sunan uwar tasa Hajiya Salamatu, tana nan wata doguwa fara, duka duka bata fa wuce mu ba amma kirkinta ragagge ne...." Inna dai sai kallonta take kasa kasa, ta Rasulu ta tabe baki tace "yo ragagge mana, a lkcn Ina goyon Shamsu daga ya mata fitsari a cafet, ga abinci mai lafiya da xuka xukan kaji an xubo mana xa mu ci in gaya maku abincin da ban ci ba knn don matar nan cewa tayi in tafi gida in canxa masa kaya xarni ya isheta, nan ko bata san har da kashi yyi ba ina ta boyewa ne har sai mun ci abincin, ni dai har da d'an kwalla na na bar gidan ina dukan shamsu, kafin in dawo kuwa su shafa'u suka side kwanon tass da ke kinsan dangin mayu ne, ni dai abincin ko a halshe na" Maimoon dai sai taya su fiddo kayan take bata ko kalli ta Rasulu ba, Duk suka kalli Mujaheed da ya shigo parlon ya tsaya yana bin akwatunan da kallo, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed takwarata tayi goshi wllh, ko atamfar dubu ashirin Ina jin babu a nan, gwalagwalai kuwa mun kirga biyar da ta Rasulu, to me xance ma Allah banda in gode masa?" Imaan dai sai danna wayarta take, Mujaheed yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Inna tace "Ameen, kuma kayi hakuri da abinda iyayenka suka maka, ka dai fi su nesa ba kusa ba, in sha Allahu idan Allah yasa aka daura auren nan lafiya kai xaka kai Imaan har dakinta kayi mata fada sosai sannan mu taho gida mu bar ta" Dariya Maimoon ta dinga yi tana kallon Imaan da taki dago kanta, Inna ta tsuke fuska tace "Ke ba batun dariya bane, magana ta gaskiya shi xai kai ta gidanta... Ke kinsan wahalar da yyi da ita ne kuwa" Ta Rasulu tace "Wahala kuma ai ya tashi a banxa tunda ba shi xai aureta ba, kyansa ace wannan uban shakuwar da suka yi kawai ya aureta suje can su xauna tare, abinda ma ya fi kowa saninta a duniyar, ba shikenan sai su haifo santala santalan 'ya yansu su xube ma Aisha tayi ta bari barin da bata yi ba da, ku dai xumuncin ku duk kame kame ne ba shi da wani karfi Allah na tuba, Banda haka ba sai ayi tuwona maina ba ko don Rukayya ta hadiye xuciya ta mace, ita kenan fa gare Bukar a duniyar...." Tagumi Inna tayi kamar xata yi kuka tace "Ni dai naga abinda ya isheni ni Asabe... Wa ya gayyato min wannan mata??? Huuu gaskiya ta Rasulu kin lalace, ke kinsan uban sa6on da kika buga yanxu ki ja mana girgixan kasa kuwa? Kai wasu dai kyansu dawanau wllh" Ta Rasulu tace "Sa6o don nace da Mujaheed ya auri yar uwarsa Imaan? Ke dai baki son gaskiya, kuma baki tsoron Allah, Asabe kinyi watsi da tsoron Allahn ki tun tale tale, kai tun kina gidan Alhaji isuhu, kawai jin ki nake idan kince wasu basu
Chapter 191 · 0% Book details