← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 207

Sashe 124

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number 07087865788Maryam tayi dariya tace "Kai Imaan haka kike da son jin abinda bai shafe ki ba?" Imaan ta marairaice mata tace "Ni dai ki gaya min" Maryam na murmushi tace "Ke ba ko ina mu ka je ba, kawai dai ya kai amaryar tasa plazan da xa ayi mata dinkunan bikin ne ya bada kudi, sai kuma gold na rings guda uku da ya siya mata for the wedding, sannan muka koma gida muka ajiye ta, after that muka je kasuwa siyo drinks da Ummansa tace ya siyo, sai flasks da bedsheets da xata yi souvenir ma kawayenta....." Imaan ta ja tsaki tace "Toh meye na cewa kar ki gaya min, ko ni ina ruwana?" Maryam tace "Ke wasa nake kawai Inna yace kar in gaya ma amma ba ke ba" Imaan ta mike tana goge jikinta tace "Toh shine xa ki ce saboda ni ku ka je inda ku ka je?" Maryam tace "I am just pulling ur legs, kin taba ganin amaryar tasa kuwa?" Imaan tace "Ehh na taba ganinta a gidansu" Maryam tace "She is beautiful but her fairness isn't natural" Imaan tayi dariya tace "Artificial ne kenan" Maryam tace "Probably... And she isn't friendly, she didn't even acknowledge my present sosai, kamar bata son mutane, sai kin ga ma yanda ta amsa min gaisuwan da na mata, she just shunned me..." Imaan tace "Tohh ba sai ki fasa bin su ki dawo gida ba, Toh me yayan yace?" Maryam tace "He couldn't say anything to her, amma shi ma naga bai ji dadi ba, coz he even introduced me to her again, amma ta ki cewa komai" Rai bace imaan tace "Toh wai me yasa baki dawo gida ba??" Maryam tace "Ae ban san hanya ba, beside I am not with money, ga shi in gaya maki sai wani shagwaba take masa a mota, shi ko a cikin magana goma bai fi ya amsa mata uku ba" Imaan tayi dariya tace "That's their problem" Maryam tace "Yea least I forget, na yi maki deciding abinda xa ki siya ma Bf din ki for his birthday" Imaan na shafa lotion dinta tana kallonta ta madubi tace "And what's that?" Maryam tayi murmushi tace "But wait... did he invite u for the birthday party?" Imaan ta gyada mata kai, Maryam tace "Kuma xa ki je?" Langwabar da kai Imaan tayi a hankali tace "Toh I haven't decided yet, ban sani ba tukun" Maryam tace "Toh after ur decision xa a bar ki kije a gida kuwa?" Imaan ta xaro ido tace "Dama wa xan gaya ma?? Tab... Am telling nobody" Da sauri ta dawo kusa da Maryam ta xauna tace "Plss Maryam wannan ya xama sirri tsakanina da ke, Kinga even Maimoon da ta ke kawata ma ban gaya ma ba, don Allah kar by mistake ki ce ma Ya Mujaheed anything about the birthday" Shiru Maryam tayi tana kallonta, hankali tashe Imaan tace "Ko dai har kin gaya masa?" Maryam tayi yake tace "Haba dai why will I, of course ban gaya masa komai ba" Imaan ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Maryam tace "May be... A day to the birthday sai mu fita babban shopping mall in nuna maka abinda ya kamata ki siya masa" Imaan tayi shiru tana tunani, can tace "Toh Allah ya kai mu" kayan baccinta ta saka ta hau saman gadon ta dawo kusa da Maryam tana kallon abinda take yi a laptop dinta. Slowly ranakun suka dinga tafiya har ya rage saura kwana biyu bikin Mujaheed da Safeenah, gida ya cika da Yan uwa da abokan arxiki, matan kawu Bala, Hansai da yaranta kai duk yan uwa dai an cika gidan barin part din su Umma, duk inda kaga Imaan toh xaka ga Maryam a gidan kamar da can sun saba da juna sosai, seriously Mujaheed ya sa ma Imaan ido a gidan, ita kuwa ko sanin yana yi bata yi ba. Da yamma Imaan na parlon Inna tare da Maryam sun kawo mata abinci, sai bin Inna dake ta neman makullin bandakinta suke da kallo, duk ta hada xufa ta wani tsuke fuska, komai sai da ta daga a parlon amma babu makulli babu labarin sa, Mama Hadiza ta fito daga daki da alamar ita ma neman makullin take tace "Toh wai ina kika ajiye makullin Inna?" Inna tace "Ke ki rabu da ni don Allah, nasan inda na ajiye xan ta neme neme, da ba don rubabbun dake shigo min nan ba har xan wani kulle bandaki kamar warce ta ajiye gwalagwalai a ciki har shegen makullin ya bata?? Ni dai ba ruwana a ma daina xuwa min nan gaba daya, tunda ba ni ke aurar da mutumi ba" Dariya Maryam ta dinga yi Inna ta daga kai daga duken da take tana kallonta, Sallama aka yi bakin kofa Inna ta mike tsaye ta amsa sallaman, Ta rasulu ta shigo tana kyabe fuska, Rahma ta ajiye mata karamin jakarta ta juya ta fita, Inna na washe baki tace "Sannu da xuwa Ta Rasulu kinga na rasa inda na jefa makullin bandaki, gudun kar a shigar min bandaki na kulle na saka makullin a bakin zani to yanxu gashi ko sama ko kasa" Ta rasulu tace "Toh ai gwara da aka nema aka rasa gaba daya, kinga bayan bikin sai a balle kofar kawai, don wani na iya xuwa ya maki dadin baki ki kunce makullin ki basa, mutane dai basu gaji mutunci ba, kinga yanda aka 6ata tsakar gidan da shinkafa ga yara jage jage kamar daga kauye, ni dai ba kowa ma ya kamata a dinga bari yana shigowa ba ma wllh, sai kace ba bikin yan gayu ba" Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni, kin ji wata fitina koh, Kai mutane dai jarababbu ne, kice tsakar gida na nan duk wari?" Ta rasulu ta tabe baki ta wuce cikin dakin tace "Ae kuma sai ki yi, abinda tsoron Allah yayi karanci a xukatan mutane yanxu" Inna tace "Toh ni kuwa xan je in basu hakuri su rufa mana asiri kada gidan 'ya yana ya lalace mu shiga uku, sannan biki dai ba ace a xo da yara ba" Mama Hadiza ta leka dakin ta gaida ta rasulu sama sama ta fita parlon gaba daya, Imaan ta tabe baki xata tashi Inna tace "Toh ke kin gaida ta rasulun ma kuwa" daga cikin daki ta rasulu tace "Ina fa ta gaida ni tana kallona ina kallonta, yaran yanxu kam sai ka kyalesu, mu dai muna masu fatan alkhairi Allah kuma ya basu miji na gari, har wannan figaggiyar ta kusa da ita ma ni bata gaisheni ba ai" Imaan ta gaida ta daga inda take tana turo baki ta mike ta fice a parlon, Maryam ta mike ita ma ta gaidata ta fice Inna na cewa "Iyayenku ku ka ma haka ba mu ba wllh" Daren ranan Daddy ya iso daga Abuja, bayan ya huta suka d'an taba hira da Mama Hadiza da yake a part din ta sauka, sannan ya fita don xuwa ya gaida Inna, Imaan ta bi bayansa da sauri, bayan sun sauka balcony yana kallonta yyi murmushi saboda yasan akwai abinda take son gaya masa kenan tunda ta biyosa, yace "Do you need anything Imaan..." A hankali tace "Daddy kaga mutane sun yi yawa a gidan nan plss ni dai ina son xuwa gidan gwaggwo in xauna har a gama biki in dawo Saturday" Da mamaki yace "Bikin yayan naki kuma Imaan?" Tace "Daddy I will be very uncomfortable, ai da rana xan wuce gidan gwaggwo din ba da safe ba" Yace "Toh ita kuma Maryam fa, won't she be lonely" Imaan tayi dariya tace "Ae tare xa mu je daddy, ita ma tace min she's already uncomfortable tun daga jiya da mutane ke ta xuwa" Murmushi Daddy yyi yace "Ohk then sai ki gaya ma Ammin ki" Imaan ta wara ido cike da jin dadi tace "Toh Daddy nagode sosai, ai dama Ammi...." Shiru tayi hango Mujaheed da ta yi yana tahowa daga part dinsu, Daddy ya kalli inda take kallo, ganinsa ya tsaya har ya iso inda suke, da ladabi Mujaheed ya gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya shirye shirye M.A" Murmushi kawai Mujaheed yayi, Imaan tayi wucewarta gaba ta bar su tana cinno baki, da sallama ta shiga parlon inna, Ta Rasulu na xaune kan darduma ta daura kafa daya kan daya ta rungume hannu tana sakace hakori, Inna kuma na xaune kan tabarma ita ma ta daura kafa daya kan daya, Umma na parlon xaune ga bucket cike da cin cin da alkaki da ta shigo da sai kallon ta Rasulu take kasa kasa, Ta Rasulu ta kyabe baki tace "Yo ai duk matsiyata ne Asabe, ni shi sa ba ruwana da kowa wllh, ba ruwana" Inna tace "A'a dama fa nasan a wajensu tsiya ya kare, ni ina ruwana da su Ina ta kai na, oh oh wlh" Ta Rasulu ta kalli Imaan sannan ta kalli Inna tace "Matar nan na amfani da iccen da kika bata kuwa?" Inna xata yi magana Daddy ya shigo da sallama Mujaheed na biye da shi a baya, Inna tace "Allah dai ya baku lada wannan hidima da kuke ta yi da Mujaheed, ko kudin jirgin da ka kashe yau ma ai xaune yake da kansa, Allah dai yasa ya ji k'an ku nan gaba, yayi ma imaan abun kirki ranan bikinta" Daddy ya xauna yana murmushi ya gaisheta sannan ya gaida Ta Rasulu, Umma ta gaishe sa sama sama, ya amsa yana tambayarta taro, ta Rasulu ta rike ha6a tana kallon Daddy tace "Ohh Bukari kana nan dama, rabona da kai fa tun da ka xo daurin auren ishaq" Daddy yace "Ina nan Baaba, sai dai yanxu a Abuja nake" Ta Rasulu tace "Toh Allah yayi maku albarka, ya kare ku sharrin masu sharri, ya sa ku gama lafiya da mu, ya ba matanku ikon yi mana biyayya yanda ya kamata" Yana murmushi yace "Ameen Baaba" Mujaheed ya gaida ta Rasulu, ta Rasulu tace "Sannu ango, amma kuma duk naga ka rame baka cin abinci ne?" Inna tace "Ke ma dai da wata magana ta Rasulu, ina
Chapter 124 · 0% Book details