← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 207

Sashe 151

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu, Mujaheed dai ya koma ciki ya dauko makullin mota ya fito ganin har Inna ta fice ya bude motar yyi warming dinsa Mai gadi ya bude masa gate ya fita, kafin Inna ta isa titi ta tare mutane sun fi biyar a hanya tana masu describing din Imaan ko sun ganta, duk aka ce mata ba a ganta ba sai ta rushe da matsanancin kuka tana cewa "Bukar baxai ta6a gafarta min ba har duniya ta nade" hakuri aka dinga bata tana tafiya tana kuka har ta isa titi, Parking Mujaheed yyi ya sauke glass, ya wani daure fuska yace "Shigo mu wuce" a fusace ta kallesa tace "In wuce gidan ubanwa ba yarinyar mutane, gidan ka dai ya xama na jaraba daga xuwa Imaan ta 6ata...." A fusace yace "Wai imaan din yarinya ce da xaki tsaya titi kina nemanta?" Ta xaro ido tace "Yarinya ce a gun ubanta wlh, ita kadai fa garesa, wllh ba ruwana ka rabu da ni Mujaheed, me xanje ince ma Bukar da Aisha idan na shiga mota...." Sai kuma ta rushe da kuka mai ta6a xuciya, ganin mutane an fara taruwa kanta Mujaheed ya ja tsaki yaja motarsa ya bar ta wajen, gida ya wuce direct, yana parking kofar gida ya shiga ciki, babu kowa compound din ya tafi part din su Imaan, ya kusa minti daya tsaye a balcony kafin yyi sallama murya can kasa ya bude kofar ya shiga parlon, imaan ce xaune parlon da plate din abinci gabanta tana ci tana kallo, suna hada ido ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi dakinta da gudu ta shige ta kulle kofa, Ammi ce ta leko daga kitchen, yyi kasa da kai yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya gida" yace "Alhmdllh" komawa kitchen tayi ya xauna saman kujera a parlon, ba a dau lkci ba Ammi ta fito tace "Ya amarya fa..." ya d'an yi murmushi yace "Tana lafiya" tace "To maa sha Allah, a xubo maka abinci?" Yace "A'a Alhmdllh" dauke abincin da imaan ta bari a parlon tayi ta kai dinning ta ajiye ta dauko wani plate ta rufe, Ammi tace "Ka dawo da Innar ne?" Yace "A'a, tana dai tahowa" Bai rufe Baki ba sai ga Inna duk ta hada xufa tace "Ina Bukar yake?" Ammi na kallonta da mamaki tace "Sannu da xuwa Inna" Inna tace "Ke tambayar ki nake Ina Bukar, ban ga imaan ba wllh..." Ammi tace "Imaan kuma, ae ta dawo tun daxu" salati Inna tayi a hankali tana tafe hannu tace "Ta dawo?? Amma wannan 'ya ta Bukar axxaluma ce wllh, Allah kaga yanda yarinyar nan ta daga min hankali na dinga tona ma kai na asiri a titi, Allah kaga yanda ta sa na bar jakata da dubu daya a gidan mutane na fito ba shiri, Allah kaga yanda ta sa cikina ya rude a titi na dinga neman bayan gida...." Sai kuma ta rushe da kuka ta fita parlon tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, don imaan jarababbiya ce, ko da yake uban nata ma fitinanne ne" Ammi dai banda murmushi ba abinda take, ta kalli kofar dakin imaan tace "Imaan" sai da ta kirata sau biyu sannan Imaan ta yi ma Sadeeq sallama a wayan da suke yi, ta fito da hijab har kasa tana sunkuyar da kai, Ammi tace "Meyasa kika taho baki sanar da Inna ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi bacci fa take ta yi, kuma ni na gaji ina son dawowa gida" Ammi tace "Toh ai kin kyauta" Imaan ta saci kallon Mujaheed dake ta kallonta, ta juya da sauri ta koma daki ta rufe kofarta. Some days later aka fara shirye shiryen saukan su Imaan a gidan, during this period soyayya mai xafi imaan suke yi da Sadeeq amma ta waya, gaba daya ya ki xuwa ta rasa me yasa sai dai ya kirata, kullum xancensa shi dai ji yake kamar ya jawo kwanakin duk da bai fi saura wata biyu xa su xana jarabawan waec ba, ko da xai xo gidan kuwa dama Inna yake xuwa gaidawa kuma ko ita imaan bata sani sai ya tafi xai kirata yace ai ya xo gidansu, ranan asabar ya kama saura sati daya saukansu, ranan kuma ya kama sati biyu da bikin Mujaheed, misalin sha daya da wani abu na safe ya xo gida tare da Safeenah, ubansun lace ne jikinta sai mayafi da ta sakale a wuya hannunta rike da handbag sai takalmi mai tsini da ta sa, tayi kyau har ta gaji, sai xuba kamshi take, fuskar nan nata ya sha make up ba a cewa komai, part dinsu ya nufa tana biye da shi, su Maimoon da Ummi suka yi welcoming dinta da fara'a, ta amsa masu da siririyar muryarta tana murmushi, Maimoon ce ta tafi sama ta kira Aunty, Aunty na sakkowa tace "A'a Aunty amarya ce a gidan namu, Sannu da xuwa" Safeenah ta kalleta tace "Yauwa..." Aunty ta xauna tace "Fatan an tashi lafiya" Safeenah tace "Lafiya lau ya gida" Aunty tace "Alhmdllh, ya naku gidan" Safeenah tace "Lafiya lau" Aunty tace "Toh madallah..." Mujaheed dai sai kallon Safeenah yake jin bata gaishe da Aunty ba, Bai dai ce komai ba ya kalli Aunty yace "Abba fa?" Aunty tace "Tun safe ya fita" Mujaheed ya mike yace "Ohk bari mu gaida Inna" Aunty tace "Toh shkkn sai kun dawo" yace "Yusuf ya dawo?" Aunty tace "A'a bai dawo ba" kofa ya nufa Safeenah ta mike ta bi bayansa Aunty ta bi ta da ido har suka fita ta girgixa kai ta mike ta je ta ci gaba da abinda take, suna fita Mujaheed ya kalleta rai bace yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan Safeenah, mum dita ce ita ma fa?" Tsayawa tayi tana kallonsa da mamaki tace "Me nayi kuma?" Yace "Did you greet her?" A fusace tace "Kai komai kace fada da bala'i, to ni ban ma sani ba, da muka fito sai kayi correcting dina ba ka dinga min fada ba haba" Bai tanka ta ba ya ci gaba da tafiya ta bi bayansa tana tabe baki, part din su Imaan ya shiga tana biye da shi tace "Nan ne part din innar?" Ya kalleta yace "Part din uncle dina" Bai jira cewarta ba ya shiga parlon da sallama, d'an tsaki tayi ta shiga ita ma, Ammi na xaune parlon ta mike ganinsu tana masu sannu da xuwa da fara'a, Mujaheed ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Sannun ku da xuwa" Safeenah da kallo daya tayi ma Ammi ta gane ita ce Mahaifiyar Imaan coz it's soo obvious, ta wani daure fuska tana kallon Tv, Ammi tun da ta kalleta sau daya taga bata gaisheta ba dama bata sake kallonta ba, ta tafi kitchen tana cewa "Bari in kawo maku ruwa" wani kallo Mujaheed ya dinga yi ma Safeenah da ta bude jaka ta fiddo chewing gum ta 6are ta jefa a baki tana tauna, murya can kasa tace "Did you greet her Safeenah?" Banxa tayi masa tana taune taunenta, Ammi ta fito ta ajiye ruwan kusa da shi, Yana kirkiran murmushi yace "Ae daga gida muke ma" Ammi ta xauna tace "Ae ruwa ne" daukan bottle water daya yayi yace "Daddy fa?" Ammi tace "Yana Abuja" Mujaheed yace "Toh xa mu je gaida Inna yanxu" Ammi tace "Toh maa sha Allah, nagode kwarai" mikewa yyi ya nufi kofa Safeenah ta mike ta bi bayansa Ammi ta bi ta da kallo, sai da suka sauka balcony ya juya yana kallonta kafin yace komai ta wuce sa da sauri tana kas kas da cingam fuska daure, gyada kai yyi ya dau hanyar part din inna ta bi sa a baya tana kyabe baki, Inna na share parlornta ta daga kai tana kallon Mujaheed tace "Waye wannan" Bai tanka ta ba ya cire takalmi ya shiga parlon, Safeenah ta cire takalmanta tana kirkiran murmushi tace "Sannu da aiki Inna, kawo in karasa share maki" Inna tace "A'a bar shi yi wucewar ki ciki, daga xuwa kuma sai ki hau shara ba ruwana, balle ma na gama" tace "A'a don Allah ki bari Inna, ki kawo in karasa" ajiye tsintsiyar Inna tayi ta mike ta amshe jakar hannunta tace "Toh ai nagode dama bayana kamar xai cire wllh, ita wancan mata tana kwance daki wai ba lafiya, dadin abun ma an san bata da lafiya kafin ta taho nan balle ace a parlon Inna, shi sa ban wani gigice ba, Allah dai ya yaye mata wannan bala'i da ba a san kansa ba....." Mujaheed sai kallon Inna yake sannan ya kalli kofar dakin bai dai ce komai ba, Safeenah ta gama tattare parlon ta kwashe dattin da bai taka kara ya karya ba a Parker sannan ta mike tana murmushi tana kallon Inna tace "A Ina xan xubda dattin?" Inna tace "Can bayan window xaki tafi kwandon sharan yana nan xaki gansa fess na wanke wllh sai a iya xuba tuwa a ciki a ci, sai ki xuba a hankali kar ya bata jikin kwandon har hypo na sa yayin wankewa" Safeenah ta fita parlon ta sa takalminta mai tsini ta wuce bayan window, Mujaheed na kallon Inna da sauri yace "Me ya sameta?" Inna na kakkabe kujera tace "Wai Imaan, toh ga ta nan dai ya dama da xaxxabi ta tashi, ko ina ciwo sai ga al'ada shi ma ya xo ya sa ta gaba, daxu ta gama sharban kuka a nan, duk babu inda bata mirgina ba a parlon nan, ni dai baranda na koma nayi xamana ba ruwana, to nace ta tafi gidansu ta ki tafiya ya xan yi da ita...." mikewa yyi da sauri tace "A'a kar ka tasheta ka rufa min asiri, daxu wannan d'an albarkan Bulasawa ya xo dubata ya taho da magunguna da allurai...." Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah ta shigo parlon ta xauna kasan rug tace "Ina yini Inna?" Inna na murmushi tace "Lafiya lau 'yar nan, amma ku daina cika powder a fuska, kin dai yi kyau wllh powdern ne yyi yawa har kina naso..." Sunkuyar da kai Safeenah tayi tana ta kirkiran murmushin karfin hali, Mujaheed xai shiga daki Inna tace "Kinga fitina ko, Mujaheed nace kar ka tasheta, wllh allura aka mata
Chapter 151 · 0% Book details